Ƙungiyar Tunawa Da Mamman Shata (Mamman Shata Memorial Association)
TARON FARKO
Arewa House, Kaduna
Asabar, 15 ga Yuni, 2013
JAWABI KAN MAƘASUDIN KIRAN TARO DAGA MAI KIRAN TARO, MALAM IBRAHIM SHEME, Editan Jaridar Leadership
Ina farawa da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin mu, fiyayyen talikai, Muhammad (SAW).
Da farko ina addu’a Allah ya jiƙan Alhaji Mamman Shata, Allah Ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, ya albarkaci bayan shi, ya sa ayyukan sa na alheri su zama tsira a gare shi, kuma ya yafe kurakuran da ya aikata, amin summa amin.
Mahalartan wannan taro kuma ina godiya a gare ku da ku ka amsa gayyatar mu, ku ka taso daga garuruwa daban-daban, wasun ku ma su ka yo asubanci, ku ka zo wannan gari domin halartar wannan taro wanda mu ke fatan Allah ya sa wa albarka. Na yi farin ciki ƙwarai ganin cewa kowannen ku ya na da aikin da ya sa a gaba, amma a yau ya sadaukar da lokacin sa, ya bar duk abin da ya ke yi, ya zo. Wannan ba ƙaramin ƙoƙari ba ne, kuma alama ce ta goyon bayan da ku ka bayar ga shukar da mu ke son mu yi a yau. Na gode ƙwarai da gaske.
Ina farin ciki matuƙa da Allah (Subhanahu wa Ta’ala) ya nuna mana wannan rana wadda mu ka daɗe mu na tsinkayar zuwan ta. Rana ce wadda a cikin ta mu ke yin zaman farko domin sa ɗan ‘ba’ a wani yunƙuri na karrama wani fasihi wanda babu irin shi a fagen sa na waƙa a ƙasar Hausa, wato Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina. Kuma wannan karramawa ita ce ta farko da aka yi masa tun bayan rasuwar sa a ran 18 ga Yuni, 1999. Wato kenan nan da kwana uku kacal zai cika shekara 14 da barin duniya. Duk da yake wannan karramawa ba irin ta ba shi takarda ko lambar girma ba ce kamar yadda Gwamnatin Tarayya da kuma Jami’ar Ahmadu Bello su ka taɓa yi masa, ita ma wannan kwatankwacin irin waɗannan ɗin ce, domin ita ma wani yunƙuri ne na nuna gamsuwa da aikin da Alhaji Shata ya yi wa ƙasar nan, musamman gudunmawar sa ga cigaban ƙasa ta hanyar yin amfani da fasahar da Allah ya yi masa.
A taƙaice, ba tare da na yi dogon sharhi kan irin wannan gudunmawa tasa ba, zan iya cewa Shata ya faɗakar da ’yan Nijeriya tare da nishaɗantar da su ta hanyar waƙoƙin sa, waɗanda ke cike da nusarwa; wasu su jefa ka kogin tunani, wasu su sa ka dariya, kai wasu ma su ba ka haushi a bisa irin fahimtar da ka yi masu. Ya taimaka ƙwarai wajen adana tarihi da al’adun Malam Bahaushe. Don haka mu ke ganin ya kamata a yi wani hoɓɓasa na ci gaba da tuno da wannan bawan Allah a kai a kai, musamman a ƙungiyance. Da gaske ne cewa ko ba mu yi wani abu ba da wuya a manta da shi tunda dai ya bar dubban waƙoƙi da ake sawa a gidajen rediyo da na talabijin, kuma mutum zai iya jin su a motar sa ko a komfuta ko a intanet, to amma duk da haka mu na ganin cewa idan mu ka yi wani tsari na daban ban da waɗancan, to sanya sunan Shata a zukatan jama’a zai ƙaru.
Saboda haka ne mu ka ga dacewar a kafa wata ƙungiya don tunawa da shi, wadda za ta riƙa aiwatar da wasu tsare-tsare da ayyuka waɗanda za su sa a ƙara zurfafa tunawa da shi tare da ba shi matsayin da ya dace da fasihai irin shi. Babu shakka, akwai fasihai irin Shata da aka yi wa hakan a wasu ƙasashen, sannan a nan ƙasar an yi wa manyan ’yan siyasa da kishin ƙasa irin wannan ƙungiyar, kun ga kenan yin hakan ba wani sabon abu ba ne.

Shin me wannan ƙungiya za ta iya yi? Na farko dai, za ta riƙa shirya taro na kwana ɗaya a duk shekara inda za a kira masana su gabatar da jawabi a kan wanene Shata da kuma ayyukan sa, kuma a yi masa addu’a. Wannan taro za a iya shirya shi a daidai zagayowar ranar da ya rasu, wato 18 ga Yuni. Masoyan Shata da iyalan sa da jami’an gwamnati da sauran jama’ar da ke da sha’awa za su iya halartar taron. Idan abin ya bunƙasa, ƙungiya za ta iya maida taron na kwana biyu ko na mako ɗaya inda za a yi kamar kalankuwa ta makaɗa da mawaƙan Hausa inda kowannen su zai baje hajar sa. Na biyu, ƙungiyar za ta iya yin jagora wajen kafa wata cibiya da sunan, wato misali, Cibiyar Mamman Shata (Mamman Shata Centre a turance) ko Cibiyar Mawaƙan Hausa ta Mamman Shata (wato Mamman Shata Hausa Music Centre). Ita wannan cibiya za ta kasance wani gidan tarihi ne inda za a tara duk wasu abubuwan tarihi da su ka shafi Shata. Babban dai shi ne waƙoƙin sa. Za a tattaro duk waƙoƙin sa a adana su a wannan gida da nufin samar da su ga masu bincike da masu saurare. Wannan ya na da muhimmanci, musamman idan mu ka yi la’akari da cewa a yanzu waƙoƙin Shata a warwatse su ke a kafafen yaɗa labarai (musamman gidajen rediyo da na talbijin), sannan wasu su na hannun ɗaiɗaikun mutane. Akwai mutumin da ke da waƙa ɗari, wani dubu ko fiye a hannun sa, akwai ma mai dubu uku! Sannan akwai mutumin da ya ce mani akwai waƙar da Shata ya yi masa wadda ba wanda ya ke da ita sai shi ka]ai. Ban taɓa jin sunan mutumin ba, amma ya na kunna min waƙar a wayar sa sai ga muryar Shata na fita, ya na yi wa mutumin nan waƙa.
Su kan su gidajen rediyo da na talbijin da ke da laburare na waƙoƙi, wasu babu tabbacin ɗorewar ingancin waƙoƙin.
To, idan yau mu ne, gobe ba mu ba ne, saboda haka a duk ran da aka ce babu irin waɗannan ɗaiɗaikun mutanen sai ka ga waƙoƙin da ke hannun su sun zama na gado, an rarraba su, daga nan sun shiga hanyar ɓacewa. Saboda haka, Cibiya za ta yi ƙoƙarin samo kwafe na duk waɗannan waƙoƙi na Shata domin a adana su a wannan gida na tarihi.
Kuma wani abu shi ne yadda zamani ke sauyawa ta fuskar na’urorin kimiyya. A da can, a farkon zamanin Shata, babu ma kayan rikodin. Wannan ya sa, kamar yadda shi da bakin sa ya faɗa, ba a ɗauki wasu waƙoƙin da ya yi a faifai ba. Kun ga kenan babu su ko kaɗan, domin wasu bai maimaita su aka ɗauka ba. Ana nan, da tafiya ta yi tafiya, sai aka zo ana samun waƙoƙin sa a garmaho; daga nan sai kaset, sai kuma sidi (CD), sai ga dibidi (DVD), sai MP3 ya zo, sai MP4; ga su yanzu a intanet da kuma cikin wayoyin mutane. To nan gaba ba mu san abin da ke tafe ba. Ta yiwu a samu wata wa}a wadda na’urar da ke akwai ba za ta iya sarrafa ta ba domin ƙila ba a riga aka juya ta zuwa sabon nau’in kimiyyar ba tun a baya.
Sannan ban da waƙoƙi, wasu abubuwan na tarihi da za a iya tattarawa a wannan cibiya sun haɗa da hotuna da tufafi da takalma da agogo da hula da duk wani abu da ya danganci mamacin. A ɓangaren hotuna, a cibiyar za ka iya samun hotunan iyalin shi, da na mutanen da ya yi wa waƙa da na wasu wurare da ya je ko ya ambata a waƙa. Ga wani misali: lokacin da mu ke tattara tarihin Shata domin yin littafi, mun samo ɗimbin hotunan mutanen da Shata ya yi wa waƙa, da na Shatan da na iyalin shi. Waɗannan hotuna su na nan a hannun mu. To ran da ba mu fa? Ka ga ƙila wasun su su salwanta. Amma in akwai cibiya, sai mu kai su can a aje saboda mai buƙata ya je ya gan su.
Bugu da ƙari, ina hangen cewa wannan cibiya za ta iya kasancewa ta kowane mawaƙin Hausa, in dai wanda ya yi amfani da kiɗa ne. Wato irin su Narambaɗa, Ɗanƙwairo, Uji, Ɗanmaraya, Sarkin Taushi, Ɗan’anace, Ahmadu Doka, Sirajo Mai Asharalle, Ɗanbade da Barmani Choge. Hatta makaɗan wannan zamanin, waɗanda ke amfani da fiyano, irin su Aminu Ala, Adamu Nagudu, Yakubu Muhammad, Sani Danja, Abubakar Yarima, Fati Nijar, Maryam A. Baba, Rabi Mustapha, Umar M. Shariff, Adam A. Zango da ire-iren su da dama, za a iya samun wani wuri da aka keɓe masu a wannan cibiya. Dalilin ƙara sauran makaɗa da mawaƙa a wannan tsari shi ne ganin cewa ba zai yiwu a yi cibiyoyi daban-daban a kan dukkan waɗannan mawaƙan ba, waɗanda su ma ya kamata a ce akwai inda mutum zai je kai-tsaye ya samu ayyukan fasahar su can wata rana lokacin da babu mu ko babu su – kamar yadda babu Shata a yau.
Za a iya yin wannan cibiyar a garin da aka ga ya dace, Funtuwa ce ko Katsina ko Kano ko Kaduna, ko ma ina ne a ƙasar Hausa. Kuma za ta iya kasancewa cibiya mai zaman kan ta kamar yadda ake da Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua a Abuja, sannan za ta iya zama a ƙarƙashin wata jami’a kamar yadda ake da Gidan Arewa don tunawa da Sardauna a Kaduna. Wannan ƙungiya tare da iyayen ta ko mashawartan ta za su iya yanke shawara a kan haka. Manufa dai ita ce a samu wani wuri inda za a tattara waƙoƙi da tarihin Shata, ƙila kuma da na wasu mawaƙan, ta yadda tarihi ba zai shafe dukkan sassan su ba.
Babu shakka, kai daga ji ka san cewa wannan aiki gagarumi ne. Aiki ne wanda ke buƙatar lokaci, da sadaukarwa, da haɗin kai, da kuma kuɗi masu gida rana. To amma duk da haka, aiki ne mai yiwuwa. Saboda haka haƙƙin ƙungiya ne ta tabbatar da cewa ta ɗauki aikin da gaske idan har da gasken ta ke yi. Kuma ƙungiya ta sani, ba kuɗi ne babba ba a wajen wannan aiki, a’a, sadaukarwa ce da kuma ƙauna ga wanda aka yi domin shi da kuma ƙaunar mu ga al’adu kyawawa na Hausa. Idan har akwai sadaukarwa, to kuɗin aikin sai su zo cikin sauƙi. Ina roƙon ku da ku zage dantse, ku tashi tsaye wajen tabbatar da faruwar abin da mu ke so mu yi a wannan ƙungiya.
Haɗuwar mu a nan a yau alama ce ta irin ƙaunar mu ga wannan aiki. Dukkan mu a nan mun zo ne saboda mun amince da mu yi wannan aikin, domin fa ba wanda aka aika wa da kuɗin mota kafin ya zo, ko aka ce za a ba shi na komawa gida. Saboda haka abin farin ciki na ne ganin cewa mun ƙudiri aniyar yin wannan aiki.
A ƙarshe, ina kira ga iyalin Alhaji Shata, waɗanda akwai wakilcin su a nan wurin, da su ba ƙungiyar nan haɗin kai domin ta cimma ƙudirorin ta. Idan sun yi hakan, to sun kyauta wa Baba Shata, kuma sun kyauta wa ƙasar nan.
Ina fatan tattaunawar mu za ta yi albarka, tare da addu’ar Allah ya sa wannan shuka da za mu yi ta yi albarkar da kowannen mu zai yi farin ciki da ita.
Ina roƙon Allah da ya taimaka mana, ya ba mu ikon kafa wannan ƙungiya da gina ta da kuma aiwatar da ƙudirorin ta, amin summa amin.