IBRAHIM Malumfashi ne ya ƙirƙiro kalmar “Adabin Kasuwar Kano”, wanda da yawan marubuta da manazarta (ciki har da ni) su ka ɗauka ƙasƙantarwa ce. Mun shafe shekaru mu na yaƙi da Malumfashi kan wannan kalmar, kafin kowannen mu ya aje makamin sa (wato biro) a gefe ɗaya, domin duk abin da za a ce, an ce, kuma duk abin da za a yi, an yi.
Na jima ina tunanin menene alamomin littafin irin wannan adabin? To, bayan na gama tunani na, sai na lissafa su. Wani abu da na gano shi ne, yawancin alamomin Adabin Kasuwar Kano akwai su a finafinan Hausa, to amma ‘yan fim sun fi marubuta ɗaukar aikin su a matsayin sana’a, kuma sun fi cin moriyar gumin su.
Ga yawancin alamomin (amma akwai wasu daban):
1. Littafin na Hausa ne ko Turanci. Kuskure ne a ɗauka cewa sai littafin Hausa ne kan faɗa a farfajiyar wannan kalma. To amma na Hausan sun fi yawa.
2. Marubuci kan ɗauki nauyin buga littafin shi, ba kamfani ba.
3. Babu lambar ISBN a yawancin littattafan.
4. Babu kyakkyawan nahawu. Saboda haka za a ga ɗimbin kurakurai a littafin, daga raba kalma ko haɗe kalma har zuwa bin ƙa’idojin rubutu kamar su saka aya, waƙafi, alamar motsin rai, ayar tambaya, alamomin fara magana da rufe ta, ds. Kai, hatta sunayen mutane da na garuruwa akwai waɗanda ba daidai ba a littafin.
5. Marubuci bai bayar da littafi wani ya gyara masa kafin a buga. Gyara ya haɗa da nahawu da kuma sukar labarin. Wani marubucin ya na tsoron kada ya ba ɗan’uwan sa marubuci a sace masa labari! Da ya gama sai ya kai wurin ɗab’i.
6. Rarraba littafi zuwa na 2, 3, 4 ko ma fiye. Ana yin haka domin riba, kuma domin masu karatu kan dinga tambayar ina na 2 ko ina na 3. Abin mamaki, masu karatu ba su cewa ina na biyun ‘Ganɗoki,’ ‘Karshen Alewa Ƙasa’, ‘Mace Mutum’ ko ”Yartsana.’ Dalili shi ne sun san labarin ya ƙare, ko kuma su na ganin waɗannan marubutan ba masu karkasa labari ba ne.
7. Saka lambar wayar marubuci ko adireshin i-mel, wasu ma har da BB Pin, a cikin littafi, saboda masu karatu su bugo waya su faɗi ra’ayin su kan littafin, kuma su kambama marubuci. Ta wannan hanyar, wasu matan aure marubuta sun sha samun ƙalubale daga mazajen su.
8. Ƙulla hulɗa tsakanin marubuci da mai karatu har ta kai ga ana ziyartar juna, ko ka ga yarinya ta sauka a gidan marubuciya wai ta na neman shawara kan wani abu (misali aure). Wani matashin marubucin ma kan samu ƙulla soyayya da ‘yan mata ta wannan hanyar.
9. Duk tunanin marubuci game da kasuwancin littafi bai wuce garin Kano. A nan manyan dillalan littafi su ke. Marubuci bai tunanin ya kai littafin sa Kaduna ko Abuja ko Sakkwato; ya dogara kan dillali ya yi masa wannan, ko kuma dillalan da ke can su zo Kano su saya su tafi.
10. Yawaitar ƙungiyoyin marubuta, kuma da yawa ba su jituwa da juna.
11. Rashin ingancin littafi wajen tsara shafukan sa, da takarda, da ɗab’i (a Turance, “final finishing”).
12. Doguwar sadaukarwa a littafi, tare da godiya ga ‘yan’uwa da masoya da makaranta da ‘ya’ya.
13. Rige-rigen fito da littafi a tsakanin marubuta, wanda gasa ko gaba ke haifarwa. A mako ɗaya sai littafi biyar su fito.
14. Maimaita labarin wani littafin ta hanyar sauya masa siga.
15. Rashin shirya babbar gasa ta rubutu, ko bajekolin littattafai.
16. Kwaikwayon yadda wani ya yi nasa labarin ta fuskar tsarin da ya bi, maimakon kai ma ka fito da naka.
17. Samun marubuta ‘yan kasuwa, waɗanda ke da “kamfanonin” buga wa sauran marubuta littafi, wata sa’a har da tallata musu littafin. Wata sa’a kashe- mu-raba su ke yi wajen buga littafin.
18. Juya labarin fim ɗin Indiya ko na Turawa ko na Canis ko na Larabawa zuwa littafi.
19. Rige-rigen rubuta labari a Facebook (musamman a Duniyar Marubuta ko Dandalin Marubuta). Tsarin wannan shi ne sai a fara labari ko da sheɗara ɗaya ce, sai kuma a bari sai ‘yan guruf sun faɗi ra’ayin su sannan a ci gaba. Sau da yawa ma babu labarin a aje, a lokacin ne ake rubuta shi.
20. Rashin ƙoƙarin a fassara littafi zuwa wasu harsunan na duniya wanda ba su jin Hausa, kamar yadda aka yi wa ‘Alhaki Kwikuyo’ na Balaraba Ramat Yakubu kwanan baya.
21. Rashin damuwar gwamnati ga harkar rubutun littafi. Gwamnati ta fi damuwa da ‘yan fim, shi ya sa ta kafa masu hukuma, kuma ta na shirya masu bitoci da bukukuwan baje-kolin finafinai. Bugu da ƙari, ofisoshin jakadun ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kan su (NGOs) kan kira ‘yan fim su ba su tallafi, ciki har da kai su ƙasashen su domin su ƙara wayewa kan harkar. A lura, marubutan Ingilishi ma kan samu wannan tagomashin.
22. Rashin zurfin hikima wajen ba da labari, wajen wasa da harshe ko sarƙaƙiyar labari.
23. Shaida wa mai karatu a cikin littafi cewa ana nan ana aiki kan wani littafin wanda zai fito nan gaba, ko kuma ba da haƙuri kan wani littafi ko rashin amsa waya, ds.
24. Yawanci jigon littafi bai wuce soyayyar matasa ko matsalar aure ko kasuwanci.
25. Saka Ingilishi a cikin labari ba don ya zama tilas ba sai don a burge mai karatu.
26. Yawanci mata ne ke yin rubutun. Kai, har ta kai maza kan yi rubutu da sunan mace don kiran kasuwa.
27. Saka hoton kyakkyawar fuskar mace a bangon littafi. Yanzu har matan Indiya da Larabawa da Turawa ake ɗaukowa daga intanet a saka; wasu har hijabi ake yi masu da Photoshop. Wannan kan nuna kamar Bahaushe bai da mummunar mace ko tsaka-tsaki. Wani lokaci kuma hoton katafaren gida ake sakawa.
28. Ba a cika ba da labarin talakawa ba, sai ‘yan boko da manyan ‘yan kasuwa. Ko da labarin talaka aka faro, to sai ya rikiɗe ya zama na masu kuɗi, masu fita zuwa ƙasar waje.
29. Idan za a nuna an fita waje a labari, to tafiyar ba ta wuce Ingila, Amerika, Saudiyya, Dubai ko Indiya.
30. Sayar da littafi ɗungurungum ga ɗan kasuwa, shi ya buga ya samu kuɗi. Yawanci babu rubutacciyar yarjejeniya ta wannan cinikin.
31. Amsar kwangilar rubuta littafi daga wurin ɗan kasuwa. “Nawa zan ba ki, ki rubuta mani littafi mai shafi saba’in?” Idan ta rubuta ta ba shi, sai ya saka sunan da ya ga dama.
32. Gamewar marubuta biyu ko uku su yi littafi guda ɗaya.
33. Rashin daɗewar littafi a kasuwa. Idan littafi ya ci kasuwa wata shida, shi kenan ba ka ƙara jin ɗuriyar sa. A lura, har yanzu ana buga ‘Ganɗoki,’ wanda ya fara fitowa a 1934.
34. Da wuya ka ga an yi sharhi kan littafin a wata jarida ko mujalla, duk da yake akwai jaridun Hausa da yawa.
35. Kafafen yaɗa labarai sun fi damuwa da rayuwar ‘yan fim. Misali, idan Fauziyya D. Sulaiman ta haihu, ba labari ba ne, to amma idan Ruƙayya Dawayya ta haihu, labari ne. Amma a marubutan Turanci na Nijeriya, idan Chimamanda Ngozi Adichie ta yi aure ko ta haihu, babban labari ne!
36. Da wuya ka ga an yi nazarin littafin a matakin digiri ko difiloma, ko a yi ƙasida a kan sa a cikin wata mujalla ta masu bincike, ko a gabatar da lacca a kan sa a wani taro a jami’a ko babbar makaranta.
37. Da wuya ka ga an yi littafin nazari kan marubucin wannan adabin.
38. Saurin shuɗewar zamanin marubuci, har ka ji an daina maganar sa, sai ta wanda ake yayi a yanzu. Misali, Ɗan’azimi Baba, Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, Ado Gidan Dabino.
39. Kallon rainin da ake wa littattafan wannan adabi ya sa a yau ko da wani ya yi littafi mai inganci sai a jefa shi cikin kwandon sharar irin waɗannan littattafan.
40. Ana kallon marubuci kusan ɗaya da ɗan fim ta fuskar darajar su. Wasu ma sun fi ganin girman darajar mai yin fim.
Waɗannan alamomin sun taimaka wajen bunƙasar ”adabin kasuwar Kano,” to amma kuma su na taimakawa gaya wajen dakusar da cigaban adabin Hausa na sashen rubutun littafi.