Allah na, ya sarki gwani,
Roƙo naka yi zan soma.
Buɗe mini tagar zurfafa-
War ƙwalwa, ban ilhama.
Domin manzon ka Ahmadu,
Wannan ɗan hannun dama.
Don Dija uwar duka muminai,
Don Zainab bint Khuzaima.
Wannan matan na Muhammadu,
Ar-Rasul hannun sa na kama.
Wani ja’iru ɗan ɗan karuwai,
Shi ne ya taɓo ne da kima.
Wai ya riƙe gurnati har da bam,
To gu nai ba ni da girma.
Shawaraki zo zauna ka ji,
Koli na za ni baje ma.
Ka ɗauka na manta da kai?
Ho takari da babu igama!
Yau sam sam lallai ba ragi,
Wallai ni sai na rama.
Dundu da gula zan yi maka,
Ga ƙusa za ni buga ma.
Kai tashi da mugun gyangyaɗi,
Sabon saƙo zan yi ma.
Yasin ce zan jawo maka,
Alƙunut kai har ma Amma.
Ko ko dai baiti ’yan kaɗan,
Babban gyambo in fama?
Ɓarawo ne na ƙwaƙwalwa,
Nomau ɗan Sarkin Noma!
A kwatar can nats tsamo ka,
Wawan kai sai kak koma.
Na ba ka kuɗi har fam ɗari
Jari, ga shanun noma.
Su ne ka kaɗar ga kilakilai,
Ka koma dogon hamma.
Kullum zagin mu cikin gari,
Harshe ya kai mil goma.
Kullum sara ta ɗai kake,
Ni gamji ina daɗa girma.
To ganye ne kaka sassabe,
Ni tushe na bai suma.
Na gode Allah Rahimi,
Duniyar nan na sha fama.
Yau ga ni garas kuma tangaran,
Ƙarfi ma yanzu na soma.
Farkar ka a ran nan ta dafa
Maka girki, oh tai himma!
Ta ba ka tuwo ka nannaga,
Wulli mai babbar loma.
Soyen alade ta buga maka,
Ta ba ka da dambun nama.
Ka take cikin ka da burkutu,
Ka ɗauka koko ta dama!
Sarkin kwaɗayi, mai kwarmato,
Doki mai ƙarnin nama.
Kai ba ka aboki yanzu mai
Sallah, sai arnan Koma.
Wawan sarki ba ka da kai,
Ɓutal, gyandai, camama.
Sannun ka da ƙaryar arziki,
Banza kullum sai homa.
Bayahude lallai ka riƙa,
Wai kai yau babu hukuma.
Dolo har yau ba ka kintsu ba,
Kai kullum ka sha mama.
Bunsuru mai neman ’ya tasa,
Domin kai ba ka iƙama.
Mai danne yara ƙanƙana,
Da uwar ma in ka ga dama.
Ba jinƙai, mugun makiri?
Ka zambaci hatta umma.
Mai laifi ba ka da karsashi,
Ɗan sanda kai yak kama.
Kai tusa, warin ya bugo
Daga Legas ya kai Bama.
Izzar ka ta ja maka zunguri,
Ga tarko na ya kama.
Je tuba ka daina haɗin faɗa,
In ka ƙi mu dinga husuma.
Yaƙin biro kuma ni da kai,
To yanzu ka san na soma.
Sunan ka mance? Iro ne,
Ko ‘Sheme bugu da guduma’.
Mai horon arna jiddadum,
To yau dai kan ka na koma.
Dangi na ku na gaida ku,
Addu’a a gare ku na nema.
Aikin da nake kun taimaka,
Hannu kun sa kun tama.
Ƙyale ni na harbi haƙarƙarin
Mugu mai sato nama.
Zan karya wuyan azzalumi,
Kun san ni da zafin nama.
Ƙarshe nan ni roƙo na yi,
Ya Jallah ka ba ni in kama,
Igiyar nan ta Islamiyya,
Na tuba gare ka na koma.
Baitin waƙar mu guda biyar,
Sai ku tara har sau goma.
TAMAT
26 ga Agusta, 2012