Marubuta irin su Ibrahim Sheme ana yin su ne sau ɗaya a ƙarni.
Sheme marubuci ne da ba shi da tsara a wannan zamanin, littafin sa ɗaya tak ya girmi ɗari na wasu fitattu marubutan, tunda daga fejin farko na littafin sa za ka fahimci irin tsananin baiwa da kwanyar da Allah ya zuba masa.
Littafin sa na ‘Yartsana 🔞 plus ne za su iya karantawa. Na yi ta maimaitawa cewa akwai mutane masu ƙwaƙwalwa a cikin al’ummar Hausawa ba a sani ba, su na da baiwa wacce ba ta da sirki. Ka na karanta littafin sa ka na ganin komai kamar a gaban ka aka yi.
Ina mafarkin na yi rubutu tare da Oga Sheme ko na littafi ko na series saboda na san daraja ta za ta ƙaru a fannin rubuta. Saboda Sheme dole daga kan sa a yi kiɗan tashi.
Mu na da marubuta a cikin Hausawa masu basira.
GOLDEN PEN