Matasa Da Tashin-Tashina

Ba tun yau ba aka san cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin Nijeriya shi ne rashin aikin yi, sannan wannan matsalar ta na ba da gudunmawa ga tashe-tashen hankula na ƙabilanci da na addini a cikin ’yan shekarun nan. A makon jiya, wani muhimmin rahoto da cibiyar yaɗa al’adun ƙasar Birtaniya, wato British Council, ta ɗauki nauyin yin sa ya yi gargaɗin cewa idan har Nijeriya ba ta samar da guraben aikin yi guda miliyan 25 a cikin shekaru 10 masu zuwa ba, to, tashe-tashen hankula da matasan mu ke yi za su ƙaru matuƙa. Idan har mu ka yi kunnen uwar shegu da wannan rahoton, kaicon mu!

Wasu manyan ’yan Nijeriya waɗanda su ka haɗa da tsofaffin ministoci da kuma masanan harkokin tattalin arzikin ƙasa, irin su Ngozi Okonjo-Iweala, Frank Nweke Jr., Lamiɗo Ado Bayero, Donald Duke, Pat Utomi da Maryam Uwais, su ne su ka yi bincike su ka rubuta rahoton mai suna “The Next Generation Nigeria”. Haka kuma wasu masanan daga Amerika da Ingila sun taka rawar gani wajen haɗa rahoton. A ranar Larabar makon jiya aka yi taron ƙaddamar da shi a Abuja. Tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Mista Frank Nweke, Jnr., shi ne ya karanta gundarin abin da rahoton ya ƙunsa a gaban jama’a. Ya ce rahoton ya gano cewa Nijeriya ta na fuskantar “barazanar yawan jama’a” saboda rashin aikin yi tsakanin matasa. Rahoton ya ƙididdige cewa yawan mutanen Nijeriya zai ƙaru daga mutum miliyan 150 da ke akwai yanzu, da ƙarin mutum miliyan 63 ya zuwa shekarar 2050. Hakan zai sa Nijeriya ta kasance ta biyar a cikin ƙasashen da su ka fi yawan jama’a a duniya. Rahoton ya hango cewa kashi 40 cikin ɗari na ’yan Nijeriya matasa ne, wanda hakan zai sa a samu ƙarin ɗimbin masu buƙatar aikin yi a nan gaba.

Wannan rahoto dai ya nuna cewa yawan mutanen Nijeriya ya ninka a cikin shekaru ashirin da su ka gabata, wanda ya saka ƙasar cikin mayuwacin hali idan har ba a dage wajen gyaran komaɗar tattalin arziki ba. Ya ce, “Samun ɗimbin matasa marasa aikin yi ya kan jefa al’umma cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi, ta hanyar yawaitar aikata laifuffuka da kuma samar da yanayin da zai jawo tashin-tashina. Duk ƙasar da ba ta shirya wa yin amfani da albarkar yawaitar matasan ta ba, za ta samu kan ta cikin fitinar yawan jama’a, maimakon ta ci moriyar hakan.”

Idan mun lura, wannan rahoton bai tsaya kai da fata kan cewa bala’i kaɗai ya hango ba, a’a, ya ba mu shawarwari kan hanyoyin da za mu bi don kauce wa bala’i. Ya yi la’akalari da cewa za a iya amfani da matasa don gina ƙasa, tare da nuna cewa matasan mu su ne albarka mafi girma da Nijeriya ta ke da ita, ba man fetur ba. Ya ce: “Matasa su ne albarka mafi girma a ƙasa, ba fetur ba, a cikin ƙarni na 21. Idan ƙasar ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen tattalin arziki kamar yadda ta ke yi a yanzu, ta inganta harkar ilimi, ta samar da ayyukan yi, to, kowane ɗan Nijeriya zai iya samun ninkin arzikin sa har sau uku kafin shekara ta 2030, sannan sama da mutum miliyan 30 za su fice daga ƙangin fatara.”

Rahoton ya ba da shawarar cewa tilas ne ƙasar mu ta fito da tsari mai kyau don samar da aikin yi a shekaru masu zuwa. Ya ce: “Idan Nijeriya ta kasa yin tsari don inganta rayuwar matasa a nan gaba, to za ta fuskaci manyan matsaloli da za su ɓullo a dalilin yawaitar matasa masu jin haushin cewa ba su da aikin yi. Saboda haka za su iya zama wani abu da zai kawo barazana ga zaman lumana a ƙasar.”

A gaskiya, rashin aikin yi a tsakanin matasan ƙasar nan ya zama abin ban-tsoro a yau. Gwamnati ta ce wai kashi 20 cikin ɗari na matasan ne ba su da aikin yi, amma duk mai hankali ya san cewa zai kai kashi har 60 cikin ɗari, musamman da yake yawancin masana’antu sun ruguje, sannan bankuna su na ta korar ma’aikata. Na kan ji zafi matuƙa idan yaran da su ka gama jami’a ko wata babbar kwaleji su ka same ni don in taimaka in sama masu aiki. Babu aikin. A shekarun baya, lokacin duniya ta na kwance lafiya, ma’aikatu neman matasa su ke yi don su ba su aiki. Musamman za ka ga kamfanoni su na zuwa jami’o’i da kwalejoji, su na ɗaukar sunayen ɗaliban da su ka kusa fita daga makaranta domin su ba su aiki da zarar sun ƙare. Hakan ta faru kafin zuwan tsarin tsuke bakin aljihu (SAP), da cin hanci da rashawa, da kuma durƙushewar tattalin arziki na duniya. Duniya juyi-juyi, kwaɗo ya faɗa cikin ruwan zafi.

Babban ofishin Ƙididdiga na Ƙasa (Federal Office of Statistics, FOS) ya bayyana cewa yawancin marasa aikin yi, a biranen mu su ke. Sannan wani rahoto da Bankin Duniya ya wallafa ya ce yawancin matasa marasa aikin yi waɗanda su ka gama makarantar sakandare ne. Ga kuma ɗimbin jama’a a karkara su na zaman warabbuka, ba abin yi sai kame-kame da kunge-kunge.

A gani na, ba sai an bi tsarin ƙayyade iyali ba don kurum a rage yawan ’yan Nijeriya, kamar yadda rahoton British Council ya ce a yi. Dubi ƙasar Chaina mana, wadda ta fi kowace ƙasa yawan jama’a. Chaina, mai mutum biliyan 1.3, har ta zarce Japan wajen ƙarfin tattalin arziki, ta zama ta biyu a duniya (bayan Amerika). Ita ma Indiya, mafi yawan jama’a ta biyu a duniya, haka ne. Me ya sa? Dalili shi ne su na da shugabanni masu son ci-gaban jama’ar su, ba wawura ba ko bin tsarin ƙasashen Turawa.

Ai jama’a albarka ce. Kada mu ji tsoro don jama’ar mu na ƙara yawa. Dalili shi ne mu na da albarkatun ƙasa masu tarin yawa da za a iya amfani da su wajen ciyar da ƙasar mu gaba. Duk inda ka waiga a Nijeriya, ba abin da idon ka zai gane maka sai albarkatu iri-iri. Tun daga sararin samaniya mai cike da hasken rana, har zuwa ƙasar noma mai dausayi wadda ke ƙunshe da ma’adinai, ga dabbobi, suke-shuke, mai, da sauran su, sannan ga jama’a masu ji da lafiyar jiki, masu ilimi da son aiki tuƙuru. To, amma matsalar mu ita ce ba a yin amfani da waɗannan albarkatun ta hanyar da ta dace. Ana banzatar da su ne. Mu na da yawaitar ɓarayi masu sace albarkatun don kurum Allah Ya ɗora su a kai, sannan su na amfani da jama’ar – musamman matasa – wajen ayyukan assha, irin su karuwanci da kuma rikicin addini ko ƙabilanci.

Shugabannin mu sun yi watsi da aikin noma, sun maida hankali ga man fetur, wanda ya sa sun kasa fahimtar alfanun da ke ƙunshe jingim cikin sauran albarkatun da Allah Ya ba ƙasar nan. Ba su ba harkar ilimi muhimmanci, wadda ita ce ƙashin bayan gina ƙasa mai nagarta. Muguwar faɗuwar da ’yan makaranta su ka yi a jarabawar WAEC kwanan nan hujja ce da ke nuna cewa shugabannin mu ba su tunanin abin da ya dace da ci-gaban ƙasa. Hujja ce da ke nuna irin haɗarin da mu ke fuskanta – wato ta al’umma marasa ilimi ko makamar aiki, wadda za ta iya jawo rigingimu a ƙasa a kowane lokaci.

Rahoton na British Council ya kuma gano wani abu da ya kamata shugabannin Arewa su sani: wato duk da yake an san cewa har yanzu jahilci ƙaruwa ya ke yi, tazarar da ke tsakanin sashin Kudu da na Arewa na ƙasar nan ya na ƙara ƙaruwa ne. ’Ya’yan Kudu sun fi samun shiga makaranta fiye da na Arewa.

Barazanar cewa rigima ta na nan tafe sai ƙaruwa ta ke yi a yayin da zaɓen 2011 ya ke ƙaratowa. Rashin aikin yi ya ƙaru saboda durƙushewar da masana’antu su ka yi a sanadiyyar rashin wutar lantarki. Hakan ya sa a yau akwai bataliyoyin matasa marasa aikin yi, su na jiran kawai a ɗauke su aikin tada husuma. Masu ɗaukar su aikin rigimar ba wasu ba ne illa shugabannin mu waɗanda su ka wawuri dukiyar jama’a kuma za su yi amfani da ita don zaɓen ta hanyar ƙarfi.

Abin ban-haushi, maimakon ka ji ana maganar samun ’yan takarar da za su magance manyan matsalolin ƙasar nan irin su rashin aikin yi, an koma kawai ana cacar baki kan tsarin karɓa-karɓa na PDP. Manufar wannan tsari fa kawai wanene zai zama shugaban ƙasa, kuma daga ina ya fito, ba wanene zai yi ƙoƙarin magance ɗimbin matsalolin ƙasar nan ba.

An buga a jaridar LEADERSHIP HAUSA

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *