Subhanallahi Mai Girma,
Kullum sujuda nake yi ma,
Yau birnin Dabo zan koma,
Domin na sanar da gogarma:
Mu ba mu fushi da yin Allah.
Ya Rabbih ka ba ni ilhama,
‘Yar waƙa in yi in cimma
Nasara a cikin ta, to amma,
Ƙaro tsirar ka mai dama,
A gare shi ƙwarai Rasulullah.
Farkon waƙa cikar aiki,
Sai na yi maraba gun Sarki,
Na Kano mai ba da mamaki,
Muhammadu wanda yai banki,
Liman baban mu gun sallah.
Duk wanda ya dubi fuskar mu,
Tarin hasken ta zai samu,
Caffa muka yi da hannun mu:
Barka da zuwa Amir namu,
Wannan fa gidan ku ne wallah.
Allah mai maganin sammu,
Shi ya sa Abba ya samu,
Ya kada farin ga mai gemu,
Lallai fa furar mu ta damu,
Sai luddai yanzu ba illa.
Sanusi sannu jan zaki,
Mai take maza suna raki,
Ka dawo yau bisan mulki,
Don ƙarasa ayyukan kirki,
Don ka yi riƙo da bin Allah.
Yau an yi naɗi gaban gwamna,
A hawa na biyun ka ka zauna,
Kowa ka gane shi sai murna,
Sai dai ko sakarai sauna,
Mai zabga fushi da yin Allah.
Ka hau karaga ta kakan ka,
Ka sake hawa da ƙarfin ka,
Duk nauyi nata ka ɗauka,
Shaida wa shugaban shirka,
Mu ba mu fushi da yin Allah.
Mai yin zagin ga ɗan guntu,
Na gan shi yana ta sambatu,
Zakara ya riƙo da ɗan kurtu,
Gun tsafi za shi ko kotu?
Mu mun rusuna wajen Jallah.
Wanzami ba ya son jarfa,
Makaho ke gudun jifa,
Shi tsoho sai da sassarfa,
Ɗawisu yana da kyan siffa,
Limami bai gudun sallah.
Sarkin mu Khalifa zai fara
Sabon ɗinki da allura,
Mannanu ka ba shi duk lura,
Domin darajar uban Zara,
Don ba ya fushi da yin Allah.
Yanzu fa gidan su zai ƙarko,
Don da ma tun a can farko,
Tun kafin mai zubin tarko,
Ya ɗana masa mun ga yai maiƙo,
Kafin su taho su ɓaɓɓalla.
Ko Dabo da ke kushewar shi,
Zai murna tunda ka so shi,
Ka gyara gida da bayan shi,
Yau babu karen da ke haushi,
Ka karɓi ƙasar ka kaf jumla.
Baban Musty da Siddiƙa,
Ka kwance shirin da sun saƙa,
Ka dawo, yanzu sai ƙaƙa?
Hatta su Naziru Mai Waƙa,
Sai murna, sai yabon Allah.
Giwar Sarki a gaishe ki,
Sarki kike nan gidan Sarki,
Kin gyara gidan gadon mulki,
Mu mun yi na’am da halin ki,
In kin yi kira mu ce yallah.
Matar Sarki, ɗiyar Sarki,
Ƙanwar Sarki, uwar Sarki,
Loto na duhun kusufin ki,
‘Yan fada suna ta kewar ki,
Sai dai wawan da bai sallah.
Sauran matan da ‘ya’yan ku,
Nai caffa gun ku sannun ku,
Jabbari ya karɓi roƙon ku,
Ya ba ku ƙasar ku barkan ku,
Sam ba ku fushi da yin Allah.
Jagora sannu mai kulki,
Mai ƙwalawa ana raki,
Kai Rabi’u kun yi jan aiki,
Sannun ka gwani wajen mulki,
Kai ba ka fushi da yin Allah.
Da masoya masu son Sarki,
Gaishe ku majagaban aiki,
Mun gode duk ɗiyan kirki,
Tsinkayar nesa sai maiki,
Yau Liman za ya ja sallah.
Wannan waƙar ku shaide ta,
Ibrahim Sheme ya yi ta,
Don murnar sake sarauta,
Ta Khalifa sai ku amshe ta,
Kan ba ku fushi da yin Allah.
24/05/2024

