A DAIDAITA SAHU

HUKUMAR A DAIDAITA SAHU TA JIHAR KANO
Lamba 2, Sabo Bakinzuwo Road, P.M.B. 3313 Kano, Nijeriya. Web: www.adaidaitasahu.org

2 ga Sha’aban 1428
16 ga Agusta 2007
Zuwa ga Shugabannin Masu Shirin Fim Jihar Kano
Assalamu Alaikum.

BUD’AD’D’IYAR WASIKA ZUWA GA KUNGIYAR MASU SHIRYA FINAFINAI TA JIHAR KANO

Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano ta na shawartar ku da ku dakatar da harkar finafinan Hausa kwata-kwata na ak’alla tsawon shekara guda, don a sami damar gudanar da ingantaccen gyara a harkar.

D’aukar matakin dakatar da harkar fim ita ce kad’ai mafita gare ku a wannan lokaci.

Mu na tunatar da ku cewa a can baya da aka sami wata matsala a harkar finafinai a Jihar Ikko, takwarar k’ungiyar ku ta Ikkon da kan ta ta dakatar da shirya finafinai har tsawon watanni shida kafin a samar da gyara a harkar.

Hukumar A Daidaita Sahu ta na k’ara shawartar ku da cewa jingine wannan harka ta fim baki d’aya shi ne kad’ai zai sa al’ummar Jihar Kano su gamsu, idan aka yi la’akari da fushin da jama’a ke ciki. Dakatar da ’yan wasa da yin sauran kwaskwarima da ku ka yi, ba za su wadatar ba.

Bayan haka, Hukumar A Daidaita Sahu ta na yin kira ga d’aukacin al’ummar Jihar Kano da a kai zuciya nesa, a k’ara hak’uri, a kuma k’ara addu’ar Allah Ya shirya.

Daga k’arshe, wannan hukuma ta na k’ara jan hankalin ku ’ya’yan {ungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano da ku lura da cewa wannan fa hannun-ka-mai-sanda ne. In kunne ya ji, jiki ya tsira.

Sa hannun:
Bala A. Muhammad
Darakta Janar
Hukumar A Daidaita Sahu

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *