Mamman Shata – Ba Rabo Da Gwani Ba…!

A yau ga wata ‘yar waƙa da na yi wa marigayi Alhaji Mamman Shata. Rasuwar Sarkin Daura Bashar kwanan nan ce ta tuno mani da waƙar, wadda an buga ta a littafin tarihin Shata da na jagoranci rubutawa. Bismillah:

GA MU NAN ZUWA!
(Waƙar Ta’aziyyar Mamman Shata)

Ya Rabbi ƙaran da ilmi na shirya
‘Yar wagga waƙa da yau zan karanta.

Na shirya waƙar yabon nawa gwarzo,
Dakta Muhammadu Alhaji Shata.

Kun san shi ko da fa ban bayyana ba:
Sarkin Mawaƙa na dukkan ƙasa ta.

Shi yai wafati gabanin na shiryo
‘Yan wanga baiti da yau zan taƙaita.

Roƙo na ke Jallah buɗan ƙwaƙwalwa,
Da za ni waƙar fasihin mu Shata.

Mannanu, Ƙuddusi, ar-Rahamanu,
Shi bai da farko da ƙarshen sarauta.

Sarkin da ba ɗa garai ko aboki,
Shi ba iyaye garai ko ko mata.

Shi yay yi kowa da komai ku gane,
Shi yah halitto fasihin mu Shata.

Na shaida Manzon Sa Mamman na Dija
Ya zo da saƙo da duk mun karanta.

Ya ce ga Allah mu zam sujjadawa,
Ko waƙ ƙi lallai ku san ya yi wauta.

Shata a farko na wannan bayani,
Musawa kakan sa shi yak kafa ta.

Sannan a nan ne garin haihuwa tai,
Iroro Yaro uba ne ga Shata.

Nan yay yi wargi da kiwo da noma,
Kakan sa Idi, uwa Lariya ta.

Shi ba ya doko a layi ga tsara,
Hatta a jeji ciki yai bajinta.

Shanu, awakai, tumakan sa kwata,
Su yai ta kiwo da sandar sa Shata.

Yai kasuwanci na goro a baka,
Hatta alewa ya na, “Zo ku sha ta!”

Baban sa bai so ya zam rera waƙa,
Shi ya fi son sui ta noma da Shata.

Hangen sa ɗan Fillo irlin sa noma,
Ko yai ta kiwon bissai har farauta.

Amma a ce yai rawar dandali kam,
Kai, ya yi hauka, a nan bai da gata!

Balle a ce ɗan taro har da sisi
An ba shi, kunya a nan ya ko sha ta.

Amma bisani ya ce, “Kai, su Shata,
Iko na Allah a nan an ƙadarta!”

Ya ƙyale Mamman ganin ya yi nisa
Can gun rawar duniya shi ya taka.

Muryar sa zaƙi ta ke yi Mahamman,
Tamkar zuma in ka saurari Shata.

Sam ba fasihi kama tai a waƙa,
In dai kiɗa za a sanya shi kwata.

Na gode Allah Ta’ala da yay yo
Wannan fasihi cikin nan ƙasa ta.

Domin raha ne ya ke shirya baitin
‘Yan dambe hatta giya wai ku sha ta.

Ya nuna illar mashayi ku gane
Don gargaɗi, ya fi ƙaunar ku bar ta.

Ai ya yi waƙar ɓarai don a dara,
Can ya taɓo masu lale ta karta.

Dukkan sarakan ƙasar nan ta Hausa
Yai masu waƙa Muhammadu Shata.

Shi yai yi waƙar fatake da tela,
Bai bar manoma haɗa har masunta.

Mai sanya khaki da mai ɗaura ƙirgi,
Mai kama biro da mai tuƙa mota.

Ya ƙera waƙa ta Malam da gardi,
Hatta kadoji a domin bajinta.

Ɗan kasuwa mai saye don ya saida,
Ko karuwai masu aikin ƙazanta.

Bai ƙyale gurgu, makaho da kurma
In ya yi waƙar su zo don su ji ta.

Hatta su Manzo, Sahabbai, waliyyai,
Ya rera waƙar su mun ji ta Shata.

Ya burge kowa a birni da ƙauye,
Yaro da babba maza har da mata.

Sun ji shi sun so shi sun so ganin shi,
Sun bai Muhammadu dubbai na kyauta.

Sun ba shi kurɗi, gidaje, dawakai,
Gona, tufafi, da mata da mota.

Arna, Musulmi, haɗa majusawan
Kurmi gani nai su ke sun ƙagauta.

Jarman Kano Ɗankabo ya riƙe shi,
Yai mai dubun arzuka duk na gata.

Sarki na Daura Bashar kar ku manta,
Tamkar uba ne a gu nasa Shata.

Ƙauna da yarda tsakanin dukkan su,
Mamman da Mamman a rayin su kwata,

Ai ta yi kauri da ƙarfin daɗewa,
Har ma ya koma ga Allahn sa Shata.

Sarki Bashar ne ya sanya shi hanya,
Mai kyau da daɗi a domin ya bi ta.

Jarma ya ɗauke shi ya sa shi jirgi
Sun je Amurka da London su Shata.

Can ya yi kallon Baturai tsanake,
Ya ƙara wayon zaman ran sa Shata.

Har ya yi waƙa a birni na L.A.,
Hausar sa Modibbo ne ya fasarta.

Sai ga Baturai a tsuke da wando,
Sun sanya naktaye rigar su kwat ta.

Amma kalangan Muhamman amon su
Ya sa su zarya da juyi ga Shata.

Mamman hali nai ya na nan da kyawu,
Don ba ya sharri ga me mai mugunta.

Ya tsaida sunna ta aure haƙiƙan,
Ya haifi ‘ya’ya na sunna da mata.

Mata ta farko da an ba shi aure,
Auren budurwar sa sunan ta Binta.

Bakori nan ne akai wanga aure,
Dangin sa sun je su shaida ga Shata.

Shi gaskiya ce ya ke so Mahamman,
Ƙarya garai ta fi ɗaci na gauta.

Ni na fa zauna da Mamman a zaure,
A Funtuwa ƙwag gida nai da kwalta.

A kan kushin nan sarakin ka harɗe,
Nan ko gaba nai mutane ka kwanta.

Ga shimfiɗu an baje mun ko zauna,
Mun buɗe kunne, idanu ga Shata.

Zance ake yi kawai kan siyasa,
Ko kan mutane da ke rafka wauta.

Ko ko a zanta a kan masu himma,
Ko masu ƙarfin hali ‘yan bajinta.

Shi ma garai mun ji daɗin ruwaya,
Ƙwalwar sa kullum batu ya cika ta.

In an ka zauna da Shata a zauren,
Shi ba ya ɓoyon batu mai bajinta.

In ya yi arba da insu da jinnu,
Take a nan gun ya na ko baje ta.

Zai ma riwayar ka san ba ya tsoro:
Ko da wuta ce katsam zai shige ta.

In tsamiya ce da jinnu a kan ta,
Bai waiwaye take ne zai haye ta.

Ko ko ruwa wanda manya ka shakka,
Mamman ciki za ya afka da mota.

In ya ga ramin kumurci da zurfi,
Hannu ya kan sa ya shaƙo wuyan ta.

Ran nan Aliyu na Ƙanƙara ya ce
Bai yarda Shata mutum an halitta.

“Kai shi fa Mamman a kai nai da motsi,
In an gaya ma ka zan gaskata ta.

“Shi ga shi tsaf ɗan’adam ne a fuska,
To aljani ne a zuci da hanta.

“Ai an yi sa’a da bai ba da tsoro,
Sai dai a so shi Muhammadu Shata.”

An so shi Najeriya zagayen ta,
Hatta ƙasashen da ak kewayen ta.

Don ya yi yawon ƙasashe ku duba,
Har Ghana, Burkina ma ya shige ta.

Har Saliyo, Kamaru da Chadi,
Ya san su sun san shi Alhaji Shata.

Ai ma Nijar san da Mamman ya leƙa,
Babban gida sun ka baishe shi mata.

Lallai Hurera uwa mai biyayya,
‘Yar malamai Inna mata ga Shata.

Tun ran da Allah ya sa ta ƙasan sa,
Ta bi shi rayin sa duk ta wadata.

Uwargida ce gidan nan na Baba,
Su su uku kun ga sun mai wadata.

Domin akwai ‘yar sarauta gidan sa,
Ta-Falgore wadda an ba shi kyauta.

Lallai Khadija fara kin yi kirki,
Allah ya zan sa ki Firdausi kyauta.

Ke ma Ta-Dukke fara kin biyayya
Gun Baba Alhaji Mamuda Shata.

Ba haihuwa gun ki Yaya Amina,
Ke cimma Mamman a Aljanna kyauta.

Ran nan fa tsufa ya karyo wa Mamman
Ga ciwuka rayuwar sun rufe ta.

Don ya yi ciwo na ƙoda da zafi,
Har Jidda an kai shi baban mu Shata.

An samu sauƙi sa’annan fa ciwon
Yay yo kwana ya ko banke shi Shata.

Duk ɗan’adam ajizi ne ku gane,
Shi rayuwar tasa an rurrubuta.

Farkon ka ƙarshen ka komai a tsare,
Ai ba tsimi ko dabarar gudun ta.

Domin hakan kun ga tilas Muhamman
Ya kai gaci babu sauran bajinta.

Birnin Kano inda Mamman ya haska,
Can ne a ƙarshe a dama ya kwanta.

An mai kushewa a Daura a ranar,
Sarki Bashar ne ya sallaci Shata.

Na gode Allah da naz zan sanin shi,
Ya san mu sosai da baban mu, Shata.

Ai sun yi hulɗa uba na da Shata,
Ni ma na zo na ci duk moriyar ta.

Taro mu zauna mu na mai du’a’i,
Mannanu gafarci Alhaji Shata.

Allah jiƙan wanga babban fasihi,
Yafe kure nai da shi ɗin ya lafta.

Sanya shi Lambu na Firdausi, Jallah,
Kafin mu cim mai a can baba Shata.

Mu ma ka yafe mu laifin mu, amin,
Domin amincin Muhamman na Binta.

Zan sanya aya a nan kar na zarce,
Ai alƙawar nay yi kan zan taƙaita.

Baiti ɗari ne cikin wanga waƙe,
Alhamdu lillahi don na gama ta.

Malam ka ƙirga da kyau don ka gane,
In nai kure sai ka yafe ni wauta.

Ya Rabbi roƙo na ke yi da ƙari,
Saka wa Shata da Lambun ka kyauta.

Amin da amin da amin da amin,
Nai fatiha ‘yan’uwa, na dire ta!

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *