Sai bango ya tsage…

Idan har wannan makon ya }are jam’iyyun adawa na siyasa a Nijeriya ba su ha]u su ka fito da ]an takara guda ]aya da za su shigar a za~en watan Afrilu ba, to kawai mu ]auka cewa duk a cikin su babu wanda zai iya doke Dakta Goodluck Jonathan – ko an yi za~e ba magu]i ko kuma an yi za~e da almundahana. Abin da ya sa na yi wannan kintacen shi ne amannar da na yi cewa a yanzu kam, kawunan wa]annan jam’iyyu da ke kiran kan su jam’iyyun siyasa duk a rarrabe su ke a kan batun yin wani gagarumin shiri don za~en, kuma babu wata }wa}}warar alama da ke nuna cewa za su iya zama su baje komai a faifai a cikin mako ]aya.

Yanzu hankalin jam’iyyun a tashe ya ke a daidai lokacin da wa’adin da Hukumar Za~e ta {asa (INEC) na su kawo sunayen ’yan takarar su ya kusa cika. Dalili shi ne fargabar da ta cika zukatan jam’iyyun ganin cewa yanzu Jonathan ya samu tikitin tsayawa takarar a }ar}ashin inuwar jam’iyyar PDP, wanda ya }ara masa }arfi fiye da yadda ya ke kafin a yi za~en fidda gwani na jam’iyyar mako uku da su ka gabata, kuma akwai alamun lallai zai iya lashe za~en da za a yi a Afrilu. Yanzu akwai bayyanannun alamu masu nuna cewa idan har jam’iyyun adawa ba su ha]u su ka mara wa ]an takara ]aya baya ba, to ham~arar da Jonathan da kaifin }uri’a zai kasance tamkar ]aukar Kano ba gwammo.

Akwai tarurrukan da ake ta yi don tabbatar da an cimma hakan, to amma har yanzu babu wanda ya haifar da ]a mai ido. A ran Juma’a ta makon jiya, jaridu sun ruwaito labarin wani taro da aka yi “a asice” tsakanin Malam Nuhu Riba]u na jam’iyyar ACN da Janar Muhammadu Buhari na CPC a gidan shi Buharin da ke Kaduna. An ce an yi taron ne da nufin fito da hanyoyin da za a bi a }wace mulki daga hannun Shugaba Jonathan. Wannan tunanin ya yi daidai da }o}arin da ake ta yi na ganin cewa mulki ya dawo arewa a za~e mai zuwa.

To amma ko wannan yun}urin zai yi nasara kuwa? Kai mai karatu, ka ma fi ni sanin amsar. A ha}i}anin gaskiya, jam’iyyun adawa na }asar nan dai duk jam’iyyun son rai ne. Kowane ]an adawa so ya ke a ce shi ne a saman sauran, shi ya sa bai yarda da duk wata yarjejeniyar a ha]u a fidda jaki daga duma in ban da wadda za ta ba shi karsashi. Duk wani taro nasu ya na }arewa ne a fayau domin duk wanda ya je taron ya na zuwa ne da }o}on barar don-Allah-wane-ka-bar-mani.

Ba sai mun wahala ba wajen gano abin da ke janyo hakan. Ita siyasar adawa da ake yi a Nijeriya a yau, ba irin ta da ba ce. Yanzu babu ~ur~ushin a}ida a jam’iyyun, wanda hakan ya sa su ka kasance tamkar ’yan biyu masu kama ]aya in ban da ta wajen sunayen su. Amma su kuwa jam’iyyun zamanin da, lokacin da duniya na kwance lafiya, wato jam’iyyun Jamhuriya ta Farko irin su NCNC, NEPU, UMBC, da AG, da na Jamhuriya ta Biyu irin su UPN, NPP, GNPP, da PRP, an kafa su ne bisa wata a}ida. Duk mutanen da je jagorantar su ko su ke cikin su mutane ne da su ka kafe kan abin da su ka yi amanna da shi, ba wai don su na tunanin cewa amannar su ]in za ta kawo masu dukiya ko suna ba, a’a sai domin sun yarda babu kokwanto da cewa hakan ita ce hanya mafi sahihanci da za a bi a gyara al’umma kuma a gina }asa.

Gidan yanar Wikipedia da ke intanet ya bayyana cewa a}idun siyasa sun kasu ne gida biyu: 1. Buri: Wato yadda ya kamata al’umma ta rayu ko a tsara ta, sai na 2. Gwadabe: Wato hanya mafi dacewa da za a bi a cimma shi wannan burin. Shi ya sa a }asar Amurka za ka taras da cewa mutum ko dai ya na jam’iyyar Democrat ne ko kuma ya na jam’iyyar Republican; a Birtaniya kuma ko dai ka na jam’iyyar Labour ne ko ka na ta Conservative. Ban da wa]annan, babu wasu manyan jam’iyyu, illa wasu }ananan jam’iyyu da ke gefe guda don kula da mutanen da su ke ganin ra’ayin su ya bambanta da na wa]annan ]in.

