A ranar Laraba, 28 ga Yuni, 2024, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1446 Bayan Hijira, mashahurin malamin nan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda shi ne jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Nijeriya, ya cika shekara 100 cur da haihuwa. A yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Ƙoli ta Al’amuran Musulunci (NSCIA). An haife shi a ranar 28 ga Yuni, 1927, wadda ta yi daidai da ranar 2 ga Muharram, 1346 Bayan Hijira. A tsarin kalandar Bature, a bana Shehi ya cika shekara 97 ne, to amma a lissafin Hijira ya cika shekara ɗari cur ne.
Asalin Shehi Bafillace ne wanda aka haifa a garin Nafaɗa da ke cikin Jihar Gombe a yau. Mahaifin sa, Gwani Alhaji Usman Adam, babban malami ne, mahaifiyar sa kuma, wato Hajiya Maryam Arɗo Sule, asalin ta daga garin Gamazo da ke Jihar Yobe take, amma a Nafaɗa aka haife ta.
A lokacin haihuwar Shehi, garin Nafaɗa cibiyar koyon addinin Musulunci ce, kuma mahaifin sa Muƙaddam ne, wato shugaba a ɗarikar Tijjaniyya wadda Shehu Ahmad Al-Tijjani, wanda ya rayu a ƙarni na 17 miladiyya a ƙasar Aljeriya, shi ne ya assasa ta. Lokacin da Shehu Ɗahiru yana yaro, ya yi karatu har ya yi haddar Alƙur’ani a gaban mahaifin sa. Daga nan, bisa shawarar mahaifin nasa, sai ya kutsa kai ya shiga garuruwa domin neman ƙarin ilimi. Ya yi karatu a ƙarƙashin malamai da dama, waɗanda suka haɗa da Shehu Abdulƙadir Zariya, Shehu Usman Zangon Barebari, da Shehu Abubakar Atiku. Ya karantu sosai a cikin ɗarikar Tijjaniyya, wadda a yau take da miliyoyin mabiya a ƙasashen Afrika da dama har ma da wasu nahiyoyin. Ɗarikar ta samu tagomashi da yaɗuwa ne a yankin Afrika ta Yamma sakamakon hidimar da manyan shaihunnai suka yi mata tun bayan wafatin Shehu Ahmad Tijjani, irin su Shehu Umaru al-Futi, Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da uwa-uba mashahurin malamin nan ɗan ƙasar Senegal, wato Shehu Ibrahim Inyass. A yau, an yi ittifaƙin cewa ɗarikar Tijjaniyya ba ta da jagora da ya wuce Shehu Ɗahiru Bauchi, wanda tun yana matashin malami ya sadu da Shehu Inyass a birnin Kano.
Shehu Ɗahiru Bauchi ya yi auren fari ne a cikin 1948 lokacin yana ɗan shekara 21 da haihuwa. Allah ya yi masa nasibi wajen ɗaukar ilimi da yaɗa shi, domin tun bai manyanta ba ya shiga ƙwaryar manya ana damawa da shi a fagen ilimi. Kuma ya samu tubarrakin malaman sa ta hanyar yi masu cikakkiyar biyayya, musamman ma dai Shehu Ibrahim Inyass, kuma ya sadaukar da rayuwar sa kacokam ga harkar koyarwa da wa’azi a duk faɗin Nijeriya. Sunan sa ya yaɗu a Afrika ta Yamma ta hanyar watsa wa’azin sa da aka riƙa yi a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a lokacin azumin watan Ramalana da sauran shirye-shirye na gidan rediyon. A shekarun da suka biyo baya ya kafa makarantu da masallatai a ƙasashen Afrika ta Yamma. Kai, ayyukan Shehi sun yaɗu har zuwa ƙasashen da ba na Afrika ba, misali Amurka.
Wani abin lura game da Shehi shi ne, bayan tasa sadaukarwar, ya kuma sadaukar da rayuwar iyalin sa da almajiran sa ga hidimar koyarwa da wa’azantarwa, a ko yaushe suna kira ga Musulmi da su riƙa karatun Alƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Gidan Shehi a Bauchi, wanda kuma babbar makaranta ce, cike yake da manema ilimi. Haka kuma yana gudanar da aikin agajin jama’a ta hanyar Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi. A yayin da ake ta zafafa kiraye-kirayen cewa a hana ‘almajirci’, wanda mutane da dama suka ɗauka cewa tsarin barace-barace na ƙananan yara ne, Shehi ya yi hoɓɓasan kafa makarantu a garuruwan da iyayen yara suke saboda iyaye su riƙa ba da gudunmawa wajen kula da ‘ya’yan su da ke karatu a makarantun nasa. Haka kuma an san Shehi da yawan kyautata wa mabiyan sa da mataimakan sa, kai har ma da matafiya. Wata kyakkyawar shaida da ke nuna cewa koyarwar Shehi ta zaman lafiya ce ita ce yadda ba a taɓa jin almajiran sa, duk da ɗimbin yawan su, a cikin ayyukan ta’addanci ko tsattsauran ra’ayi da suka addabi Nijeriya a wannan zamanin ba.
Wani abu da ake saurin tunawa game da dogon zamanin Shehi shi ne rawar da ya taka a cikin zazzafar taƙaddamar nan da aka yi tsakanin Ɗarika da yake jagoranta da ƙungiyar Izala da marigayi Sheikh Abubakar Mahmood Gumi ya jagoranta, abin da ya jawo rarrabuwar kan al’ummar Musulmi a zangon shekarun 1980 da na 1990. Wannan rarrabuwar ba ta sa Shehi ya yi sanyin gwiwa ba ko ta karkatar da shi daga hanyar aƙidar da yake jagoranta ba. Miliyoyin mabiyan sa, kai har ma masu adawa da shi, sun ci gaba da girmama shi matuƙar girmamawa daga wancan lokacin har zuwa yau ɗin nan.
Abin farin ciki ne a ce malami irin Shehu Ɗahiru Usman Bauchi ya cika shekaru ɗari a raye. Duk da yake a matsayin sa na ɗan shekara ɗari za a ga ya tsufa ya yi tamoji tare da nuna alamun raunin jiki, wanda ba abin mamaki ba ne, to amma ƙwaƙwalwar sa ras take, ba ya da mantuwa, kuma muryar sa garau idan yana karatu. Har yanzu babu irin gigicewar nan ta tsufan ɗan shekara ɗari a tare da shi.
Haƙiƙanin gaskiya, Shehi ya ba da gudunmawa sosai ga ƙarfafa Musulunci a Nijeriya, kuma Nijeriya ta ci moriyar aikin da yake yi na tabbatar da zaman lumana da adalci a cikin al’umma. Ya gina al’adar karatu da karantarwa, tare da yin kira ga jama’a da su yi zaman lumana da haɗin kai da juna, da bin tafarkin Manzon Allah – wanda wannan shi ne gundarin saƙon Islama. A kan haka ake kallon sa a yanzu da ya cika shekara ɗari a doron ƙasa, kuma a hakan za a ci gaba da tuna shi ko bayan babu shi.