Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki – Ƙamaruddeen Imam

Ƙamaruddeen Imam ya na daga cikin ’ya’yan kakan marubutan Hausa, wato marigayi Alhaji Dakta Abubakar Imam, marubucin littattafai kamar su ‘Ruwan Bagaja, ‘Magana Jari Ce,’ ‘Tafiya Mabuɗin Ilmi,’ Tarihin Annabi Da Na Halifofi’, ‘Tambaya Goma Amsa Goma’, da sauran su. Shi ma Alhaji Ƙamaruddeen marubuci ne, kuma mawallafi, kuma shi kaɗai ne daga cikin ’ya’yan Imam da ya gaji mahaifin sa a fannin adabi.

Kamar Baba Imam, shi ma Alhaji Ƙamaruddeen ya kwanta dama. Ya rasu a ranar Juma’a, 12 ga Mayu 2006 a gidan Imam da ke Tudun Wada, Zariya, a Jihar Kaduna, bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon shekara biyar. Shekarun sa 56 a duniya.

Ya rasu ya bar mahaifiyar sa da matar sa da ’ya’ya shida da kuma jikanyar sa. Allah ya jiƙan sa, amin summa amin.

Abin ikon Allah, na samu damar yin hira da Ƙamaruddeen a Zariya tun ya na da rai, wato a ranar 29 ga Agusta 2004. Mun tattauna a kaset lokacin da na halarci wani taro da iyalan Imam su ka kira don ƙaddamar da kwamitin Gidauniyar Tunawa da Alhaji Abubakar Imam (Abubakar Imam Foundation) tare da gina gidan yana a intanet. Ni memba ne a kwamitin. Mun yi tarurruka da dama don ɗabbaka wannan muhimmin nufi, wanda a ƙarshe an kafa cibiyar tattara bayanai kan Imam a wani gini da ke duban Ƙofar Babban Dodo a birnin Zariya, sa’annan an gina gidan yanar (www.abubakarimam.com).

Malam Ƙamaruddeen mutumin kirki ne, mai sauƙin kai, mai sanyin murya, mai fara’a – kamar dai dukkan ’ya’yan Imam da na gani. Lokacin da na buƙace shi da mu tattauna, nan da nan ya amince, mu ka zauna mu ka tattauna kan sha’awar sa ta rubuce-rubuce, da matsalolin sha’anin wallafa a Nijeriya da kuma halin da ake ciki.

Na so in wallafa hirar a jaridar Leadership lokacin ina editan ta, amma sai abubuwa su ka rincaɓe; haka lokacin da na ke babban editan jaridar Public Agenda, na so buga hirar, amma nan ma abubuwa su ka giggitta. Sai a yanzu ne Allah ya ba ni damar wallafa wannan tattaunawar da marubucin.

Wannan hira ta na da muhimmanci, domin kuwa ita ce ta farko da Malam Ƙamaruddeen ya yi da wani ɗan jarida a kan rubuce-rubucen sa, kuma ita ce ta ƙarshe. Allahu Akbar!

Bismillan ku:

SHEME: Zan so ka faɗi sunan ka da kuma dangantakar da ke tsakanin ka da marigayi Alhaji Abubakar Imam.

ƘAMARUDDEEN: To ni suna na Ƙamaruddeen Abubakar Imam, kuma ni ɗan Alhaji Abubakar Imam ne.

SHEME: Yanzu aikin me ka ke yi?

ƘAMARUDDEEN: Yanzu ni marubuci ne kuma ina buga littattafai, kuma ana ba ni gyaran rubutu kamar na ‘manuscript’.

SHEME: To ko za ka gaya mana yawan littattafan da ka rubuta da kuma sunan su?

ƘAMARUDDEEN: Na rubuta littattafai da dama. Akwai ‘Tsaka Mai Wuya’, ‘Hannun Ka Mai Sanda’, sannan kuma na rubuta ‘Halaye Nagari a Cikin Musulunci’, ‘Sir Usman Nagogo’ – amma da Turanci ne ni da (Ɗahiru) Coommassie mu ka rubuta shi – da kuma ‘To Use Knowledge’.

SHEME: Kamar daga wane lokaci ne ka fara rubuce-rubucen nan?

ƘAMARUDDEEN: Na fara wannan rubuce-rubuce tun lokacin da marigayi Baba Imam ya ke da rai, har ma ya sa ni a kan wasu hanyoyi inda ya ke ce mani, ‘In za ka rubuta tarihin mutum, to rubuta abin kirkin da ya yi na alheri ga jama’a, maimakon ka yi yabon shi.”

SHEME: Yanzu kenan kai kaɗai ne cikin ’ya’yan marigayi ka gaji baban ka ta wajen rubuce-rubuce?

KAMARUDDEEN: I to, haka ne, don har yanzu ni kaɗai ke yin irin waɗannan ayyuka na rubuce-rubuce.

SHEME: A da, ka ɗan rubuta littattafai na ƙirƙira, amma kuma daga baya sai ka bari. Ko me ya kawo haka?

ƘAMARUDDEEN: To dalilin dai shi ne saboda rashin kuɗi, kuma in ka rubuta ka kai ma wasu su taimake ka sai su ce ba su da kuɗi, ko kuma su ce kai ka kawo rabi, in ka kawo ma in ba a yi sa’a ba sai ka ga kuɗin ka ma ya maƙale.

SHEME: To ban da matsalar rashin kuɗi, ko za ka iya faɗin wata matsala da ke iya shafar aikin wallafa, musamman a nan Arewa?

ƘAMARUDDEEN: Akwai matsaloli mana. Misali irin yadda mutane ke rubuta littattafai barkatai ba tare da an tsara shi yadda ya kamata ba, musamman masu soyayya. Ba wanda bai iya soyayya ba, to amma ya kamata in za ka rubuta ka tabbatar da ka rubuta abin da yake mai kyau kuma mai inganci.

SHEME: Menene maganin abin?

ƘAMARUDDEEN: Maganin abin shi ne gwamnati ta shigo ciki, ta zo ta riƙa sayen littattafan. Ya kamata kuma a riƙa sayar ma makarantun sakandare. Ta haka za a samu tarbiyya a makarantu, ba wai mutum ya je ya kalli fim ya zo ya maida shi littafi ba, ko kuma irin yadda ake cusa ma matasa ra’ayin soyayya ba; misali, duk wanda ya karanta ‘Magana Jari Ce’ ya san lallai wannan Bahaushe ne ke magana, kuma ba batsa, sannan ga tarbiyya a ciki.

SHEME: To Alhaji, ga shi Allah ya haɗa mu a nan Zariya don tunawa da shi marigayi da ƙaddamar da kwamitin tunawa da shi. Ko za ka gaya mana abin da ya sa ku ke son a kafa wannan kwamiti?

ƘAMARUDDEEN: To, akwai wani ɗan jarida wanda ake kira Ibrahim Sheme, ya na yawan rubutu a kan Dakta Abubakar Imam. A gaskiya ya nuna mana ƙauna, ya nuna ya na son marigayi Dakta Abubakar Imam. To kwanan nan sai ya yi wani rubutu wanda ya zama mana kamar tuni ko ƙalubale, don kuwa har wani shaguɓe ya yi mana inda ya nuna mana cewa ’ya’yan marigayin kamar ma sun manta da shi. To jin haka sai mu ma mu ka harzuƙa mu ka fara shirin kafa wannan kwamiti don tunawa da marigayi Dakta Alhaji Abubakar Imam.

SHEME (dariya): Ya ka ke ganin wannan abin zai amfani mutane a nan gaba?

KAMARUDDEEN: In aka kafa wannan Foundation, to kowa da kowa zai zo ya zauna ya duba duk abin da ya ke buƙata na Dakta Alhaji Abubakar Imam, kuma wannan ya haɗa kowa da kowa. Misali, akwai wata mata, mutuniyar Jamus ce, ta ke bincike a kan Dakta Abubakar Imam, yanzu haka har ma ta yi nisa ta kai wata matsaya babba. Ka ga yanzu in ta zo sai kawai mu nuna mata wannan wurin don kuwa da man an taɓa yi mata bayanin ana wannan aiki.

SHEME: To a ƙarshe, ko za ka iya ba ni ɗan tarihin rayuwar ka?

ƘAMARUDDEEN: To ni shekaru na 54 da haihuwa, kuma a nan Zariya aka haife ni. Bayan na gama karance-karance na na sakandire da jami’a, na yi aiki da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, lokacin Edita Baban Zarah.

SHEME: Ai ina zaton kai a Katsina ka ke.

ƘAMARUDDEEN: Asali na shi ne Katsina, kuma mu na da yawa, misali su Shamsuddeeni Imam, Nuruddeen Imam, su su ke can Katsina; amma mu da aka haifa a nan Zariya – Najmuddeen Imam, Ƙamaruddeen Imam, Amadi Imam, Jalaladdeen Imam – nan Zariya mu ke.

SHEME: To Alhaji, na gode.

ƘAMARUDDEEN: Ni ma na gode. Allah ya saka maka da alheri, amin.

(BAYANI: Hoton ƘAMARUDDEEN da ke wannan shafin ya daɗe da ɗauka, wataƙila sama da shekara 20 kafin rasuwar marigayin, domin ya zama dattijo lokacin rasuwar sa. Allah ya rahamshe shi, amin.)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *