• About
  • Contact
Thursday, July 31, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa Waƙa

Aburaɗi

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
May 11, 2024
in Waƙa
0

ABURAƊI

Daga Ibrahim Sheme

Rabbana a gare ka na zo,
Ba ni tsaba ba ni ƙanzo,
Durƙuso na yi gun sa Manzo,
Ɗan Amina uba gare ni.

Zuljalali ka ba ni fiƙira,
Ban da izza ban gadara,
Ban tsimi da yawan dabara,
Ya Ilahi ka agaje ni.

Zuciya ta ce ta shilla,
Tsallaken boda ta lula,
Gun habibti ne ta ɓulla,
Son ta ba mai sa ma’auni.

Shi garin su fa shi masoyi,
Bai da zafi bai da sanyi,
Bai da nisa bai da ɗoyi,
Sai yawan ƙamshi amini.

Tau habibtin malama ce,
Can a koyarwa ta dace,
Rabbi ya sa mun yi zance,
Har na wo sa’a ta so ni.

Tunda ta amsan da gaske,
Nai shiri da shiga ta sulke,
Ko a barci ko a farke,
Don na tsallake dukka tsauni.

Ta shigen ruhi da ɓargo,
Ko rufa na yi ni a bargo,
Har jikin bishiya da bango,
Sai na gan ta gaba gare ni.

Ni a rai na ga ta zaune,
Nan a gefe na a manne,
Ba mu sauraren mutane,
In suna magana da muni.

Ni a rai na ga ta kwance,
Sai ina kallo a sace,
Ba ni so hangen ya kauce,
Tunda son ta ya mamaye ni.

Na yi roƙo gun Tabara,
Don ya ba ni ɗiya na aura,
Sai ko mai koyar da yara,
Sai ya ɗauko ta ya ba ni.

Ga ta kyakkyawa a fasli,
Ga yawan haske na ilmi,
Ba ɗagawa babu irli,
Ga cikar haiba, zabuni.

Lafuzzan ta kamar sarewa
Aka busa, ga sakewa,
Murmushin zaƙin alewa,
Gun ta mai daɗin bayani.

Ba ta burga ita wannan,
An kira ta fa to a ran nan,
In daɗewa ce a sannan,
Za ta ce mani, “Ɗan jira ni”.

Duk dare in mun yi taɗi,
Safe har rana ta faɗi,
Ta cikan ƙalbi da daɗi,
Mamayar dukkan sukuni.

Na yi murna, nai salati
Gun Muhammadu mai wafati,
Ɗan Amina uban su Fati,
Wanda yai gata gare ni.

Sai kwatsam ran nan ta ɗauke
Min wuta, sam babu aike,
Ta saka ni a banke-banke,
Sai ka ce ɗan ci-da-raini.

Jarumar duk sai ta sake,
Na zamo Fillo a make,
Mai rashin shanu a garke,
Duk tunani ya ishe ni.

Zuciya ta na ta gumza:
Me na gatsa ko na ciza?
Me ya faru kwatsam ta canza,
Har ya janyo ta guje ni?

Ba ta so na ne da farko?
Tai kalamai masu ƙarko,
Ko shiri ne duk ta narko,
Har na yarda da za ta so ni?

Nai waya domin mu gaisa,
Nai wasiƙa babu amsa,
Ba halin ta ba ne ta kasa,
Tai shiru ba ta kula ni.

Na jima ba na sukuni,
An yawan magana gare ni,
Ban kula ba ina tunani,
Ba na jin ƙamshin furanni.

Tun da safe zuwa maraice,
Nai ta saƙa sai in kwance,
Sai ka ce gado ya zauce,
Ya kasance majanuni.

Nai zaton harshen magabta,
Mai yawan zagin maƙwabta,
Ya yi tasiri a kan ta,
Har ya sa ta ji ta tsane ni.

Su fa shashashun mutane,
In ana magana ta so ne,
Sun fi so su ga tada zaune,
Ba su son haske gare ni.

To ahir a gare ku jumla,
Tunda ƙauna muka ƙulla,
Rabbi ya hasko fitilla,
Ba ku cusa duhu gare ni.

Jallah mai ƙudira da iko,
Tabbatar mana wanga baiko,
Ai biki sannan a ɗauko
Tau amarya zuwa gare ni.

Wanga waƙe nan ya ƙare,
Sai jiran guɗar amare,
Nan gida na za su tare,
Jallah kai tanyo gare ni.

Wagga waƙar ba hasashe,
Na zubo domin ku kwashe,
Ko na rera don ku amshe?
Ga lafuzza shar suhani.

Sha’irin ku kira ni Iro,
Faƙiri gun zana biro,
Don ku gane za na ƙaro
Inkiyar Sheme gare ni.

Tammat wa bihamdillahi

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: waƙawaƙe
Previous Post

Taken Mahammadu ɗan Saleh daga Kassu Zurmi

Next Post

Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in

Next Post
Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in

Ta'aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba'in

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d