Taƙaitaccen Tarihin Malam Ibrahim Ɗanmani Caji

Malam Ibrahim Ɗanmani Caji a Kaduna a cikin 1974

Ba a san takamaiman shekarar da aka haifi Malam Ibrahim Ɗanmani Caji ba, amma ana hangen an haife shi ne a tsakanin shekarar 1905 zuwa 1909, wato jim kaɗan bayan Turawan mulkin mallaka sun ƙwace ƙasar Hausa. Inda za ka gane tsufan sa shi ne ya taɓa faɗa da bakin sa cewa ya fara waƙa ne a wajen shekarar 1927.

Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Ɗanmani Caji ko Malam Ɗanmani Bauchi, shahararren mawaƙin Hausa ne wanda ke ajin farko na makaɗa irin su Hamza Caji, Musa Daɓalo, Nagelu da Ibrahim Narambaɗa. Ya yi fice tun kafin a san da irin su Mamman Shata da Musa Ɗanƙwairo. Hasali ma dai, lokacin da ya fara waƙa, Shata ya na goye!

An haifi Ɗanmani Caji a Sakkwato. A can ya yi makarantar allo har ya sauka, ya shiga littattafai. Ya yi zurfi ƙwarai a karatu, domin har ya fara zama matashin malami, kafin ya bar gida ya tafi garin Kaduna domin ya gano wani wan sa wanda ya jima da barin gida.

Ban sani ba ko ya ga wan nasa, amma a Kaduna ne ya fara rera wata waƙa wadda ya shirya daga wani Hadisi na Manzon Allah (s.a.w.), wanda ya sa ya kasance cikin mawaƙan bege waɗanda masana adabi ke kiran su “mawaƙan madahu”. Su, Hadisai su kan ɗauka su shirya waƙa a kan su, kuma waƙar su babu kiɗa ko ‘yan amshi. Idan su na yi, sai a riƙa ba su kyautar kuɗi ko ta tufafi ko ta abinci. Ɗanmani ya zama mawaƙin madahu a wajen shekarar 1927.

Daga Kaduna, sai ya koma Kano inda ya ci gaba da waƙar Hadisi. A can ya zama yaron mota, ya na sana’ar sa ya na yin waƙe-waƙen sa na Hadisi. Rannan sai ubangidan sa da su ke aikin mota tare, mai suna Ibrahim Nadada, ya yi sanadin sanya shi fara waƙa da ganga. Yadda abin ya faru shi ne, wasu makaɗa su ka zo su na kiɗan caji a garejin da Ɗanmani ke aiki, sai Ibrahim Nadada ya kira Ɗanmani ya ce masa ya rera waƙar nan tasa ta Hadisi a kaɗa masa ganga. Shi kuma ba ya so, domin shi malami ne, ba maroƙi ba. Duk da haka, sai ya rera, ana ba shi kiɗa. Tun daga ranar, sai son ya rera waƙa da kiɗan caji ya shiga ran shi. Amma idan an ba shi kyauta sai ya ƙi karɓa domin ba ya so a ce ya zama maroƙi.

A wancan zamanin, makaɗan da ke tashe a Kano makaɗan kotso ne da na caji; su ne ke zuwa fada ko ƙofar gidan attajiri su yi wasa su samu kuɗi da tufafi. Manyan cikin su dai su ne Hamza Caji da ƙanen sa Inu Caji da Musa Daɓalo da Nagelo. Mamman Shata? Ina! A lokacin bai ma fara waƙa ba!

Ɗanmani ya koyi kiɗan caji daga waƙoƙin Hamza Caji har ya kafa tasa rundunar ta masu buga masa ganguna da ‘yan amshi, wato ya zama maroƙi. Ya watsar da aikin mota. Amma fa bai zauna a ƙarƙashin Hamza ko Inu ɗin ba, ya dai ɗauki samfur ɗin kiɗan Hamza ɗin ne, ya tafi ya na yi har wasu na zaton cewa Hamza ne. Ɗanmani bai bi wani mawaƙi ba.

