Maryam Usman Hiyana ta haihu

Mata ku zo ku yi gud’a: “Ayyiririii!!”

Shahararriyar jarumar nan ta finafinan Hausa, Maryam Usman (Hiyana), ta haihu. Wata majiya ta sanar da ni cewa a ranar Lahadi da ta wuce ne Maryam din ta haihu. An samu d’a namiji.

A cewar majiyar, Maryam ta haihu ne a birnin Kano, a wani asibiti mai zaman kan sa.

Idan kun tuna, Maryam ta shiga tsaka-mai-wuya sakamakon bullar majigin batsa da su ka dauka ita da wani saurayin ta mai suna Bobo. Majigin, wanda aka dauka da wayar hannu, ya bulla ne a farkon watan Agusta 2007. Nan da nan ya fantsama a cikin al’umma kamar wutar bazara.

Bullar majigin ya sa jarumar ta shiga buya, ta bar industiri ana ta cece-ku-ce; kai, ba ma industiri ba, har da dukkan kasar Hausa da sauran sassa na duniya.

Bayan watanni uku ana cacar baki, a cikin Nuwamba 2007 sai wani namijin duniya, wanda ya dade ya na soyayya da Maryam, ya aure ta. Wannan ba wani ba ne illa Alhaji Ado Ahmed Dangulla, wani dan kasuwa a Kano. Auren da su ka yi ya burge mutane da dama, musamman masoyan Hiyana. An yi masu fatan alheri.

To amma hayaniyar Hiyana-Bobo din nan ta yi wa sana’ar fim babbar illa. Gwamnatin Jihar Kano ta jefo da wani mutum mai suna Malam Rabo cikin lamarin, a matsayin shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano. Ba tare da bata lokaci ba, malamin ya k’ara ingiza harkar fim cikin mawuyacin hali: ya dakatar da sana’ar fim har wata shida, daga bisani kuma ya kulle manyan ‘yan wasa, da furodusoshi da ‘yan kasuwar finafinai, ban da kamfen din batanci kan ‘yan fim da ya shiga yi a kafafen watsa labarai. A yanzu haka akwai shari’u da ake tafkawa da shi a kotu.

Ko ma dai yaya ta je ta dawo, ita Hiyana ta yi zaman ta lafiya lau da mijin ta. Na ji an ce rayuwar auren su abar burgewa ce. To amma tuni ta yi bankwana da shirin fim. Hasali ma dai, ba ta yarda ta yi mu’amala da ‘yan fim, sai ‘yan kalilan (irin su Maryam Oloni).

A cewar majiya ta, Hiyana da d’an da ta haifa su na nan cikin k’oshin lafiya. Ranar Lahadi za a yi suna. (Wasu sun ce sunan mahaifin ta, wato Usman, za a rad’a wa yaron).

To ko ma dai me aka rada masa, mu tamu ita ce addu’ar Alah Ya raya shi cikin k’oshin lafiya. Kuma Allah Ya ba uwa lafiyar mama, amin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *