Akwai alamun cewa sauƙi ya fara zuwa masana’antar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, domin kuwa mako uku da su ka wuce ne Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wani hoɓɓasa na kyautatawa ga masu aikin fasaha da basira na ƙasar nan. Kuɗi ne zunzurutu wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 200 ya bayyana bayarwa ga masu sana’ar nishaɗantarwa a matsayin rance don haɓaka sana’ar su. A kuɗin Nijeriya, sun kama kimanin naira biliyan 30.
Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne a Legas, a wurin bikin cikar shahararren kamfanin nan masu gidajen silima da shirya gasar sarauniyar kyau mai suna Silverbird Group shekara 30 da kafawa. Mamallakin kamfanin, wato tsohon Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Mista Ben Murray-Bruce, shi ne ya roƙi shugaban da ya yi wani abu don karrama masana’antar, wadda ta ƙunshi masu shirya fim da kuma mawaƙa. Jonathan, wanda ya halarci taron da kan sa, ya ce wannan jari da gwamnati ta zuba an yi shi ne “ba don komai ba sai don a mara wa masu sana’ar fasaha baya da kuma haɓaka masana’antar mu ta nishaɗantarwa.”
Mutane da yawa da ke da ruwa da tsaki a masana’antar sun yi murna da wannan kuɗin, su na ganin su a matsayin agajin da ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sa, wato a daidai lokacin da ruwa ya kusa ƙare wa ɗan kada. Su na ganin sa a matsayin wata babbar karramawa da amintaka ga gudunmawar da waɗannan ɗimbin masu basirar su ka bayar wajen sa a ƙara sanin Nijeriya a fagen ayyukan nishaɗi, wato fim da waƙa.
Nollywood, wadda masana’anta ce da ke bunƙasa a ko yaushe, ta na tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da masana’antar da ta girme ta a fagen, wato ta kiɗa da waƙa. Duk an san su a duniya. A wani rahoto da hukumar UNESCO ta buga a cikin watan Mayu 2009, an bayyana cewa masana’antar Nollywood ce ta uku a duniya wajen fito da yawan finafinai, wato ta na bin masana’antar Hollywood ta ƙasashen Turawa da kuma Bollywood ta ƙasar Indiya. An ƙiyasta cewa darajar Nollywood ta fuskar kuɗi ta kai kimanin dala miliyan 250, kuma akwai mutum aƙalla miliyan ɗaya da ke aiki a masana’antar. Wannan masana’anta ta haifar da ’yan wasa waɗanda sunan su ya zama ruwan dare a cikin ƙasar nan da ƙasashen waje. Sunaye irin su Genevieve Nnaji, Omotola Jalade-Ekeinde, Ramsey Nouah, Kate Henshaw-Nuttal, Pete Edochie, Ali Nuhu, Segun Arinze, Funke Akindele, da sauran su, sanannu ne. Akwai kuma irin waɗannan sunayen a fagen waƙa. A dalilin haka, akwai manazarta da dama da ke tururuwa daga ƙasashen duniya su na zuwa nan domin yin nazarin irin tashin gwauron zabon da wannan masana’anta ke yi. Abu sai ka ce tsafi! A yau ɗin nan akwai tashoshin talabijin na satalayit da dama da ke nuna finafinan Nollywood dare da rana, ciki kuwa har da shahararriyar tashar Africa Magic, kwatankwacin yadda tashar Fox Movies ke nuna finafinan Hollywood da kuma yadda tashoshin B4U da Zee Aflam ke nuna na Indiya. Waɗannan mutane, mazan su da matan su, waɗanda yawanci matasa ne, su na rayuwa cikin jin daɗi a matsayin attajirai, a cikin aikin da su ka ƙirƙira da kan su, ba tare da sa hannun hukuma ba.
To amma kuma akwai mutanen da ke kallon wannan garaɓasa da Jonathan ya yi ga ’yan fim da mawaƙa a matsayin wani abu bambarakwai. Su na ganin cewa ya yi abin ne da ka kawai, ba tare da ya numfasa ya yi tunani ba, don kawai Mista Murray-Bruce ya roƙe shi da ya yi masu ko ma menene don nuna kulawa. Tun daga lokacin da aka bayyana garaɓasar, na ji ‘yan fim da mawaƙa da dama su na yin wasu tambayoyi a kan ta: Shin wannan kyautar yaudara ce ko kuwa? Shin siyasa ce? Shin Jonathan ya na ƙoƙarin samun goyon bayan masu sana’ar nishaɗantarwa a daidai lokacin da ’yan adawa ke girgiza kujerar sa? Shin kishin ƙasa ne ya sa ya ba da wannan babbar kyautar? Ko kuwa ma gwamnati ta na so ta yi wa ’yan fim da mawaƙa ƙofar raggo ne, wato ta biyo ta bayan fage domin ta mamaye harkar saboda gudun irin saƙwannin da ake iya jefawa a cikin finafinai da waƙoƙi?
Bayan haka, wa zai karɓo kuɗin daga hannun gwamnati a madadin ’yan fim da mawaƙan, waɗanda ba su da wasu tsayayyun shugabanni da kowa da kowa ya yarda da su? A yanzu dai, ba a ma san yadda za a raba kuɗin ba. Shugaban ƙasa dai ya ce gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) tare da ministan kuɗi su ne za su je su fito da hanyar da za a bi a fito da kuɗin da kuma yadda za a yi da su. Jonathan, a jawabin sa, ya ambaci kalmar Nollywood ne a matsayin masana’antar finafinan Nijeriya, to amma don Allah ainihi su wanene Nollywood ɗin? Da yawa in an ce Nollywood, to ana nufin ’yan fim na Kudu kenan, waɗanda ke zaune a Legas da Anacha. To su kuma ’yan fim na Hausa fa da ke Arewa, waɗanda sunan tasu masana’antar Kannywood? Sannan kuma ina sauran Wood Wood da ke akwai – misali masana’antar finafinai ta Nupawa, wadda ƙarama ce kuma ba ta kallon kan ta a matsayin wani yanki na Kannywood, da sauran wuraren da ake shirya fim cikin harsunan mu na gado? Su yaya za a yi da su? Bugu da ƙari, me ake nufi idan an ce makaɗan Nijeriya? Shin sun haɗa da masu waƙoƙi da harsunan gargajiya, irin su Nasiru Garba Supa na Kano da Musa Ɗanbade na Kaduna, ko kuma ana nufin mawaƙa na zamani masu waƙoƙin Naija irin su Dapo Oyebanjo (D’banj), Abolere Akande (9ice), Innocent Idibia (Tuface), 2-Effects da Sound Sultan? Sannan ina za a saka su Aminu Ala, Fati Nijar, Maryam A. Baba da ire-iren su? A gaskiya, akwai buƙatar a fito a yi wa jama’a bayani, kuma a fito da hanyoyin da za a bi waɗannan kuɗin su kai ga ’yan fim da mawaƙa. Idan har ba a bi a sannu ba, to wannan garaɓasa ta gwamnati za ta haifar da babban rikicin shugabanci a industiri, ta jawo rarrabuwar kai tsakanin masu fasaha a ɓangarori daban-daban.
Ni a nawa ganin, har yanzu tsugunne ba ta ƙare ba ga masu shirya finafinai da kuma buga waƙoƙi a Nijeriya. Industiri ba ta buƙatar waɗannan kuɗin. Dalili: an yanke shawarar ba da su ne kurum a cikin irin tunanin gwamnati da ya daɗe ya na addabar ƙasar nan, wato inda za ka ga an watsa kuɗi ga matsala a matsayin magani maimakon a gano dalilin faruwar cutar. Abin da masana’antar nishaɗantarwa ke buƙata shi ne a samar da kyakkyawan sararin da mutum zai yi sana’a har ya ci riba. Mu tuna, wasu ’yan kasuwa masu tarar aradu don faɗin kai ne su ka haifar da industirin Nollywood da rana tsaka kimanin shekara 18 da ta gabata lokacin da su ka fitar da fim mai suna ‘Living in Bondage’, kuma tun daga lokacin ta ke ta ƙara bunƙasa ba tare da jarin gwamnati ba. Na san cewa masana’antar ta na fama da manyan matsaloli. Na farko, matsalar da ke damun Nijeriya ma ita ke damun ta, domin abin da ya ci Doma ba ya barin Awai. Matsalolin sun haɗa da satar basira da wasu ɓarayin zaune ke tafkawa, ga rashin tsaro da kuma taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar nan. Ɗaya daga cikin manyan matsalolin ita ce satar basira, inda wani zaunannen ɓarawo zai ɗauki kayan ka ya gurza ya riƙa sayarwa, kai kuwa ko oho. Rashin ƙarfin doka da oda ya sa masu aikin basira sun kasa cin moriyar shukar su. Ɓarayin zaune sun yi masu talala. Ya kamata a fitar da su daga wannan ƙangin, su samu sa’ida.
Lokacin da hukumar UNESCO ta ce Nollywood ce ta uku a duniya, ta ba ta wannan matsayin ne a kan yawan finafinan da ake shiryawa kawai, ba wai saboda ƙarfin arziki ko kuma ingancin finafinan ba. Su finafinan mu na Nijeriya, ana shirya su ne bisa kuɗi ƙalilan, tare da yin amfani da kayan aiki masu araha. Yawanci babu ilimin abin domin su masu ruwa da tsakin ba wani horo su ka samu a makaranta ba; duk a lokeshin ake koyon komai. Shi ya sa za ka ga a finafinan ana nuno abu a duk yadda aka ga dama. Idan ka na kallon finafinan Kudu, sai ka yi tunanin cewa a ƙasar mu ba abin da ake yi sai tsafe-tsafe da aikata laifuffuka da kuma tsiraici. Rashin doka mai ƙarfi da kuma hanƙoron samun ƙazamar riba sun sa lamarin ya ƙazanta. Don haka babu mamaki, finafinan Nollowood ƙalilan ne ake ɗaukar su da wata daraja a ƙasashen da su ka ci gaba, in ban da a unguwannin da ’yan Nijeriya ke zaune, masu ƙawazucin tunowa da gida. Yanzu dubi wani fim da aka yi a Afrika ta Kudu wai shi ‘Tsotsi’, da wani da aka yi a Indiya mai suna ‘Slumdog Millionaire’. Waɗannan finafinai ne da ake ji da su a duniya. Shi ‘Tsotsi’, dalar Amurka miliyan 3 aka kashe wajen shirya shi, to amma an samu dala miliyan 10 daga nuna shi a silima. Haka kuma ya ci manyan gasa guda biyu na duniya, wato lambar Oscar (a cikin 2005) da lambar Golden Globe (a 2006) a matsayin gwarzon fim cikin harsunan ƙasashe ban da Ingilishi.
Amma mu finafinan mu na Nijeriya, ba su da labarai masu ƙarfi, sannan da an fara fim za ka iya cankar inda zai ƙare. Sakamakon haka, za ka ji ana kuka da finafinan a gida da waje. Yanzu haka a Uganda har wata mata ’yar Majalisar Dokokin ƙasar mai suna Sarah Wasike Mwebaza ta ɗora laifin ƙaruwar ayyukan tsafe-tsafe a ƙasar ga yawaitar finafinan Nijeriya a ƙasar. Gwamnatin Uganda ta na nan ta na shirin kafa dokar da za ta magance matsalar. Wannan ya nuna cewa ya kamata masu shirya finafinan mu su yi karatun ta-natsu, su mayar da hankali wajen shirya finafinai masu inganci, da nuna gwaninta wajen ba da labari, da kyan hoto da sauti. Ya kamata su nuna wa sauran ƙasashen duniya cewa ba wai neman kuɗi kawai ya sa su ke shirya fim ba, a’a har ma don su nuna bajinta a basira da fasaha. Saboda haka, kada a dubi garaɓasar da Shugaba Jonathan ya bayar a matsayin kuɗi kawai, maimakon haka a ɗauka cewa alama ce ta nuna goyon baya da kuma karramawa. Idan har aka saka ido a kan kuɗin, to ba abin da zai biyo baya sai cacar baki da rarrabuwar kai da faɗace-faɗace, daga nan kuma zancen bizines ya ƙare kenan.