A ranar 17 ga Satumba, 2010, Allah ya ɗauki ran Malam Turi Muhammadu, a Kaduna. Shekarun sa 70 a duniya. Kafin rasuwar tasa, ya taɓa riƙe muƙamin editan jaridar New Nigerian, sannan daga bisani ya zama manajan daraktan kamfanin da ke buga jaridar. Malam Turi fitaccen ɗan jarida ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban aikin jarida a ƙasar nan. Sai dai kash! yawancin mutane, ciki kuwa har da waɗanda su ka san shi, farin sani, ba su kula sosai da nasarorin da malamin ya samu a wannan fagen ba har sai da ya koma ga Mahaliccin sa. Da ma akwai irin waɗannan mutanen jingim a garuruwan mu – waɗanda su ka yi abin a zo a gani amma ba a damu ba har sai wani abu ya faru gare su, musamman ma mutuwa.
Kamar yadda mu ka gani a makon jiya, ’yan jarida da dama a Nijeriya sun ci moriyar tarayyar su da Malam Turi. Da yawa, ya kasance uba a gare su a lokacin da ya ke aikin jarida da kuma bayan ya bar aikin. Daga rubuce-rubucen ta’aziyya da ’yan jarida irin su Sam Nda-Isaiah da Mohammed Haruna da Clem Baiye da Adamu Adamu da wasu su ka yi a jaridu, za mu iya fahimtar cewa Malam Turi babban masani ne a wannan fage, wanda ya yi amfani da ƙwarewar sa don ciyar da aikin jarida gaba, sannan mutum ne mai son ganin cewa an ci gaba da yaɗa ƙudirorin dalilan kafa jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo, ba kawai ga kamfanin ba a yau, a’a har ma ga maza da matan da su ka taɓa yin aiki a kamfanin amma yanzu su na rubutu ko gudanar da wasu kafafen yaɗa labaran na Arewa. Don haka ne ma ya ke sa ido kan mutanen da ke aiki a wasu jaridu ko ko gudanar da jaridun da ke da alaƙa ta asali da kamfanin New Nigerian, wato jaridu irin su Daily Trust, Leadership da Peoples Daily. Na tabbatar da cewa ’yan jarida da dama da ke aiki a waɗannan jaridun – da kuma waɗanda har yanzu su ke a New Nigerian a yau – za su shaida cewa Malam Turi ya na daga cikin dattawa ƙalilan da su ka damu da yin mu’amala da su, su na tuntuɓar su, ba don komai ba sai don ganin cewa sun ci gaba da yin aiki a bisa turbar kyakkyawar tarbiyya da bin ƙa’idojin aikin jarida. Wasu daga cikin su, ya ɗauke su kamar ’ya’yan sa a aikin, yayin da wasu kuma ya ɗauke su jikokin sa.
Ni ɗin nan ina daga cikin irin waɗannan mutanen. Na fara haɗuwa da Malam Turi shekaru 13 daidai da su ka wuce, lokacin da ya aiko mani da wata wasiƙa da ya rubuta da hannun sa ya ce ya na so ya gan ni. Na yi mamaki ƙwarai, tare da jin daɗi, a ce babban mutum kamar sa ne ya ke so ya gan ni. A takardar, ya ce ya samu labarin cewa ina ƙoƙarin rubuta tarihin sarkin mawaƙan Hausa, Alhaji Mamman Shata, kuma ya na so mu sadu don ya faɗa mani wasu abubuwa waɗanda ƙila su taimaka mani a aikin. A lokacin, ban taɓa ganin Malam Turi ba, illa iyaka dai na kan ji labarin sa a matsayin fitaccen ɗan jarida da ake girmamawa. To amma dai na san cewa ’yan jarida su kan yi sha’awar abubuwa da dama a rayuwa, wato ban da aikin su, ciki kuwa har da son kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe. Da ma tun kafin lokacin, wani tsohon manajan daraktan kamfanin buga jaridun New Nigerian ɗin, wato Alhaji Tukur Othman, ya taɓa kira na ya yi doguwar hira da ni kan dangantakar Shata da wasu manyan ’yan bokon Arewa da ke zaune a Kaduna a lokacin da Shatan ya ke kan ƙololuwar tashe, irin su Alhaji Sani Zangon Daura.
Na samu Malam Turi a gidan sa da ke unguwar Malali, Kaduna, a ran 22 ga Yuli, 1997, kamar yadda mu ka aje. Ba zan taɓa mantawa da wannan haɗuwar ba. Na farko, na yi sha’awar rashin girman kan sa da ƙoƙarin sa na faranta mani rai. Malamin ya ce lallai in tashi daga ƙasa inda na zauna na harɗe don girmamawa, in koma kan kujera kusa da shi. Sa’annan ya sa aka kawo mana abinci. Da ƙyar na samu na ɗan ci abincin domin gwarzantakar sa a fagen da na ke fafutikar yin nawa sunan duk ta miskile ni.
A tattaunawar mu, Malam ya nuna mani cewa ya na biye da abubuwan da na ke yi a fagen aikin jarida. Ya san cewa na taɓa riƙe muƙamin mujallar Rana da mujallar Hotline shekaru biyar da su ka gabata, bayan na yi wasu shekarun a kamfanin jaridar The Reporter, na kuma samo digiri na biyu a aikin jarida a ƙasar Birtaniya, sannan yanzu kuma ina aiki a New Nigerian a matsayin ɗaya daga cikin ƙusoshin gidan. Ita ma tattaunawar da mu ka yi a kan Mamman Shata, ta karantar da ni abubuwa da dama. Ni a da na ɗauka na san duk wani abu game da Shata ta yadda ba wani sabon abu da wani zai iya faɗa mani kuma, ballantana kuma wani Banufe. To amma Malam ne ya faɗa mani wani abu da ban sani ba: wato yawan waƙoƙin zambo da Shata ya yi bai kai ko cikin cokalin waɗanda ya yi na yabo ba, wanda hakan ya taimaka masa wajen samun ƙarin farin jini da kuma ɗaukaka. Da na dubi wannan magana da kyau, sai na ga gaskiya haka ɗin ne. Waɗannan bayanai da Malam Turi ya yi mani su na cikin littafin da mu ka yi mai taken ‘Shata Ikon Allah!’ mai shafi 604, wanda aka wallafa a cikin 2006, kuma mun nuna cewa shi ne ya faɗa.
Mu’amalar mu da Malam ta ci gaba ne kwan-gaba-kwan baya; sai a jima ba mu haɗu ba, wanda laifi na ne. Ya kan so mu haɗu a kai a kai, to amma sai in kasa kamar yadda na ke so. Na kan laɓe da cewa saboda ina da gida biyu ne, ɗaya a Kaduna ɗaya a Kano. Amma yanzu idan na tuna baya sai in ga cewa wannan ba ƙwaƙƙwarar hujja ba ce, kuma na yi nadamar rashin kusantar Malam kamar yadda ya ke so. Na yi nadamar rashin yin kiwo sosai a cikin faffaɗar gonar ilimin sa don in ƙaru da basirar sa, wanda a shirye ya ke ya ƙosar da ni daga gare ta. Na kan ɗan yi ƙoƙarin ganin sa jefi-jefi. Kuma a ko yaushe ya kan karɓe ni hannu biyu-biyu, tare da tambaya ta, “Shin wane ya faɗa maka cewa ya gaida mani da kai lokacin da ya zo nan gidan?”
Ba shakka, idan abokai na sun je gidan sa su kan ce mani, “Na je gidan Malam Turi kwanan nan, ya ce in gaida kai.” Da zarar na ji haka, sai in ji kunya ta rufe ni. Nan da nan na kan yi alƙawarin cewa lallai zan ziyarce shi don mu ci gaba da wata tattaunawa wadda wataƙila mu ka fara a zuwan da na yi gidan sa can a baya.
A ko yaushe Malam ya na so in ci gaba da zama ɗan jarida, ya kan ce Arewa ta na buƙatar mutane iri na a aikin. Amma bayan na yi aikin shekara huɗu a New Nigerian, inda na riƙe muƙamai daban-daban kamar su editan maƙaloli, editan labaran ƙasashen waje, editan adabi, sakataren kwamitin editoci, har zuwa mataimakin edita, sai na aje aikin. Dalili shi ne an yi wata shida ba a biya albashi ba, wanda ya sa na fara tunanin irin makoma ta idan na zauna a aikin da ba zai iya ba ni damar ci da iyali na ba. A ƙarshe dai, na dawo aikin jaridar, kuma na ji daɗin hakan.
Malam Turi mutumin } ƙwarai ne wanda ke son ganin ci-gaban Arewa. Abin baƙin ciki shi ne bai yi tasiri a siyasa da ya shiga ba, bai samu cin zaɓen zama sanata ba bayan ya bar aiki a New Nigerian a cikin 1980. Ya yi la’akari da cewa siyasa mugun wargi ce, wadda bai kamaci mutane irin sa ba. Na san dai cewa ɗaya daga cikin abubuwan da bai ji daɗin su ba shi ne koma-bayan da jaridar New Nigerian ta samu a matsayin babbar jarida daga Arewa. A rubutun ta’aziyya da Malam Mohammed Haruna ya yi a Daily Trust ta ran Larabar makon jiya, ya yi nuni da cewa rugujewar ƙimar jaridar da koma-bayan ta ya fara ne daga lokacin da Malam Turi ya bar aiki a kamfanin, domin shugabannin kamfanin da su ka zo bayan sa sun sauya turbar da waɗanda su ka kafa kamfanin su ka ɗora kamfanin a kai. Ni ma na yarda haka ne. Manufar littafin da Malam Turi ya rubuta na tarihin jaridar, mai suna ‘Courage and Conviction’, ita ce a isar da wannan saƙon ta hanyar bayar da cikakken tarihin jaridar a cikin shekarun ta ashirin na farko inda ta cimma gagarumar nasara. Ka dubi dai jaridar da ke buga kwafe 250,000 a kullum lokacin da ta ke tashe, sai da ta koma ta na buga kwafe 2,000 a wani lokaci. Duk da yake an sha yin hoɓɓasan dawo da martabar jaridar a baya, abin ya ƙazanta a cikin shekaru kamar goma da su ka gabata. A gaskiya, babbar karramawar da za a yi wa Malam Turi (Allah Ya jiƙan sa) har ma da mutane irin sa da su ka yi aiki tuƙuru don gina New Nigerian, ita ce a yi dukkan abin da ya dace a yi don dawo da ƙarfin jaridar kamar yadda ya ke a da.
—–
An buga wannan maƙalar a LEADERSHIP HAUSA ta ran 1 ga Oktoba, 2010