Karuwanci sana’a ce da ta daɗe a ƙasar Hausa. Haka ma rubutun ƙirƙirarrun labarun Hausa. Littafin ’Yartsana ya fito da sabuwar sigar rubutun labarin karuwanci wanda tun farkon fitowar sa ya tada ƙura a duniyar adabin Hausa. Tun yaushe aka rubuta littafin? Wanne irin faɗi-tashi littafin ya sha zuwa yanzu? A tattaunawar mu da marubucin littafin, babban ɗan jarida Malam Ibrahim Sheme, ya amsa waɗannan mabambantan tambayoyi da ma wasu da dama. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
AMINIYA: Ka daɗe da rubuta littafin ’Yartsana. Ko za ka yi mana bayanin ainahin tarihin rubuta shi tun daga farko har zuwa yanzu a taƙaice?
SHEME: Na fara rubuta littafin ne a cikin mujallar Rana, wadda kamfanin wallafa na Hotline ke bugawa a Kaduna, a cikin shekarar 1992. A lokacin, ni ne Editan Rana ɗin. Sunan labarin “Balaraba: Labarin ’Yar Gagara”. Kuma na rubuta labarin ne ana gutsura wa masu karatu a duk mako biyun da mujallar ke fitowa, a wani fili na nishaɗantar da su ta hanyar adabi. Idan ka tuna, na riƙa gabatar da irin wannan filin a jaridar mako-mako ta Nasiha a lokacin da na ke aiki a matsayin Mataimakin Editan ta a tsakanin 1991 da 1992.
A cikin 1993 sai na tafi Birtaniya domin ƙaro karatu. Sai na bar sauran labarin na ’Yartsana a hannun babban aboki na, Malam Ibrahim Malumfashi, wanda yanzu Farfesa ne, domin ya riƙa bayarwa a mujallar Rana ana bugawa. To amma ina can sai aka rufe kamfanin Hotline ɗin, don haka sai filin ya daina fitowa. Da na dawo daga karatu, sai na yanke shawarar in fito da littafin wannan labarin. Amma fa a lokacin da ake warwarar labarin a mujallar Rana, ina jin bai fi rabin yawan shi ba, don haka dai na ci gaba na ƙarasa shi. Littafin ’Yartsana ya fara fitowa a cikin 2003, wato shekara kamar goma daga lokacin da na fara rubuta shi. A cikin wannan lokaci, na dage ƙwarai wajen inganta labarin ta hanyar ƙara masa duk wani gishiri da na ga ya dace a ƙara saboda a fito da jigon sa sosai. Kuma na sauya masa suna zuwa ’Yartsana ne saboda kada a alaƙanta shi da wata ’yar fim ɗin Hausa, wato Balaraba Mohammed, wadda ta rasu a daidai lokacin.
AMINIYA: Waɗanne darussa ka ke son nusarwa ga al’umma a wannan littafi?
SHEME: Darussan su na da yawa, kuma ina jin masu nazari ne za su fi ni iya fito da su. Ni a gani na, da farko dai ina so a san illar karuwanci, musamman abin da ke jawo karuwancin. A nan, na alaƙanta shi da auren dole. Na yi ƙoƙarin nuna wa al’umma cewa ya kamata a bar yarinya ta auri wanda ta ke so. Bayan haka, na nuna yadda karuwanci kan shafi zamantakewa a al’umma, tsakanin miji da mata, tsakanin masu mulki, tsakanin su kan su karuwan da maneman su, tsakanin mutum da Mahaliccin shi, da sauran su. Haka kuma a ƙarshe an fito da illar zinace-zinace da ta shaye-shaye, musamman wajen da aka nuna yadda ake hadahadar hodar ibilis da yadda cutar ƙanjamau ta kama wasu daga cikin manyan taurarin labarin, don a wayar da kan mutane, a tsoratar da su.

AMINIYA: Kafin fitowar wannan littafi, an samu littattafan hikaya na zamani, musamman waɗanda ake kira Adabin Kasuwar Kano. Shin ta yaya wannan littafi naka ya bambanta da irin su?
SHEME: Kalmar ‘Adabin Kasuwar Kano’ an fito da ita ne da nufin ƙasƙantar da rubutun Hausa, a nuna cewa bai kai bante ba idan an kwatanta shi da rubutun da aka yi a baya. Wannan kuskure ne, musamman ma da aka yi wa harkar rubutun jama’u, wato aka nuna cewa daga tsakanin lokaci kaza zuwa lokaci kaza babu rubutu mai inganci kwata-kwata. Masu wannan tunanin sun manta da cewa a kowane lokaci al’umma ta na samun nagartattun mutane da kuma masu naƙasu.
Ko kaɗan ban ɗauki ’Yartsana a matsayin ɗan ajin su Adabin Kasuwar Kano ba don kawai ya fito a zamanin da ake ce-ce-ku-ce kan irin wancan adabin. Lokacin da na ɗora biro kan takarda don rubuta shi, na ƙudiri yin rubutu mai inganci wanda za a ɗaga a ce, “E, wannan ya bambanta da sauran!” Kuma a gani na, na cimma wannan nasarar domin ko makaho ya shafa littafin ya san cewa ba kwashi-kwaraf ba ne, musamman ta fuskar ƙwarewar bada labari, warwarar jigo, nahawu, zurfin fiƙira, kai har ma da ɗab’i. Za ka ce wannan yabon kai ne; e, yabon kan ne, to amma ba irin na jahilci ba. Wanda ya yi gardama, ya duba ya gani.
AMINIYA: Ka ci gasa da littafin nan. Ka yi mana ƙarin bayani.
SHEME: Ina jin a cikin shekarar 2007 ko 2008 ne wata cibiya mai suna Gidauniyar Tunawa da Injiniya Bashir Ƙaraye da ke Abuja ta shirya gasar rubuta ƙagaggun labaran Hausa ta ƙasa baki ɗaya. To, ni ne na zo na ɗaya da wannan littafin na ’Yartsana. Balaraba Ramat Yakubu ta zo ta biyu, sannan Maje El-Hajeej Hotoro ya zo na uku.
AMINIYA: Ko akwai wasu makarantu ko jami’o’i da su ka saka littafin nan a manhajar karatun su?
SHEME: Ƙwarai kuwa. Su na da yawa. Na dai san cewa tun daga lokacin da littafin ya fito ɗalibai da dama a wasu jami’o’i da manyan kwalejoji sun yi nazarin sa. Wasu ɗaliban ma sun rubuta kundin neman digirin su na farko ne a kan littafin. An yi a Kano, Katsina da Sakkwato. Wasu ɗaliban sun aiko mani da kwafe na kundin su. Ko kwanan nan wata ɗaliba ta aiko mani da nata kwafen daga Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato. Akwai ma malamin jami’a wanda ya yi kundin neman digirin sa na uku a kan littafin. Haka kuma akwai malaman jami’a irin su Dakta Bashir Abu Sabe da su ka gabatar da maƙala a kan littafin. Ko a yanzu da mu ke magana, ana karanta littafin a wata jami’a bayan an saka shi a manhajar karatun ɗalibai masu nazarin Hausa.
AMINIYA: Shin wace martaba ko tagomashi ka samu daga littafin nan na ’Yartsana?
SHEME: Martaba ta farko ita ce muhawarar da littafin ya janyo jim kaɗan bayan fitowar sa, kuma har yanzu ba a daina ta ba. Ban tsammanin akwai wani littafin Hausa a tarihi da aka yi faɗi-in-faɗi a kan shi kamar ’Yartsana. A zaurukan musanyar ra’ayi na yanar gizo har zuwa cikin jaridu da sauran majalisun hira an yi ce-ce-ku-ce kan littafin, masu yabo na yi, masu suka na yi.
Na biyu, littafin ne ya zo na ɗaya a babbar gasar rubutu wadda kafin a yi ta an shafe aƙalla shekara 17 rabon da a yi gasar rubutun Hausa. A waccan ta 1990 ɗin ma, wato wadda gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya, ni ne na zo na biyu da littafi na mai suna Kifin Rijiya.
Haka kuma wani ƙarin martaba shi ne littafin ’Yartsana ya sauya tunanin marubuta da dama. Domin akwai marubutan da su ka ce mani karanta littafin ya sauya masu tunani kan yadda ya kamata a yi rubutun hikaya na Hausa, da irin ingancin da ya kamata littafin Hausa ya fito da shi. Kai, akwai ma waɗanda su ka yi ƙoƙarin koyon dabarun rubutu da su ka gani a littafin!
Sannan uwa-uba, ɗalibai da malaman jami’a su na nazarin sa. Wannan ma martaba ce.
AMINIYA: Wasu na ganin cewa yadda aka rubuta littafin ma bai dace da al’ummar Hausa ba, domin wasu na cewa ma kamar ana koya wa mutane karuwanci ne da sauran su. Me za ka ce game da wannan batu?
SHEME: Ƙwarai kuwa, wannan na daga cikin muhawarar da aka yi. To amma kada ka manta, akwai waɗanda su ka yi dogon sharhi kan dacewar littafin. Abin tambaya shi ne, shin har akwai wani rubutu da ya dace da al’ummar Hausa, musamman idan zai tunkari wata matsala da ta addabi ƙasar Hausa? Shin karuwanci ba wani muhimmin ɓangare ba ne na rayuwar Hausawa – a da da kuma yanzu? A da, da wuya a ce ga wani matsakaicin gari a ƙasar Hausa inda babu gidan karuwai. Duk da yake mutane ne da ake kyara, amma kuma sun kasance wani nau’i ko sashe na garin!
Kamar yadda aka nuna a ‘Yartsana, hatta saraki da attajirai da ma’aikata da ’yan makaranta su na cikin manema mata! Ko a yau ɗin nan karuwanci na ɗaya daga cikin matsalolin da ke addabar ƙasar Hausa, ba kamar idan ka yi la’akari da yadda karuwancin ya sauya daga na kama ɗaki zuwa na zinace-zinacen da ake yi ba tare da an shirya gida da sunan gidan karuwai irin na da ba. Kuma kusan komai da ake aiwatarwa, tare da karuwan zamani ake yin shi. Karuwai su na fa da ɗaurin gindi a ƙasa, a da da yanzu! Kamar yadda Malam Ɗanmani Caji ya ce a wata waƙa tasa, in da a ce babu manema mata to da ba a samu karuwai ba.
Amma duk wannan ba ya na nufin cewa karuwanci ya dace ba ne. A’a, littafin ma ya na nuni ne da yadda Musulunci ya yi hani da karuwanci ko ma kusantar zina. To amma duk wanda ya ce maka bai kamata a yi magana kan karuwanci ba, to ya na yaudarar kan sa ne, kuma ba so ya ke a magance matsalar ba. Kuma ka tuna, ba ni ne na fara rubutun adabi kan karuwanci ba, mawaƙan mu da dama sun yi, kama daga kan su makaɗa irin su Alhaji Mamman Shata da Ɗanmani Caji da Ɗangoma har zuwa kan malamai irin su Malam Aƙilu Aliyu da Malam Mu’azu Haɗejiya.
Sannan batun a koya wa mutum karuwanci, wannan rashin fahimta ne. Littafi ne kan karuwanci, to yaya za a yi ba a fito da ainihin yadda ake karuwancin ba? Ko likitoci, ba su ƙoƙarin warkar da cuta har sai sun naƙalci yadda cutar ta ke.
AMINIYA: Ya zuwa yanzu, sau nawa aka buga shi daga fitowar sa kuma kwafi nawa aka sayar?
SHEME: Bugu na kwana-kwanan nan shi ne na uku ko na huɗu, na manta. A bugu na farko an buga 2,000, daga nan aka ci gaba da buga 1,000 ina jin sau biyu, sai kuma yanzu da aka buga 2,000. Kuma duk wanda aka buga babu ko ƙwaya ɗaya in ban da wanda ya fito kwanan nan, wanda ke kasuwa. Shi ma bugun kwanan nan ɗin, matsa mani aka yi kan a sake fito da shi, musamman ɗalibai da ke neman shi ruwa a jallo don su yi nazari.

AMINIYA: Ko akwai wasu bayanai game da littafin da za ka so mutane su sani, waɗanda ban tambaye ka ba a nan?
SHEME: Abin da zan faɗa, ba a kan littafi na kaɗai ba ne. Ina so mutane su maida hankali wajen karance-karance maimakon kalle-kalle. Yanzu kallon talbijin ya yi wa mutane yawa, musamman ma matasa. Sai ka ga mutum ya shekara bai karanta littafi ba, wai da ya fara sai ya ji kan shi na ciwo! Amma sai ya yi awa uku ya na kallon fim a kusan kullum. Ko kuma ya ce karatun littafin hikaya sai mata. Wannan kuskure ne babba. A ƙasashen da su ka ci gaba, an ɗauki karatun ƙagaggun labarai da rubutattun waƙoƙi da muhimmanci ta yadda a duk wata a cikin albashin mutum akwai kasafi na littattafai da za a saya a karanta.
Karatu ya na buɗe ƙwaƙwalwa, ya zabga haske cikin tunani, ya ƙara ilimi. Karatu ya na bambanta mai yin shi da wanda bai yi, ya saka babbar tazara a tsakanin su. Don haka ina kira ga jama’a da su maida hankali wajen karanta littattafai da jaridu, musamman waɗanda aka rubuta cikin harsunan mu na gado.
—
* Na ciro wannan hirar daga jaridar Aminiya ta ranakun Juma’a, 23 da 30 ga Disamba, 2016