Ka lura, ita a}idar siyasa kamar addini ce: mutum ba ya ficewa don kurum kwa]ayin wata ganima da ya hango. Mutane su kan ha]e ne saboda sun yi amanna da wasu muradai da aka tsara, wanda shi ne ke sa su su yi wani abu a siyasance tare da yin aiki da kundin a}idar su. Ba su ha]uwa don kawai a taru a ci abin }walamar da ke kan tebur ko don a yi ginsamin abin jefawa cikin aljihu.

A yau, labari ya bambanta. Sai ka ga gungun mutane su na ta nin}aya a tekun siyasa, su na sanye da bajen wai su ’yan siyasa ne. Duk }ibar su, mayunwata ne kawai, kuma yunwar da su ke ji (ta giyar mulki ko ta naira) ita ce ke tunzura su, ba wai a}ida ba. Shi ya sa ba mamaki ka ga yadda ’yan siyasar da su ka yi suna a matsayin ’ya’yan wata jam’iyya, an wayi gari sun yi tsalle sun auka wata jam’iyyar, ko da kuwa sun yi shekaru su na ~ata ta. Ana kiran wannan halayyar wai sauyin she}a, kuma ’yan siyasa da dama a wannan }asa tamu su kan yi hakan cike da alfahari, kuma iya }arfin su, a yayin da kuma su ke borin kunyar cewa wai an }i jinin su ne a ]aya jam’iyyar. Misalin irin wa]annan ’yan siyasa bai da adadi. An za~i Alhaji Atiku Abubakar a matsayin gwamna a }ar}ashin PDP a shekarar 1999, to amma lokacin da wasa ya yi tsami tsakanin sa da Obasanjo sai ya kafa jam’iyyar AC, wadda ta lashe za~e a Jihar Ikko. A yau, ya dawo PDP, jam’iyyar da ya so ganin bayan ta, har ga shi ya nemi zama ]an takarar ta na shugabancin }asa. Alhaji Aminu Bello Masari babban ]an PDP ne, wanda shi ne kakakin Majalisar Wakilai na tsawon shekaru. A yau, ya na takarar gwamna a jam’iyyar CPCa Jihar Katsina. Dora Akunyili ma ’yar PDP ce wadda ta ri}e mu}amin ministar ya]a labarai da sadarwa a }ar}ashin shugabannin }asa har biyu; a yau, ’yar takarar zama sanata ce a }ar}ashin jam’iyyar APGA a Jihar Anambara. Dakta Abba Sayyadi Ruma, wanda a da babban ]an PDP ne, inda har ya ta~a zama sakataren gwamnati a Jihar Katsina kuma daga bisani ya zama ministan aikin gona, yanzu ya na takarar gwamna a }ar}ashin CPC. Shi ma Sanata Adamu Aliero jagora ne a PDP a da, amma yanzu ya na takarar zama sanata a }ar}ashin CPC a Jihar Kebbi. Malam Nuhu Riba]u wani jigo ne a gwamnatin PDP a zamanin Cif Olusegun Obasanjo, amma yanzu ]an takarar zama shugaban }asa ne a }ar}ashin ACN. Alhaji Attahiru [alhatu Bafarawa ya zama gwamnan Sakkwato ne a }ar}ashin ANPP, amma ya tafi ya kafa jam’iyyar DPP har ya yi mata takarar zama shugaban }asa a za~en 2007, amma a yau }usa ne a ACN, inda kwanan nan ya nemi tsayawa takarar shugaban }asa. Kai, lissafin bai kammaluwa.

A yanzu wa]annan mutanen da ire-iren su su na nuna mana cewa su wasu mahajirai ne da aka cuta a baya. To amma kowa ya san cewa sun canza she}a ne don kawai an tokare su a jam’iyyun su na baya, kuma za su iya komawa inda su ka fito da zarar sun samu mulki ko kuma sun ga babu sa’ida a inda su ka zo. Dalili kuwa, su a wurin su ai siyasa ba addini ba ce. Sai ka ce ba su ma san ma’anar kalmar ‘a}ida’ ba. Shi ya sa su ke watangaririya daga wannan jam’iyya zuwa waccan ba tare da jin kunya ko tsoro ba, sai ka ce }udan zuma mai neman furen kallo don ya yi }oto. Ha}i}a, wannan shi ne babban dalilin da ya sa ha]ewar jam’iyyun adawa don su kada shugaban }asa da ke kan gado ya ke da matu}ar wuya a }asar nan, wai gurguwa da auren nesa. Bari mu gani a cikin ’yan kwanakin nan idan a siyasar wannan zamanin za su sauya hali duk da yake Hausawa sun ce hali zanen dutse, ba ya kankaruwa.

—-
An buga a LEADERSHIP HAUSA

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *