Gidan yanar Ali Nuhu

Fitaccen jarumin finafinan Hausa, wato Ali Nuhu, ya fito da sabon gidan yana nasa na kan sa. Jiya ya aiko mani da rariyar, kamar haka:

www.alinuhu.tv

Gidan yanar ya na ba da bayani kan daya daga cikin ‘yan fim din Hausa da su ka fi sauran yin fice: tarihin sa, rawar da ya taka a fagen fim, jerin wasu finafinan sa, lambobin girma da ya samu sakamakon yin zarra da ya yi a finafinai, da kuma hotunan sa da na iyalin sa.

Sai dai kuma har yanzu ana cikin gina gidan ne, ba a kammala ba, domin wasu shafukan ba su dauke da bayanai. Haka kuma na lura akwai matsalolin haruffa (proofreading) a wau shafukan.

Jarumai a fagagen adabi daban-daban kan mallaki gidan yana domin masu kaunar su su shiga su gani. Sau da yawa ma, ba su jaruman ba ne ke kirkirar gidan yanar, a’a masoyan su ne. Idan su da kan su ne su ka kirkiri gidan yanar, ko su ke ba da umarnin abin da za a saka a ciki, to ya zama “official website” kenan – kamar dai irin na Ali Nuhu.

Mallakar gidan yana ya na daga cikin ci-gaban da harkar fim din Hausa ta samu duk da yake an samu koma-baya wajen shirya finafinai. Ali Nuhu shi ne dan wasa na farko da ya fito da gidan yana kacokam don tallata kan sa a dandalin duniya na intanet. Na tuna, kamar shekaru hudu da su ka gabata, na taba ba shi shawarar ya mallaki gidan yana, amma bai kula da shawarar ba, sai yanzu.

Zai kyautu sauran fitattun jarumai a fagagen adabi na Hausa (wato fim, rubutun littafi, wakoki, ds) su yi kokarin mallakar gidan yana. Sai dai, akasin na Ali, ya kamata su mallaki gidan yanar da harshen Hausa domin hakan zai kara tallata harshen Hausa a duniya.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *