Farkon ƙasida ba ni kai ku da nisa,
Sai nai salatin wanda bai da makusa,
Manzo mahaifin Fati Nana lawisa,
Sujada nake gun Wanda yai yo Isa,
Ya zame cikin hasken sa bawan Allah.
Jigon ta Sallah ce na wannan waƙe,
Murna muke ƙalbin mu ya ɗau haske,
Wannan biki lallai mu yi shi da gaske,
Ikhwan Musulmi ragunan mu a turke,
Layyar mu sai lagwada muna hamdala.
Sallah ta idi muka je mun yi ta,
Mun sa tufafi masu kyau domin ta,
Lada haɗa shiriya muna neman ta,
Liman yana huɗuba ƙwarai mun ji ta,
A zuwa da dawowa muna hailala.
Sunnar Ma’aiki ce fa sallar idi,
Domin cikar koyon sa Manzo Sidi,
Wannan da ya kawo shi Babban Kundi,
Ya zamo siraɗal mustaƙim, mun sirdi,
Mu tsaya a kai sam babu tsilla-tsilla.
In mun tsaya ƙyam babu inda-inda,
Bautar Ta’ala yin ta ba ma ganda,
Ladar tana da yawa garai shi wanda
Neman ta ya dage da kurɗa-kurɗa,
Balle a yau rana ta Babbar Sallah.
Ba a fushi kuma ba faɗa ba zagi,
Sai cin tuwo da miyar da ta sha magi,
Ko cin su shinkafa da kaji shirgi,
In kai yawan santi a sa maka waigi,
Soye na rago an cika maka kula.
Daga nan zumuncin ‘yan’uwan mu haƙiƙa,
Mota da mashin har su keke mu tuƙa,
Hatta da sawayen mu yanzu mu taka,
Da kiran waya ko tes mu zam mun miƙa
A farin ciki saƙon zumunci wallah.
Duka ‘yan’uwa na jini da sauran dangi,
Baban mu, Mama haɗa da tsagi-tsagi
Na aboka jumla babu sauran kingi,
A cikin su yau dai duk muna shawagi,
Mu je zumuncin nan na murnar Sallah.
Mai son ganin Sarki a gan shi a fada,
Don gaida zaki shugaba, don sada
Duka martaba domin cikar al’ada,
Kuma gun iyaye ka zamo ka jakada,
Riƙa yin hakan daidai a yau ba illa.
Haka ne ake yi duk a birnin Dabo,
Mu ma a KT mun jima mun sabo,
Birni na Shehu da yankuna har Yabo,
Sauran ƙasashen namu duk na ɗebo,
Daga can cikin Zazzau da birnin Yola.
Jama’a mu gode Zuljalal Rabbani,
Wannan da yai ƙwalwa ya ba ta tunani,
Da ya ba mu iko ƙauyuka har birni,
Ƙarfin zukata shi ya ƙara zabuni,
Komai muke yi mu yi domin Allah.
Allah Ta’ala ƙara ikon naka,
Sallar baɗin baɗaɗa mu gan ta da harka,
Ka zubo yawan haske a kowace garka,
Domin isar Manzo masoyin Makka,
Wato Muhammadu Ɗaha ɗan Abdallah.
Ni ma a nan zan dakata in nisa,
Kada in wuce marayi da bushin busa,
Har ma wanin ku ya ce da ni ya ƙosa,
Na shirya waƙar don mu sadu mu gaisa,
Rana ta yau don miƙa saƙon Sallah.
Tsarin bayani ga shi dalla-dalla,
Na kammala zancen mu filla-filla,
Allah ya yafen kuskuren da na ƙulla,
Wannan ƙasida wadda nai ran Sallah,
Baitin ta goma haɗa biyar kai jumla.
Burhama ni ne sha’irin da na yi ta,
E, Sheme ne sunan da zan ɗan gitta,
Na kwaɓa baitoci da fannonin ta,
Na yi su babu isa irin ta gwaninta,
A cikin muradi na na ɗokin Sallah.