KIƊAN FARAUTA
(Taken Mamman Ɗanfagge)
Na ALHAJI SURAJO MAI-ASHARALLEF (Farautan Katsina)
Rubutawa daga faifai: Ibrahim Sheme
*
Lale ahayye yere,
Zuljalali, wa ɗan yaro?
–
Haka dare marecen kura,
Yaro ka je ka nemi ya naka.
–
Kai wanga kiɗin da na fara,
Waƙar mutum guda ɗai tas sa.
–
Muhammadu Ɗanfagge ya zo,
To don saboda kai nai yi ta yanzu.
–
Baturiya Sa’adiyya,
Ranar bikin ta ban manta ba bara.
–
Mamman Ɗanfagge Mamman shi ne ya ba ni riga shadda kyauta.
–
Har da Wazirin Mamman,
Mamman ya ba shi riga shadda kyauta.
–
A faɗa a cika sai manya,
‘Yan yara ba su yi mani wannan yanzu.
–
Muhammadu Ɗanfagge ya zo,
An ce yana cikin taron nan zaune.
–
Ga kiɗin maza na fara,
Har na tuno da dokar daji.
–
Ga kiɗin maza na fara,
Har na tuno da dokar daji yara.
–
Kai, wanga kiɗin ƙaura ne,
Ba masu zage-zage fage ba yara.
–
Mai wuƙaƙ ƙashi banza ne,
In dai Surajo har na motsa yanzu.
–
Yau tauri ya ɓaci,
Tauri na yanzu duk ƙwaya ce, yara.
–
Sai an shawo rasta,
An zo ana ta mamashalon wohi.
–
Kai da ka buga mashi ƙarhe,
Burki ƙashi – ina labari?
–
Kai, da ka caka mashi tsinke,
Burki ƙashi – ina labari?
–
Ga Amadu nan Ɗankurna,
Ya ɗau kuɗin shi ya ba Mamman yanzu.
–
Samari sai shagali na,
Har na tuno da Mamman Vice.
–
Na tuna Mamman Vice,
Wannan ya na ƙasas Saudiyya yara.
–
Kai, ina masoyi na ne,
Baballiya mijin Zahra’u, bai nan?
–
Yara na tuno Alkasim,
Jikan Makoɗa mai ƙaunar mu bai nan.
–
Babandi mai kaɗa mota,
Shi ma yana gida bai zo ba yara.
–
Duw wanda ya ba ni abin shi,
In na faɗe shi ban laihi ba yara.
–
Tuna mani dogon yaro,
Baballiya mijin Zahra’u.
–
Ɗan Hajiya na gode,
Har na tuno da ran ATK bai nan.
–
Da na yi bayanin waƙa,
Mamman Surajo ya tuna Bogi.
–
Ina Labaran yak koma,
Mai jan hali na Mamman Vice?
–
Mamman Bashar na gode,
Yaro ɗan ƙarami mai naira bai nan.
–
Wai ina Bashar bai zo ba,
Yaro na Ɗayyaba mai naira bai nan?
–
Garba Ciyaman ya zo,
An ce yana cikin taron nan yara.
–
Ya Bismillah Allah,
Kare mu kan sharrin maƙiyan mu, amin.
–
Ka dubi inda su Rimi
Giwa ɗiyan Sa’a da Sa’idu bai nan.
–
Ga Surajo nan ya zauna,
Shi kau Surajo ɗan sanda ne ga shi.
–
Ga Surajo nan mai waƙa,
Ga kuma Surajo ɗan sandan mu zaune.
–
Ai maza irin gujiya ne:
Sai an fasa a san mai ƙwara.
–
An ce ba ni farauta,
Wannan maganganun banza ne yara.
–
Yara ina kan aiki,
Ko gobe ma a koma daji!
–
Yara ina bisa aikin,
Ko gobe ma a koma daji, ga ni!
–
Da na tuno da farauta,
Dajin Maraɗi an kwakyara yara!
–
Wani tsoho ya buga gora,
Mamman Surajo sai na caɓo ta!
–
Ya ɗauki babbar gora,
Wai ‘Mai Hawainiya’ yaj jehwa.
–
Tun kan in yi in duƙa,
Nan har ta samu Audussalamu.
–
Ko da ta samo yaron nan,
Sai na hangi ya ɓaci.
–
Na ga jini ya ɓullo,
Wai ga ya nan saman rigash shi.
–
Na ce, “Tsoho ka sake ni,”
Amma wurin ana da bala’i yanzu.
–
Akwai wani dogon yaro,
Ya ɗauki ‘yat takobi tashi, ga ni.
–
Da shi da takobin tashi,
Na rungume su na kai geza!
–
Lokacin da na tashi,
Mamman Surajo da – Kai!
–
Yanzu abin yai sanyi,
Ai ga ni nan ina yin waƙa.
–
* ALHAJI SURAJO MAI-ASHARALLE, Farautan Katsina (Waƙar Mamman Ɗanfagge)
