Yau shekara 21: Tunawa da Garban Bichi da Shata

A YAU, 24 ga Satumba, 2020 Alhaji Garba Bichi, MON, ya cika shekara 21 da rasuwa. Fitaccen ɗan kasuwa ne, mutumin garin Bichi ta Jihar Kano.

Duk da yake sanannen mutum ne a harkar kasuwanci da kuma taimakon jama’a, waƙar da Alhaji Mamman Shata ya yi masa a cikin 1972 da taken ‘Haji Garban Bichi Ɗan Shehu’ ita ce ta ƙara fito da shi har duniya ta san shi a ko’ina.

Na sadu da Alhaji Garba a gidan sa a Bichi a cikin Satumba 1998, shekara ɗaya cif kafin Allah ya yi masa rasuwa. A lokacin da na isa gidan ma ba ya da lafiya, ya na kwanciyar da bai ƙara tashi daga gare ta ba. Da ya ji cewa daga wajen Shata na ke, sai ya aiko ya ce in shiga cikin gidan. Na same shi kwance a kan gadon sa. Ya tashi, mu ka gaisa. Na faɗa masa abin da ke tafe da ni: Alhaji Shata ya sa ni in rubuta tarihin rayuwar sa, kuma na zo ne in ji tsakanin su, musamman kan fitacciyar waƙar nan da ya yi masa. (Hasali ma dai waƙoƙi uku ne, akwai mai amshin ‘Habu Garban Bichi Baban Audu’ da ‘Ranar Alhaji Garba Bichi’, amma ɗayar aka fi sani).

Nan take ya amince, mu ka tattauna. Kuma na je da kyamara, na ba wani hadimin sa ya ɗauke mu hotuna, sannan kuma na ɗauki Alhajin hotuna. A wannan hoton, ga mu nan zaune a gefen gadon sa a lokacin.

Hirar tamu (a tsarin tambaya da amsa) ta fito a cikin littafin ‘Shata Ikon Allah!’ (bugu na biyu, 1998) wanda na rubuta (tare da gudunmawar hirarraki daga abokan aiki na su uku).

Ba zan kawo hirar baki ɗayan ta a nan ba, amma akwai abubuwa guda uku da na ke so in yi tambihi a kan su. Na ɗaya, kada mutane su ɗauka cewa Alhaji Garba ya tsofe wa Shata don an ji ya na ce masa “Baba” a waƙar. A zahiri, Alhaji Garba da Alhaji Shata tsararrakin juna ne; an haifi Alhaji Garba a cikin 1924, Shata kuma an ƙiyasta 1925. 

Na biyu, me ya sa Shatan ya ke ce masa “Baba” a cikin waƙa tunda dai tsaran sa ne? Dalilin dai shi ne dangantaka irin ta da. Mahaifin Shata, Ibrahim Yaro, yaron Alhaji Garba Bichi ne. A tsakanin 1960 zuwa 1964, Alhaji Garba ya yi kasuwancin sayen gyaɗa a sassan ƙasar Kano da kudancin ƙasar Katsina, ciki har da Musawa, garin su Shata. Garba ya naɗa Yaro a matsayin wakilin sa a Musawa kamar yadda ya ke da wakilai a wasu garuruwa huɗu inda ya ke da tashoshin sayen gyaɗar. Musawa ce babbar tashar sa; ya kan ba Yaro kuɗi ya saya masa waɗannan kayayyaki, ya tara masa su, shi kuma idan ya zo sai ya karɓa a loda a mota a kai masa Kano inda Ƙwarori ke saye su na kaiwa ƙasar waje. To, a kan idon Shata ake ta wannan hada-hadar. Kun ga kenan abokin baba ai baba ne, ballantana kuma ubangidan baba.

A waƙar ‘Haji Garban Bichi Ɗan Shehu’, mawaƙin ya tuno da wani zunɗe da wani mutum ya riƙa yi kan mahaifin Shatan a wata shekara, da Alhaji Garba ya ɗan yi jinkirin zuwa Musawa, har wannan ɗan adawa na cewa ƙaryar Ibrahim Yaro ta ƙare! Shata ya taɓo batun, ya na faɗin:

“Ranar tahiyas sa ƙauyen mu,

Ran da yab ba maraɗa kunya.

Ana, “Bai zuwa, uban Nura,

“Bana ba shi ciniki, Habu zaki,”

Magariba ana jibi sai ga Garba a kan mota.

Nan da nan na ga ya kori munahuki.

Garba sai na ga ya kori marak kunya!

Mugun madambaci Garba uban Nura!”

Kafin wani ya tambaya, kalmar “jibi” na nufin cin abincin dare, wato kamar tuwo kenan bayan sallar magariba. Sau da yawa a ƙauye, taruwa ake yi a ƙofar gida ko a zaure, kowane magidanci ya kawo nasa abincin, a taru kowa ya saka hannu ya ci. To, ana irin wannan “jibi” ɗin ne ne sai aka ga Alhaji Garba ya dirkako ya shigo gari. A nan ƙaryar magulmaci ta ƙare kenan!

Abu na uku shi ne zurfin amincin da ke tsakanin Alhaji Garba Bichi da Alhaji Shata. Sun shaƙu matuƙa a matsayin ‘ɗa’ da ‘uba’, musamnan bayan mutuwar Ibrahim Yaro a Makka. Ta kai har Shata ya kan je gonar Alhaji Garba ya ɗebi kayan lambu (har da kaji da zabi) ya cika mota ya yi tafiyar sa ko da Alhajin ba ya nan; kuma ya kan tsaya a gidan man Alhaji Garba da ke nan ƙofar gidan sa a Bichi a cika masa tankin motar sa ƙirar GMC (har ma ya ɗiba a duro), ya yi gaba abin sa. Yaran Alhaji Garba ba su iya hana shi. 

Wannan ɗabi’ar ce ta sa a waƙa Shatan ya ke cewa:

“Baba ina tunani Habu zaki:

Ɓarnar da na ma a gida,

Laihin da na ma gona,

Ka yahe mani dattijo.

A’a! Baba ka yahe mani ɗan Shehu.

Da Allah, Baba ka yahe mani laihin nan.

Don ko ina tunani Habu zaki,

Komi ka yi wa dattijo,

In babu sani kai mai, idan ka tuna akwai hakki.

To Baba ka yahe mani laihin nan.”

A’a, Baba ka yahe mani ɓarnar nan.”

Allah ya jiƙan waɗannan bayin Allah su biyu, amin.

Da yawa an san tarihin Shata. To shin menene tarihin Alhaji Garba Bichi? Ga tarihin da ɗan sa, Alhaji Ibrahim Garba Bichi, ya rubuta a bara lokacin da dattijon ya cika shekara 20 da rasuwa:

ALH GARBA BICHI, NCE, MON

An haifi Alhaji Garba Bichi a unguwar Huggalawa, cikin garin Bichi a Jihar Kano a shekarar 1924. Sunan mahaifin sa

Malam Ali. Ya yi karatun Alƙur’ani da na ilmi a hannun Malam Bawa da Malam Umaru, duk a unguwar Huggalawa. Ya kuma yaƙi jahilci a fannin ilmin zamani domin ya iya rubutu da karatu.

Tun ya na ƙarami ya ke da ƙwazon neman na kan sa, domin ya na ɗaukar tallar goro ne a hannun wani mutumin unguwar su mai suna Ɗanyayye. 

Daga baya ya shiga harkar kasuwanci nasa da jarin sule saba’in. A hankali harka ta fara bunƙasa a fannin amfanin gona. A hankali sai ya shiga harkar kayan masarufi, musamman a lokacin da kayan amfanin gona su ka yi ƙasa. A wancan lokaci, ya na harka da kamfanoni irin su John Holt, UAC da Leventis. A shekarar 1946, sai ya fara cinikin gyaɗa tare da Alhaji Abdu Farar Hula, domin shi ya na da LBA (Licensed Buying Agent). 

A shekarar 1958 sai ya kafa kamfanin sa na farko, wato Alhaji Garba Bichi & Sons Ltd. A 1960 ya samu LBA tare da su Alhaji Sunusi Ɗantata, Aminu Ɗantata, Musa Gashash, Haruna Ƙassim, Baballe Ila da sauran su.

Ya sake kafa wasu kamfanonin daga baya irin su Garba Bichi Tankers Ltd da Bichi Petroleum Company Ltd. Haka nan sun taɓa kafa wani kamfani shi da Alhaji Imam Shu’aibu mai suna EKODIS a Nijeriya, a Faransa kuma su na kiran sa EKODIMA.

Harkokin kasuwancin Alhaji Garba sun wuce garin Kano da Nijeriya har sun shiga Afirka da kusan duniya baki ɗaya.

A harkar siyasa kuwa ya yi NPC da NPN. Daga baya sai ya yi murabus daga al’amuran siyasa, ya zama uban kowa.

Ya samu lambar girma ta MON. Ya taɓa zama uba ga Amnesty International, reshen Nijeriya. Haka nan makarantar FCE Bichi ta taɓa ba shi kyautar NCE.

Allah ya karɓi ‘giwa uban Nura’ ran 24 ga watan Satumba, 1999. Ya mutu ya bar ‘ya’ya 20. Shi ne mahaifin su marigayi Nura, Surajo da Ahmed ɗan takarar gwamnan nan na jam’iyyar PDP a shekarar 2007 kuma tsohon Ministan Ciniki da Masana’antu na ƙasar nan.

Kuma shi ne wanda Dakta Mamman Shata ya yi wa waƙar ‘Haji Garban Bichi Ɗan Shehu’ da ‘Habu Garban Bichi Baban Audu’.

Wani abin lura shi ne ya rasu a daidai sa’ad da al’umma ke buƙatar dattawa irin sa. Kuma al’ummar Bichi, Kano da ma ƙasa baki ɗaya ba za a manta da irin gudunmawar da su ka bayar ba.

Allah ya jiƙan sa, ya albarkaci bayan sa.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *