Masu Kunnen Ƙashi!
A makon jiya, gidan talabijin na CNN ya tambayi ɗaya daga cikin ’ya’yan Shugaba Muammar Gaddafi na ƙasar Libya, wato Saiful-Islam Gaddafi, abin da mahaifin sa da ’yan gidan su za su yi tunda ga shi ’yan ƙasar su na zanga-zangar ƙin amincewa da mulkin su. Shin za su tsere ne kamar yadda shugaban Tunisiya …