• About
  • Contact
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Aron Fitila Ga Marubuta

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
September 13, 2012
in Da Hausa
0

 

Bismilla yau ma na taho,

Taswira zan ɗan zana.

 

Ya Jallah ka ba ni tagomashi,

Da basira don na zauna.

 

Yi salatin angon A’isha,

Ni gun sa na karkata so na.

 

Matsalar marubuta ‘yan’uwa,

Zan sa yatsa in nuna.

 

Marubuta ku ni ka tausayi,

Na fara shirin in daina!

 

Don kun ƙi tiyatar maganin

Ciwon da yake muku ɓarna.

 

A sana’ar kun gaza warware

Babbar illa mummuna.

 

A rubutu kun gaza ci-gaba,

Wayyo, ku ‘ya’yan ANA!

 

‘Ya’yan HAF, sauran ma haɗo,

Ogogin har da ƙanana.

 

Kaicon ku haɗin kai kun gaza,

Wallen ku na gan shi a rana.

 

Shi yas sa ba kwa kasuwa,

Gwandar ku tana ƙin nuna.

 

Haske a gida bai samuwa,

Lantarki sai an jona.

 

Dillalai sun muku kwaf ɗaya,

Rami ne ku kuka gina.

 

Sun kama tudu sun tsallaka,

Sun bar ku a zafin rana.

 

Hajar ku idan sun sai da su,

Sun hau jirgi sai Ghana.

 

Ko Dubai, Indiya sun gano,

Sabon aure sun ɗana.

 

Ku ko cika baki ɗai ku ke:

“Ni ɗin nan ni ke suna.”

 

“Tarin makaranta zahiran,

Wallai ni ba mai fi na!”

 

“Ni ne Na-Filinge, ka dakata,

In ka yi musu zan tona.”

 

“Shago na je ka ga dandazo

Na masoya sun zo gu na.”

 

“Kullum a gida na har dubu,

Mata da maza mun gana.”

 

Wallahi ku farga abokanai,

Zancen nan nai mini ƙuna.

 

Ku ne fa ka haskaka duniya,

Littafi shi ku ka kunna.

 

Malammai, sha’ir, ƙirƙirau,

Amma a gane ku a raina?

 

Mai dokar barci, gyangyaɗi

Ya ɗaukai ya kai Chana?

 

Mafitar nan nema za ku yi,

To tilas sai kun zauna.

 

Domin tsoron ku aya ta ji,

To dutse sai kun tauna.

 

Kai tanƙwasa ƙarfe in gani,

Laushi nai tamkar waina.

 

Mudu kuka sawa tsaf a yau,

Garin ku ku bi shi ku auna.

 

Mota in an hau za a ja,

Injin ta fa sai an wana.

 

Zancen nan ni kam na gama,

Don Allah kadda ku raina.

 

Fata na lamiri na faɗa,

Kun ɗauka ni sai murna.

 

Nan zan ɗiga aya bissalam,

Wata rana in mun gana.

 

Baitin mu talatin sa biyar,

Na ƙirga ba in’ina.

 

Sunan mai baiti Iro ne,

Sa ‘Sheme’ gaban sa ka manna.

 

TAMAT

13 ga Satumba, 2012

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: kiramarubuta
Previous Post

Bugu Da Guduma

Next Post

Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

Next Post
Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100
  • Wanda Ba Ya Fushi Da Yin Allah

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d