Waƙar farko da ya fara yi da kiɗan caji, ya ji ta ne a wajen “wani Alhaji” mai waƙar bege, wanda bai san ko wanene ba. Ya dai ji shi ya na rera ta. Abin mamaki, ita wannan waƙa ita ce ta zama waƙar da ake kira “Waƙar Ɗanmani”, mai amshin ‘Ya Yi Magani, Mai Sama Ya Ba Da Magani Ba Ƙarya Ba’. A cikin ta ne ya ke cewa, “A Sakkwato an ka haifi Malam Ɗanmani, amma a Kano an ka yaye Malam Ɗanmani”. Ka taɓa jin inda waƙar farko ta mawaƙi ta zama bakandamiyar sa? Sai a wannan waƙa ta Ɗanmani Caji. Wannan waƘa ita ce wadda ta sa – wato ta yi “inspiring” – Malam Aliyu Namangi ya rera waƙar sa ta ‘Basukur, Hawan Ka Sai Mai Zanzaro’.

A matsayin sa na mawaƙi, Malam Ɗanmani ya yi tafiye-tafiye cikin Nijeriya, daga Arewa har Kurmi. Kuma ya je Kamaru da Nijar. A Kamaru ma ya zauna a ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Ahmadu Ahidjo, har ya yi gidan kan sa a Gamdare. A nan ya kasance mai masaukin baƙin maroƙa da ke zuwa Kamaru daga Nijeriya domin su ci arzikin Ahidjo.

Tun a zamanin Sardauna ya yi gida a Bauchi inda ya ci gaba da zama tare da iyalin sa har zuwa ƙarshen rayuwar sa. A gidan sa akwai makarantar allo, kuma shi ma ya kan koyar. A yanzu haka a gidan akwai wata tsohuwa, jikanyar sa, ta na zaune tare da wasu dangin su. Ɗaya daga cikin sanannun waƙoƙin Ɗanmani ita ce waƙar Sarkin Bauchi Alhaji Adamu Jumba mai taken ‘Mai Rabo Ga Allah Ɗan Sanda Mai Martabobi’.

Wasu waƙoƙi fitattu na Malam Ɗanmani sun haɗa da waƙar Sarkin Mubi mai taken, ‘Babban Bajimi Mai Ratsa Maza, Ɗan Garba Shiri Nai Yai Daɗi’, da ‘Waƙar Shede’, da waƙar Ahidjo, da kuma wata wadda ta ƙara fito da shi, wato waƙar ‘Ayyaraye Akwara’, wadda ya ƙirƙira a garin Gusau. Wannan waƙa ta ‘Akwara’ ta ja hankalin mutane matuƙa domin ya yi ta ne babu kiɗa. Ana ma jin cewa ita ce ta saka wa Shata tunanin yin waƙa babu kiɗa shi ma, wato waƙar ‘Kwalam!’ da ma wata bakandamiya wadda babu kiɗa. Dalili shi ne Ɗanmani ya yi waƙar ‘Akwara’ ne tsawon lokaci kafin Shata ya yi nasa babu kiɗa. A cikin ‘Akwara’ ya kan ce:

“Daɗin duniya tuwo, daɗin duniya fura ba fa daɗin ba kenan,

Daɗin duniya ka hau doki har ka na ta gaba, ba fa daɗin ba kenan,

Daɗin duniya sa girken saƙi da wando, ba daɗin ba kenan,

Daɗin duniya kai kwance da masoyi ka karye ka ɗan yi tuma!

Mai kaza ba zai ci kai da ƙafa ba, sai dai a sake rabo.”

Idan kun tuna, Garba Liyo mai kukuma ma ya ɗauki waɗannan kalmomin ya rera wata waƙar sa da su, inda ya ke cewa:

“Daɗin duniya tuwo, ba daɗi ba ne ba,

Daɗin duniya fura, ba daɗi ba ne ba,

Daɗin duniya zama da masoyin ka.”

Tun sama da shekaru arba’in da su ka gabata, Malam Ɗanmani ya hango taɓarɓarewar sana’ar roƙo da kaɗe-kaɗen gargajiya. A wata hira da Adamu Salihu ya yi da shi a Yerwa, Maiduguri, aka watsa a rediyon BCNN a cikin 1966, mawaƙin ya bayyana cewa kaɗe-kaɗen gargajiya su na gushewa, duk da yake akwai masu son su.

RIGIMA DA SHATA

Ba zan rufe ba sai na ce wani abu kan wani al’amari wanda ya ƙara fito da sunan Malam Ɗanmani, wato rigimar su ko cacar bakin da su ka yi da Alhaji Mamman Shata Katsina. Kamar yadda na labarta a littafin tarihin Shata mai suna ‘Shata Ikon Allah!’ hakan ta faru ne sanadiyyar adawar da Ɗanmani ya yi da wata waƙa da Shata ya yi, mai taken ‘Na Ga Sakarci Wurin Karuwai’, a kan korar karuwai daga Kano da Sarki Muhammadu Sanusi ya yi, har Ɗanmanin ya maida masa da martani. Shata ya zafafa lamarin duk da yake bai kai inda ake tsammani ba. Ya yi wa Ɗanmani zambo fiye da biyu a kan lamarin, har abin ya zama kamar cin ƙwan makauniya. Zambon farko shi ne ‘Don Sallah Da Salatil Fatih, Don Allah Mata Ku Bi Aure’. Hasali ma dai a cewar Shata, kafin lokacin bai taɓa yi wa kowa zambo muraran ba. Kuma ma a binciken da na yi, Shata ba ya kama sunan mutumin da ya yi wa zambo kai-tsaye, sai dai ya sakaya ko ya kwatanta, amma sai a kan Malam Ɗanmani.

A nazarin da na yi wa lamarin, ce-ce-ku-cen Shata da Ɗanmani ya na da tarihi daban, ba wai kan waƙoƙin korar karuwai ba ne. Tun daga bikin ‘yan Sarki da aka yi a Kano a farkon shekarun 1950, inda Shata ya cinye kasuwar, aka ƙulla adawa wadda ta zama gaba a tsakanin sa da kusan dukkan makaɗan caji, waɗanda har ya kama sunayen su a wata bakandamiyar sa, wato su Ɗanmani Caji, Hamisu da Daɓalo. Ya yi masu haka ne ganin ƙulle-ƙullen da su ka yi masa don hana shi haskawa a bikin ‘yan Sarki. Haka kuma makaɗan caji na jin haushin yadda Shata ya karɓe fada a Kano, a matsayin sa na makaɗin kalangu, domin kafin hasken sa a Kano manyan makaɗa su ne na caji da na kotso, musamman a gidajen sarakai; sai ga Shata ya kutso da kalangu ya ture su gefe ɗaya.

Don haka, ba abin mamaki ba ne da Ɗanmani, wanda ake masa kallon malamin allo a cikin da’irar mawaƙa, ya yi musu da Shata kan korar karuwai. Wani abu kuma shi ne a lokacin, Ɗanmani ne sarki ko gogarma a fagen kiɗan caji, musamman tunda Hamza da Daɓalo sun kauce. Amma saboda Shata Shata ne, wannan cacar bakin ta ƙara fito da Ɗanmani.

Kada mu manta, Shata ya yi irin wannan adawar da wani gungun makaɗan da su ka taɓo shi, har abin ya jawo ce-ce-ku-ce da hayagaga, wato makaɗan kukuma da banjo, waɗanda ya kira sana’ar su da “wargin yara”. Ahmadu Doka ya ba shi amsa, daga baya kuma ya yi nadama.

Ɗanmani ya yi tsufan sa a Bauchi, ta yadda har wasu na tsammanin ɗan asalin Bauchi ne. Sunan sa ma Ɗanmani Bauchi.

Ban binciko shekarar da Malam Ɗanmani ya rasu ba, amma na san a Bauchi ya rasu a lokacin da tsufan sa ya kai tsufa matuƙa.

Allah ya rahamshe shi, amin.