• About
  • Contact
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Ƙalubale Ga Aminu Ala

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
July 31, 2012
in Da Hausa
0
Ƙalubale Ga Aminu Ala
Aminu Alan Waƙa

Aminu Alan Waƙa

Salam. Jiya na ce zan yi wa Aminu Ladan (Alan Waƙa) wani ƙalubale. Na san za ku ce kun ji shiru. To a yau ga shi na kawo muku. Sai a karanta da haƙuri; kun san abin ‘yan koyo (dariya da ƙwalla). Kuma don Allah sha’irai a yi mini gyara.

 

ƘALUBALE GA AMINU ALA

 

Bismillah zati tsarkaka na gun ka,

Buɗan ƙwaƙwalwa baitika in shirya.

 

Nai dogaro a gare ka neman sa’a,

Allah Ta’ala wanda bai tarayya.

 

Ƙaro salati gun sa hasken haskaka,

Manzo na Dija cikamakin anbiyya.

 

Na yo salati har dubu kuma sau dubu,

Tsira ga Mamman wanda bai fariya.

 

Wannan da yai yaƙi da fir’aunoni,

Ya karya dukkan gunkunan jahiliyya.

 

Tsira, aminci Rabbana ka isar masa,

Manzo gare shi a kullu na yi biyayya.

 

Saƙon sa ya zo ne a babban kundi,

Komai da ke ciki ba ni yin jayayya.

 

Wani ɗan mafarki ne yake cizo na,

Ala nake neman ya yo alfiyya.

 

Ala Aminu da ke Kanawan Dabo,

Sarki uban ‘ya’yan da ke ƙafiyya.

 

Waƙa yana yi tai dubu na ƙirgo,

Duk wanda ya ce a’a shi yai ƙarya.

 

Kullum yaƙini nai ya wargaza zalumai,

Yaƙi yake da halin mu Najeriyya.

 

Tauhid a ilmu nasa Abban Husna,

Mugun halin mu da shi yake ƙiyayya.

 

Biron sa ga kaifi, da ya zaro shi,

Wane takobi in yana gogayya.

 

Duk ya karaɗe lunguna da jihadi,

Bakin shi bai hutu wajen ilmiyya.

 

Daddyn su ‘yanbiyu fasihul zamani,

Baban Sa’adatu, Rabbu yai sakayya.

 

Duka baitukan Ala akwai su a rediyo,

Kuma mun karanta darasin mun koya.

 

Amma mu duba ƙanƙana ne galiban,

Bai yin awa ɗaya sai ya ce ya tsaya.

 

Ala ka karkaɗe kunnuwa domin ka ji,

Roƙo nake, Allah ya sa ka shirya.

 

Lallai fa aikin nan da ke hannun ka,

Har yau da saura, sai ka ɗauro niyya.

 

Takun ka yai nisa uban Muhsinu,

Amma su Rumi sun yi ma tserayya.

 

Ban ce a dole ka zam kamar Bin Malik,

Ko ko a ce kai ne gaban su ba manya.

 

Lallai su Rumi sun yi ma nisa a nan,

Sai kai shiri domin ka kamo hanya.

 

Hau taguwar ka da tsikari ya fasihu,

Keto hazon daji cire gajiyya.

 

Azama kake Ala a kan alƙaluma,

Domin ka zano baituka ba jinya.

 

Tabbas jiran ka muke amon ta ka kunno

Sauti dubu, baiti dubun alfiyya.

 

Ƙalubale ne ga shi nan na harbo,

Cene da ni ‘cas’ ka ji mai alkunya!

 

Sabon bajinta ne nake ta kira ka yi,

In ka ƙiya tilas in ɗauko lauya.

 

In dai ka kasa zan yi kukan kura,

In ce Kanawa kar su ‘yam ma miya.

 

Suna a ƙarshe Sheme ne Burhama,

Yaro makoyi, sallama kulliya.

 

Asali ƙasar mu ta Dikko ɗakin kara,

Amma Abuja nai zaman tarayya.

 

Hamdan kasiran ga ni nan na sauko

Daga mumbarin saƙon kiran alfiyya.

 

Baiti talatin ne a wannan waƙa,

Ƙaro guda huɗu maganin jayayya.

 

Ya Jallah sa Ala ya ɗau aniyya,

Domin darajar Ɗaha mai Safiyya.

 

Allah daɗo tsirar Rasulu ka ƙara,

Amin da amin Jallah na dasa aya.

 

TAMAT WA BIHAMDIL LAH

31 ga Yuli, 2012

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: alfiyyaAminu Alakiraƙalubalewaƙe
Previous Post

Sam Nda-Isaiah @ 50: My Personal Odyssey With Chairman

Next Post

Bugu Da Guduma

Next Post

Bugu Da Guduma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100
  • Wanda Ba Ya Fushi Da Yin Allah

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d