Na Bala na Bala kwakaya,
Ina dunga baƙab bisa karen ɗan Inna,
Kahira ba a sakin ki sai duniya tai kwana,
Ba tagumi ba hawaye na Sani ka sa mutane kuka,
Ɗan Sanda ubangijin cocilan,
Shiga na ji ɗaki ana hamsari,
Ɗauki ɗauki ɗauki ɗauki ɗauki ɗauki na Sani.
Ba tagumi ba hawaye na Sani,
Barka da yawon duhu ɗan Geshe,
Mahammadu barka da ‘yan zage-zagen birni,
Barka da ‘yan take-take na kashi,
Na Amadu barka da ‘yan ƙunge-ƙunge cikin gida ba ka aje komi ba.
Sugugum ɗaka madugu na cikin ƙorai,
Mai fatauci ana nasari.
Albishirin ka ɗan Saleh ga jan banza,
Ka ka hwasa su sai ka bari an dawo,
An dawo dag Gusau an game ma kuɗɗi.
A ba ni in tasbaha ta bayat,
In dunduhwa ta bayat,
In ta bashe ku kau kun wuce, shi an nan,
A raɓa a baj jaye-jaye na kowa.
Ƙaramin ɗan duniya ka tonon rairai,
Mamman ya hwaɗa haƙoran mata,
Sai ƙoƙarin ɓantalar tasoshi,
Shegen ɓarayi an nan,
Rangama ba ta zanen suna.
Gamshiƙa na Sani in kai ne in ji kuwwa ana Buzanci:
“Iy! Tare! Kai namiji!”
Mahammadu in ji ka ba Bugaje haushi.
To!
Mala’ikan Bugaje ɗan Saleh ciyyon cikin ‘yan banza,
Albishirin ka ɗan Saleh, ga jan banza,
Kada ka fasa su sai ka bari an dawo,
An dawo dag Gusau an game ma kuɗɗi.
Mahammadu fatake na dare,
Ɗan Saleh a ba ni in jiniya ta kawo,
Tarago mai jan kaya,
Jirgin bisa mai ‘yat tselen uwar yaya,
Kana gaba rigimak ka na biya dab baya ɗan Sanda.
Baƙin Abarshi arnan na Magaji su ba su ƙamnah haske,
Mamman son sukai a dai ɗibga duhu da iska ana yaf-yaf-yaf,
Wada aka takin kare ba a jin ƙara tai.
Maigida bai sani sai sun yi.
Kai masama, kowas samu fan ɗari yai Makka,
In yaƙ ƙiya su mai sai ga bara,
Akwai mu da rairai masu mai da mutane baya.
Dukiyab bahili ta yaɗu sai masu cin sun kawo,
Allah ya tama ka ɓanna na dare,
Mahammadu Allah shi tama ka ɓanna kullun,
Manyan fatake na dare ɗan Saleh tayin kura,
Tayin kura, kare ba ya son golo nai.
Abin da ba mu so ɗan dokad dare,
Kun san ɗan dokad dare, taro?
A’a shegen ƙwaron ga mai ɗan gaton uwaz zahi karen gida:
Bai aje ba bai ba wani ya aje ba sai yay yi tsugunne yah hana ido nai kwana.
Haushin mutum daban da na kura:
In ka ji karen ka ya kwashi haushi ya yi bakin gida,
Ya dawo dab baya-baya yana bugun ƙohwaɗ ɗakin ka, kura ce!
Gudummawa ka cecai an nan,
Amma haushin ɓarai da ka ji ya kwasa ya kewaya bakin gida an kewayo dag gabas ya kewayo,
Shina: “Ga su ga su ga su ga su!
“Ga su ga su ga su ga su ga su!
“Ga su ga su ga su su ga su!
“Ga su ga su ga su ga su ga su!”
To gar ka sake, hito masu yin sun kawo!
Maganin maza ɗan Sanda,
Mamman ɗan Saleh maganin samnokin maza masu gigin kwana.
Mata na hwaɗi, “Ana motci,”
Maigida na hwaɗin, “Haba, kusan ɗakin ga ne,
Kin san halin ɗakin ga da ɗan neman kusa.”
Kun jiya masama, wallahi ka mutum ya yi kwana ya rer rena motcin kusa,
Kowar rena su wata zamba na shafa tai.
Ba tagumi ba hawaye na Sani wa za ka sawa kuka?
Bari sai wani ya samu sa’ak Kano ya dawo.
To fa!
Mahammadu fatake na dare,
Sugugum ɗaka madugun cikin ƙorai,
Mai fatauci ana nasari.
Ban rena mai gafara-ƙyaure ba,
Ban dai rena gobarah hannu ba tunda ni ba ta cin komi nau.
Kura ta wuce, ƙasa aka nuni,
Da ‘yan ɓace-ɓace na banza:
“Kun ga sau nai, ho ɗan bura-uba!”
“Kun ga inda ya bi nan!”
Ha!
Ai ya riga ya wuce sai sau nai.
Mahammadu fatake na dare,
Ƙusuru kwashe ginat tama,
Ɗan Sanda ɗan baƙin dabba kal,
Ga ya nan ko Sarkin gari ba ya son kuka nai,
Gamshiƙa ubangidan Hasana,
Ba ka yi lattin taɓin ƙyaure ba.
Ta!
Bautag godiya ga Mamman ɗan Saleh doki takwas yab bayas,
Amma hwa hay yau kari ne yay yi man ba biyan take ba.
Wada ni ka so da kai yi man mai geza,
Ushe matak ka ta ba ni dilar turamen lailai,
Don kau ba saye za ka yi ba, suna gida jiniya ta kawo!
Manya ka zam ɓanna ta dare!
Tarago mai jan kaya ɗan Sanda,
Jirgin bisa mai ‘yat tselen uway yaya,
Ɗauki ɗauki ɗauki ɗauki ɗauki na Sani,
Mahammadu fatake na dare,
Gamshiƙa ubangidan Hasana,
Ta!
Masu ‘yan kunge-kunge na Sani.
Gamshiƙa ubangidan Hasana,
Masu ‘yan ƙurme-ƙurme na Sani.
Mamman fatake na dare,
Kura ta wuce, ƙasa aka nuni,
Da ‘yan ɓace-ɓace na banza,
Mai hanƙurin jan ciki,
Ɗan Saleh an wa guwawu kanta.
Dunga baƙat bisa karen ɗan Inna,
Kahira ba a sakin ki sai duniya tai kwana,
Mahamman fatake na dare,
Ba tagumi ba hawaye na Sani,
Amma Allah ya tama ka ɓanna na dare,
Aha!
*
Taken Mahammadu ɗan Saleh daga Kassu Zurmi
Rubutawa daga faifai: Ibrahim Sheme