• About
  • Contact
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

Rubutawa daga faifai: Ibrahim Sheme

by IBRAHIM SHEME
January 01, 2013
0
Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi
Littafin tarihin Kassu Zurmi
0
SHARES
18
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ya san hanyah hwaɗa,

A’a Musa na ƙasaɗ Ɗa’ali mai tauri!

Kai mutane, tauri ya koma ga gadadde.

Manyan hwaɗa Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali, wan ƙarhi!
Aha!

Na so zuwa gidan Mani Akaye ina woba, ba ‘yan yara wari na.
Sai yac ce ɗiya nai ba su son tauri.
Tsohon kau ya yi yayi nai,
Nic ce sai nai kiɗi in dai hanyai kiɗi ta taho.

Jama’a, na so zuwa gidan Mani Akaye ina sauna,
Ba hanyak kiɗin tauri.

Ɗan yaro ne Musa,
Ashe ya ci magani bai samu wurin gwadi nai ba.

Ran nan sai yaɗ ɗauki kwashe nai,
Yat tasam ma gona tai,
Ya’ iske Sulluɓawa yab bi yana bugun shanu,
Yab bi yana kashe shanu,
Yab bi yana kashe shanu.

Ashe Musa ya ci magani bai samu wurin gwadi nai ba!
Suna ta bugu suna sara,
Duk dai ba a huda kai nai ba.

Ku am manyan hwaɗa, Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali, mai tauri!

‘Yan kai kurwar hwaɗa, mata, kuma sun sheƙa suna kuka:
“Ku yo gudammawa Hillani sun kashe Musa!
“Ku yo gudammawa Hillani sun sabatta shi!”

Har Ɗan’ali zai yo hawa,
Yac ce, “Ko ba ka ji, Mani, Hillani sun kashe ma ɗa?”

Tsoho bai ɓata rai nai ba.
Bai ko kau da kai nai ba, sai yai ta jiƙon ƙarera nai,
Ya san ya shiryi yara nai.

Yac ce, “Ko ba ka ji, tsoho, Hillani sun sabatta ka,
Sun kashe ma ɗa.”

Yac ce, “Ɗan’ali koma gida, ja dan nan ba ni son ƙarya!
Ba da bugu ba, ba sara, ba kau yaƙin takobi ba,
Don su, Musa na tahowa gida!”

Manyan hwaɗa Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali wan ƙarfi!

* Hoto daga: Chapter One Bookshop, Kano

Loading

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading...
Tags: Ɗan'alikalanguKassu Zurmikiɗin gargajiyatauri
Previous Post

Aron Fitila Ga Marubuta

Next Post

Alamomi 40 na da’irar Adabin Kasuwar Kano

Next Post
Alamomi 40 na da’irar Adabin Kasuwar Kano

Alamomi 40 na da'irar Adabin Kasuwar Kano

Buƙatar Samun Cibiyar Waƙoƙi ta Mamman Shata

Buƙatar Samun Cibiyar Waƙoƙi ta Mamman Shata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Tsokaci Kan Waƙar ‘Sarkin Bori Sule’ Ta Alhaji Mamman Shata Katsina
  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran at 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d