BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MALAM IBRAHIM SHEKARAU
Mai Girma Gwamna,
NA rubuto maka wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ne saboda na yi amanna da cewa za ta fi saurin isa gare ka maimakon in bi hanyar da ku ka tsara, saboda ina da magana mai buƙatar sauri. Idan na miƙa wasiƙar a ofishin ka, za ta iya ɗaukar kwanaki da yawa ko ma watanni kafin ta isa gare ka, kuma kafin lokacin ba za ka iya samun bayani na haƙiƙa ta kafa mai zaman kan ta ba kan tantagaryar zaluncin da wasu jami’an ka su ke aikatawa da sunan ka. Na biyu, tun tuni ma ake ta zancen a majalisun hira a tsawon watanni da su ka gabata. Yanzu akwai alamun an jingine maganar ta hanyar wata shari’a wadda ko kaɗan ba ta da kan-gado, inda wasu masu fushi da fushin wani su ka yi amfani da aƙidar ka ta aiki bisa doka da oda, da tausayin talakawa, da rashin yaudara da kuma tanadodin Musulunci. Bugu da ƙari, buga wannan wasiƙar a bainar jama’a zai ba wa duk wani mai sha’awar sanin abin da ake ciki damar samun ƙarin haske kan ɗaya daga cikin muhimman al’amuran da ke gudana a gwamnatin ka.
Ran ka ya daɗe, ina da cikakkar masaniya kan wannan lamari, ba kawai don ina biye da maganar a kotun majistare ta Kano inda aka kai ta ba, a’a har ma saboda ni ɗan cikin gida ne a al’amuran sana’ar finafinan Hausa. Ba sai na nanata maka ba cewa Kano ce cibiyar finafinan Hausa a sama da shekara goma da aka yi ana yin sana’ar.
Na tabbatar da cewa ba za ka rasa masaniya ba kan shari’ar da ake tafkawa tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano (KSCB) da wani furodusan fim mai suna Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama. Ran ka ya daɗe, Iyan-Tama ɗan asalin Kano ne wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da harkar finafinan Hausa gaba, sannan kuma ɗan wasa ne ɗan sahun gaba. Hasali ma dai shi ne shugaban farko da aka zaɓa na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFPAN). Kowa ya san cewa bai taɓa shirya fim ko kuma ya fito a fim ɗin da za a yi Allah-wadai da shi ba, wato wanda ya saɓa wa kyawawan al’adun jama’ar Kano ko addinin Musulunci. Duk rol ɗin da zai yi a fim, za ka taras na manyantaka ne; ya kan nace kan lallai a yi fim da ya dace da al’adun mu, sannan shi mutum ne mai bin doka. Finafinan sa sun ci manyan kyaututtukan girmamawa.
Ran ka ya daɗe, idan har ka samu damar karanta wannan wasiƙar a yau, to Iyan-Tama ya kwana biyu a gidan yarin Kano, domin a ran Talata wata kotun majistare ta yanke masa hukunci kan abin da ta kira laifuffuka guda biyu, bayan an shafe watanni ana yawo da hankali a kes ɗin. A hukuncin da kotun ta zartas, Iyan-Tama zai shafe wata uku a tsare ba tare da zaɓin biyan tara ba. Haka kuma zai biya maƙudan kuɗi na tara ko kuma ya yi zaman kaso na tsawon shekara ɗaya.
Yawancin mu da ke sa ido kan lamarin ba za mu damu ba ko kaɗan da hukuncin in da a ce da gaske Hamisu ya aikata laifuffukan. Ni ɗin nan na yarda da bin doka da oda, domin hakan shi ne ginshiƙin ɗorewar mulkin dimokiraɗiyya. Ba wanda ya fi ƙarfin doka. In an yi amfani da wannan tsarin ne dimokiraɗiyya za ta iya ɗorewa kuma ƙasa za ta samu zaman lafiya. To amma gaskiyar magana ita ce, Hukumar Tace Finafinai ce ta ƙirƙiri laifukan da aka ce Iyan-Tama ya aikata, sannan wani alƙali mai goyon bayan hukumar, wanda kuma ya yi ƙaurin suna wajen ɗaure duk wani wanda aka gurfanar a gaban sa, ko da bai da laifi, shi ne ya yanke masa wannan ɗanyen hukuncin. Wani abin ban-damuwa shi ne ana tafka wannan aika-aikar ne da sunan tanadojin nan masu tsarki na Shari’ar Musulunci. Daga fahimta ta da abubuwan da ke fitowa daga bakin ka da ganin wasu abubuwan da ka aikata, har yanzu ban amince ba da cewa kai ɗin nan za ka goyi bayan zalunci ta kowace fuska ko kuma ka bar wani ya na saka siyasa cikin shari’ar Musulunci don ya ci mutuncin jama’a cikin son rai.
’Yallaɓai bari in ɗan faɗa maka abin da ya faru. Jami’an Hukumar Tace Finafinai sun kama Iyan-Tama a ofishin sa a Kano, su ka kai shi kotun tafi-da-gidan-ka wadda aka kafa don yi wa ’yan fim da marubuta shari’a (aka faɗaɗa zuwa duk wani nau’i na rubutu). Abin mamaki, babu wata kotu irin ta; babu kotun ’yan acaɓa ko ta karuwai ko ta ’yan caca ko ta ’yan luwaɗi, da sauran su. An tuhumi Iyan-Tama da “laifuffuka” guda biyu:
1. Sakin fim ɗin sa na ‘Tsintsiya’ a Kano ba tare da Hukumar Tace Finafinai ta amince da shi ba kamar yadda doka ta tanada;
2. Gudanar da kamfanin shirya fim mai suna Iyan-Tama Multimedia ba tare da yin rajista da gwamnati ba.
To amma duk waɗannan tuhumar, ƙarya ne, kuma lauyan sa ya yi ƙoƙarin nuna wa alƙali Alhaji Mukhtar Ahmed hakan. An ɗauki watanni kafin a yanke hukuncin, wanda ya yi matuƙar girgiza yawancin mazaunan Kano da wajen ta.
Bari mu fara da tuhuma ta biyu. An yi wa kamfanin Iyan-Tama Multimedia rajista da gwamnati, wato a Corporate Affairs Commission (CAC), wadda ke da alhakin yi wa dukkan kamfanoni rajista a Nijeriya. Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta ce wai Iyan-Tama bai sabunta rajistar sa ta shekara-shekara da ita ba. Wannan ma ƙarya ce domin watanni kafin a kama shi, ya sayi fom ɗin har an ba shi rasiɗai. To wanda ya yi wannan yunƙurin ai ya na kan hanyar yin rajistar ne kuma bai yi kama da wanda ke ƙoƙarin karya dokar yin fim a Kano ba. Kuma ya na da amincewar Gwamnatin Tarayya.
Tuhuma ta farko ma ta fi ban-haushi. Ran ka ya daɗe, Iyan-Tama bai saki fim ɗin ‘Tsintsiya’ a Kano ba. Hasali ma dai ya yi tallace-tallace da hirarraki a rediyo da jaridu kafin a ƙaddamar da fim ɗin a Abuja, inda ya fito ƙarara ya ce ba za a saki fim ɗin a Jihar Kano ba.
A lokacin da Hukumar Tace Finafinai ta yanke shawarar “koya wa Iyan-Tama darasi,” jami’an ta sun karya shagon saida finafinai na HRB da ke unguwar Tarauni a Kano, su ka samo faifan sidi na fim ɗin, wanda wani ɗan wasan fim ya ɓoye cikin durowar teburi wanda ya ce a Kaduna ya sayo shi da nufin zai ba wa wata mai sha’awar finafinan sa. Ba wai an kasa sidi ɗin don sayarwa ba. Ɓullar sa a Kano bai da wata alaƙa da Iyan-Tama. Idan ka karanta takardun kotu inda lauyoyi ke yi wa jami’an Hukumar Tace Finafinai su biyu tambayoyi a gaban alƙali, za ka yarda ɗari bisa ɗari cewa ba a tabbatar da cewa Iyan-Tama ne ya kawo faifan sidi ɗin wannan shagon ba.
A bayyane yake cewa shari’ar Iyan-Tama ramuwar gayya ce kurum. Wani ɓangare ne na yunƙurin yaƙi da wasu ’yan fim ko ta halin ƙaƙa wanda Hukumar Tace Finafinai ta ɗaura. A gajeren tunanin hukumar, ta hanyar yin haka ne za a iya share duk wani abu na sana’ar fim da harshen Hausa. Hukumar ta na amfani da baƙar farfaganda, ta na ba da bayanan ƙarya, tare da yin ragguwar fassarar Dokar Tace Finafinai ta 2001, sannan ta na amfani da sunan Musulunci ta hanyar da ba ta Musulunci ba wajen sauya alƙiblar hanyoyin nishaɗi a Kano.
Mai girma Gwamna, duk wannan ya saɓa wa furucin ka na tabbatar da adalci. Kuma hakan ya haifar da abubuwa marasa daɗi ga gwamnatin ka da kai kan ka, waɗanda zan faɗa maka su yanzu tare da duk girmamawa a gare ka.
Ya mai girma Gwamna, yaƙin da ake yi da sana’ar fim a Kano, ana yin sa ne da sunan Shari’ar Musulunci, to amma ko kaɗan ba Musulunci ba ne. Waɗanda ke yin yaƙin sun yi gangami ne su na furta kalaman Alƙ’ur’ani mai tsarki da Sunnar Manzo, to amma abubuwan da su ke aikatawa kai ka ce Hitla ne ya ce su aikata shi. Babu wani abu da su ka aikata kan ’yan fim da ya nuna cewa sun bi nasihohin Annabi Muhammadu (SAW). Kamar yadda na faɗa a sama, tsarin da su ke bi na halaka sana’ar fim ta na da illa matuƙa, ba wai kawai ga ’yan fim ba har ma ga gwamnatin Jihar Kano. Zan ɗan bayyana wasu daga cikin illolin yanzu:
1. An jefa dubban matasa cikin rashin aikin yi bayan kuwa a da su ne su ke sama wa kan su hanyoyin abinci, wanda hakan ya shafe su tare da iyalan su. Ba a sama masu wasu hanyoyin na daban ba domin samun abinci. Mayaƙan ka su kan ce, “Ina ruwan mu da su? Ai yawancin su ba ’yan Kano ba ne!” To amma hakan ya saɓa wa ƙoƙarin gwamnatin ka na sama wa ɗimbin matasan Kano aikin yi.
2. Yaƙin ya kawo koma-baya ga tattalin arzikin Kano wanda da ma ya na cikin garari. Da yake manyan kamfanonin Kano duk sun durƙushe, kamata ya yi a gina harkar fim ta yadda za ta kasance mai dogaro da kan ta, kuma wadda ta dace da al’adun Kano da dokokin hukuma. Maimakon a yi hakan, sai aka koma ana kashe ta.
3. An haifar da fargaba da rashin sanin alƙiblar rayuwa a zukatan matasan, kuma da yawan su sun koma ’yan maula.
4. An haifar da ƙin Shekarau a zukatan matasan. Hujja ita ce irin waƙoƙin ɓatanci da ke ta bayyana daga situdiyoyin waƙoƙin finafinai a Kano, Zariya da Kaduna. Da fari, irin waɗannan waƙoƙin su na sukar Hukumar Tace Finafinai ne, to amma yanzu akalar su ta sauya har su na haɗowa da gwamna da iyalin sa. Kai, waƙar da ta fi yin fice a wannan fagen ma, an shirya ta ne a situdiyon da wani na hannun daman ka ya mallaka, to amma Hukumar Tace Finafinai ta kasa yin komai a kai saboda shi mai situdiyon ba ya taɓo a gare ta. Wannan tsanar da ake yi wa Shekarau ta na ta ƙaruwa kuma za ta iya kasancewa baƙar guguwa ga jam’iyyar ANPP a zaɓen da za a yi a shekarar 2011 a Jihar Kano.
5. An fara yin shakku kan manufa da kuma alƙiblar yekuwar Shariar Musulunci, wadda miliyoyin jama’a su ka runguma. Duk shugaban da ke yin nasihar adalci da gyaran tarbiyya, bai kamata ya hana dubban matasa hanyoyin samun abincin su ba.
Ran ka ya daɗe, ina daga cikin masu goyon bayan shirin ka na gyaran zamantakewar jama’a ta yadda za su yi daidai da al’adu da tanadodin addinin da jama’ar mu ke bi. Shi ya sa na ke goyon bayan shirin gwamnatin ka na A Daidaita Sahu, wanda abokin mu Malam Bala Muhammad ke aiwatarwa cikin ban-sha’awa da kuma samun cikakkar nasara. To amma Hukumar Tace Finafinai ta na warware duk wata tufka da A Daidaita Sahu ta cimma nasarar yi. Gaba ɗaya tsarin a bauɗe ya ke, kuma ana aiwatar da shi a kan tafarkin mugunta da ramuwa da rashin jin ƙai. Ya kauce wa duk wani tsari na ya-kamata.
Mun yarda da cewa sana’ar finafinai ta shiga ruɗu wanda ya kamata a gyara ta a cikin shekarun baya. Hakan ya ƙara bayyana ne bayan ɓullar majigin batsa na Hiyana. To amma akwai buƙatar a jawo shugabanni na sosai na industiri ɗin don a samu nasara. Maimakon haka, sai Hukumar Tace Finafinai ta ture su gefe ɗaya, ta jawo wasu ’yan koren ta, sannan ta na shirya tarurruka na yaudara da rainin wayo, har ma da shirya dina don magoya bayan ta su zo su ci abinci. Ba shakka, wannan tsarin na raba kan jama’a da farfaganda irin ta ’yan Nazi da hukumar ke yi ba abin da ya haifar sai bala’o’i, sannan an samu gazawa a wajen gyaran tarbiyyar industirin finafinan Hausa.
Har yanzu ana sayar da finafinai da fosta-fosta na batsa a Kano. Haka kuma, ’yan ƙalilan ɗin finafinan Hausa da magoya bayan Hukumar Tace Finafinan su ka shirya (tare da amincewar hukumar don a ɓoye ƙaryar cewa ba kashe sana’ar fim ake yi ba) ba su da wani bambanci da irin finafinan da hukumar ta ke iƙirarin cewa marasa inganci ne. Don Allah, finafinai masu inganci kuma “waɗanda sun dace da tarbiyya”, guda nawa ne aka shirya a ƙarƙashin jagorancin Hukumar Tace Finafinan tun daga lokacin da majigin Hiyana ya fito?
Ran ka ya daɗe, za ka yarda da ni idan na ce maka ainihin dabarar shirin fim ba aba ce mai illa ba, don haka bai kamata a kashe ta ba. Za a iya shirya finafinai kan jigogin rayuwa iri-iri waɗanda su ka dace da al’adun mu. Kamata ya yi a yi wa ’yan fim jagora, ba wai a riƙa yi masu ɓatanci ba ko kuma a yi masu korar kare daga gari.
Ran ka ya daɗe, Hamisu Iyan-Tama dai fursunan siyasa ne: ya yi adawa da kai lokacin zaɓen 2007 ta hanyar fitowa takarar gwamna shi ma. Ai bai ma yi maka wata barazana ba. Kai aka ƙara zaɓa. To amma saboda tsaurin idon da su ke ganin ya yi na yin takara da kai, jami’an ka su na hukunta shi. Sun ce wai shi mutum ne mai cika baki, mai surutu kuma wai ya na sukar gwamnatin ka. To mun ji, shin su ɗin ba masu cika baki ba ne, su na yin abu sai ka ce sun fi kowa iko a duniya? Shin ba sa kallon duk wani wanda bai yarda da ra’ayin su ba a matsayin abokin gaba ko su kafirta shi, ko maras bin biyayya gare su, ko su ce ai ba ɗan Kano ba ne ko kuma bai san ainihin abin da ake ciki ba? Shin wannan ba babbar ɗagawa ba ce?
Kuma ma ko da a ce Iyan-Tama na da cika baki ko kuma abokin adawar ka ne na siyasa, shin hakan hujja ce ta hukunta shi da zaman gidan yari duk da yake bai karya doka ba? Shin ya yi maka illa a siyasance irin illar da masu surutan nan ke yi maka a gidan Rediyon Freedom? Shin a ina dimokiradiyyar da ake ta magana ta ke? Shin ko Manzon Allah (SAW) ko wani daga cikin halifofin sa ko ɗimbin tabi’an da su ka biyo bayan su za su bi irin wannan hanyar don hukunta abokin adawa?
Mai girma Gwamna, ya kamata ka binciki wannan al’amari na Iyan-Tama, don Allah, musamman rawar da alƙalin da ya ɗaure shi ya taka a shari’ar da sauran shari’un zalunci da ya yi wa masu sana’ar fim. Kuma don me za a ce kotu ta na yi wa wata hukumar gwamnati aiki? Don me alƙali ɗaya ne kaɗai zai riƙa yin duk wata shari’a da ta haɗo da Hukumar Tace Finafinai bayan an ga sau da yawa ya nuna inda bakin sa ya karkata? Shin wannan mutum ne mai tsoron Allah ko kuwa ɗan siyasa mai ƙullatar jama’a?
Ka yi amfani da ƙarfin mulkin ka ka fitar da Iyan-Tama daga ƙangin da aka saka shi a ciki ta hanyar janye ƙarar da ku ke yi da shi a kotu. Na san ka na da zuciyar yin hakan domin ai ka taɓa yin irin haka a wasu al’amura da su ka haɗo da kai, ciki kuwa har da wanda ya haɗo da ɓatanci da aka yi wa maiɗakin ka. Kada ka bari wasu mutane ’yan ɗoki waɗanda ka ba muƙamai su riƙa yaƙar abokan adawar ka ta hanyar zalunci domin kuwa Gobe Ƙiyama za ka amsa tambayoyin ka ne yayin da za su amsa nasu daban da naka.
’Yallaɓai, zan tsaya a nan, sai a nan gaba za mu ƙara yin wannan magana da sauran maganganu. Ni ne mai biyayya a gare ka, kuma mai ba ka shawara tagari. Wassalam.
(Wannan fassara ce na sharhin Turanci da na yi kwana baya. An wallafa wannan na Hausan a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a da ta wuce)