• About
  • Contact
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

BASHIR YAHUZA MALUMFASHI by BASHIR YAHUZA MALUMFASHI
June 21, 2019
in Da Hausa
0
Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata
Ibrahim Sheme da littafin sa na 'Shata Ikon Allah!'

Ibrahim Sheme da littafin sa na 'Shata Ikon Allah!'

Aminiya ta gana da marubuci, mawallafi kuma ƙwararren ɗan jarida, Daraktan Watsa Labarai na Buɗaɗɗiyar Jami’ar Najeriya (NOUN) da ke Abuja, Malam Ibrahim Sheme, wanda Shata ya ba amincewar ya rubuta tarihin rayuwarsa. Sheme ya bayyana wasu daga cikin muhimman al’amura da suka faru a shekara 20 bayan rasuwar Alhaji (Dokta) Mamman Shata Katsina: 

 

AMINIYA: Malam Ibrahim, ko za ka bayyana yanayin da Shata ya rasu?

SHEME: Ƙarfe 12:00 na dare ya gota da kusan rabin awa a wani ɗaki da ke cikin Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano, inda Shata ke kwance; minti kaɗan kafin lokacin, ’yar sa Jamila da ke jinyar sa tana zaune a kan kujera a gefen gadon, gyangyaɗi na ɗibar ta. Ganin haka, sai ma’aikacin jinya da ke kula da shi, mai suna Malam Umar Ali Dodo, ya ce mata, “Idan barci kike ji, ga ɗaki can ki je ki kwanta zuwa wani lokaci.” Ta miƙe za ta fita daga ɗakin kenan, sai ta ga ya kama mahaifin ta, ya juya shi a hankali. Tana fita, a daidai ƙarfe 12:30 na wannan dare, sai Allah Ya yi wa mahaifin nata cikawa. Allahu Akbar! Rana ta faɗi a rayuwar mawaƙin da babu kamar sa a ƙasar Hausa.

AMINIYA: Shata yana da shekara nawa a duniya ya rasu?

SHEME: Alhaji (Dakta) Mamman Shata Katsina ya rasu yana da kimanin shekara 76 a duniya. A ranar da ya rasu aka yi masa jana’iza a Daura, inda ’yar sa Jamila ta kai shi domin a yi masa sutura kuma ta yi haka ne ba domin ya yi wasiyyar a rufe shi a can ba maimakon Funtuwa ko Musawa, sai don ganin cewa can ne garin babban masoyin sa, ubangidan sa, wato Sarkin Daura a lokacin, Alhaji Muhammadu Bashar. Ranar Juma’a ce, 18 ga Yuni, 1999, wadda a Talatar da ta gabata ta yi daidai da shekara 20 da rasuwar sa.

AMINIYA: Me za ka ce game da yanayin waƙar Shata?

SHEME: Ba zan cika ku da tarihin Shata ba, domin kusan kowa ya san wannan. Illa iyaka in ce a rayuwar sa, Shata ya yi wa kusan kowane abu da aka sani a ƙasar Hausa waƙa ko ya ambace shi a waƙa, mai rai da mara rai, har ma da abin da ya shafi addini kamar Allah da Manzon Sa da shaihunnai. Waƙa a wajen Shata ba ta da gefe, don haka ba za mu iyakance ta ba.

Saboda gudunmawar da ya bayar ga cigaban ƙasa ne aka karrama shi a lokuta daban-daban. Misali, tun lokacin da yake raye Ƙungiyar Mawaƙa ta Nijeriya (PMAN) ta taɓa ba shi lambar girma; haka ita ma Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Kaduna a da, da kuma Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, wadda ta ba shi kyautar Digirin Dakta a 1988. Amma fa babbar karramawa babu kamar irin soyayyar da masu saurare ke masa har zuwa yau ɗin nan. Da wuya ka samu mawaƙin Hausa wanda mutane suka ci gaba da son sa shekaru masu ɗimbin yawa bayan mutuwar sa kamar Shata.

Wani abin sha’awa kuma shi ne yadda aka samu ɗimbin sababbin masoya waƙoƙin sa, matasa, duk da yake mun shigo zamanin da ake gurɓata al’adun mu na gargajiya da wasu baƙin al’adu daga ƙasashe masu nisa da baƙin al’ummomi da ke kusa. Wannan shaida ce da ke nuna cewa lallai mutanen yau da na gobe za su ci gaba da son Shata ko da kuwa ba su taɓa rayuwa a lokacin da shi ya rayu ba.

AMINIYA: A matsayin ka na marubucin littafin tarihin Shata, ko za ka bayyana wasu abubuwa da suka biyo bayan rasuwar sa shekara 20 baya?

SHEME: Na farkon su shi ne rabon gado kamar yadda shari’a ta tanada. An yi hakan ne jim kaɗan bayan rasuwar Shata. Sarkin Daura na lokacin, marigayi Alhaji Muhammadu Bashar, shi ne ya kafa kwamitin da ya yi bincike, ya tara bayanai kan abin da Shata ya bari kuma ya raba gadon ga magada.

To amma kamar yadda na bayyana a littafi na, Shata bai bar wasu miliyoyin naira ba kamar yadda waɗansu ke zato. Dalili shi ne shi mutum ne wanda bai tara dukiya don ta taru ba, shi duk abin da ya samu rabarwa ya riƙa yi ga mabuƙata. Duk wanda ya zo neman agaji a wajen sa, zai ɗauka ya ba shi. Hasali ma dai, ba kowa ba ne ya san cewa Shata ya biya wa ɗimbin jama’a kujerar Makka, kuma ya saya wa waɗansu ragon suna, ya yi wa waɗansu aure, ya biya wa waɗansu kuɗin haya ko kuɗin magani, da sauran su. Sannan ya kula da iyalin sa sosai. Don haka, ba abin mamaki ba ne lokacin da ya rasu aka ga asusun sa babu nauyi duk da yake ya samu ɗimbin kyaututtuka na kuɗi da na dukiya kuma ya yi kasuwanci da noma da siyasa.

AMINIYA: Ko yaya batun littafin sa da kai da waɗansu ku ka rubuta?

SHEME: An ƙaddamar da littafin da shi ya ba da amincewar a rubuta kan tarihin rayuwar sa a cikin watan Yuli, 2006 a Kaduna. Mun so mu kammala littafin tun yana da rai, amma hakan ba ta samu ba. Duk da makarar da muka yi, ya kasance littafi na farko da ya taskace tarihin sa da zurfi kuma zai kasance babban kundin dubawa a wannan fanni. A ƙarshen bara, mun sake fito da sabon bugu na littafin wanda tsarin sa da abin da ya ƙunsa suka fi na farkon inganci.

Marigayi Mamman Shata da yaran sa a bakin sana’ar sa

A watan Yuni, 2013, ni da waɗansu masoyan Shata da waɗansu daga cikin ’ya’yan sa muka haɗu a Gidan Arewa da ke Kaduna, muka kafa Ƙungiyar Tunawa da Mamman Shata. A jawabin da na gabatar a taron, wanda ya zo daidai da shekara 14 da rasuwar Shata, na nuna buƙatar da ke akwai ta kafa “Cibiyar Mamman Shata” ko “Cibiyar Kaɗe-kaɗe Da Waƙe-waƙe ta Mamman Shata” wadda aikin ta ya haɗa da tattaro duk wani abin tarihi na makaɗan Hausa, irin su duk wata waƙa da aka yi da harshen Hausa da aka ɗauka domin a taskace su don kada tarihi ya shafe su. Na nuna cewar waƙoƙin Hausa na da – irin na su Shata, Narambaɗa, Caji, Doka, Uwaliya, Barmani, Uji, Ɗanmaraya, Surajo Mai Asharalle, Ɗanbade da sauran su – da kuma na zamani – irin na su Sani Danja, Aminu Ala, Yakubu Muhammad, Fati Nijar, Fantimoti, Zango, Sharifai da sauran su – suna cikin haɗarin ɓacewa wata rana. Ban ce duk ba, amma ya kamata a adana da yawan su saboda ’yan baya su same su. Kada mu zauna mu zura ido har al’amuran rayuwa da ke rincaɓewa su ɓatar da su.

AMINIYA: Yaya yanayin waƙoƙin Shata a cikin waɗannan shekaru 20 da rasuwar sa?

SHEME: Bayan rasuwar Shata kuma an samar da waƙoƙin sa a matsayin sautin kiran wayar hannu, wato ‘ring tones’. Kamfanin MTN ne ke tallata waƙoƙin, waɗanda jama’a kan biya ’yan kuɗi domin a ji su idan an kira su a waya. Ana ba iyalin Shata ɗan hasafi daga cikin kuɗin, koda yake ba kowa ba ne ya san yarjejeniyar da aka yi da kamfanin. Abu mai muhimmanci dai, a gani na, shi ne ana jin waƙoƙin Shata a bisa wannan tsarin fiye da na kowane mawaƙin gargajiya.

Bayan haka, an ƙara karrama Shata bayan rasuwar sa. Gwamnatin Tarayya ce ta fara yin hakan a ranar 28 ga Fabrairu, 2014 lokacin da ta ba shi kyautar karramawa a matsayin ɗaya daga cikin “manyan masu basira, marubuta da ’yan jarida da duniya ta san da su.” A bikin, wanda aka kira “Centenary Awards,” wanda aka gudanar a cikin Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Shugaba Goodluck Jonathan da hannun sa ya miƙa kyautar ga iyalin Shata. Ban da Shata, shahararren mawaƙin nan Fela Anikulapo-Kuti kaɗai ne mawaƙin da shi ma aka karrama shi a bikin.

AMINIYA: Bayan wannan ko akwai wata kyautar da ya samu bayan rasuwar sa?

SHEME: Wata kyautar da aka ba shi bayan ya rasu ita ce wadda Gidan Rediyon Jihar Kaduna ya ba shi. A lokacin, gidan rediyon ya yi bikin murnar dawo da matsakaicin zangon sa ne. Gwamna Mukhtar Ramalan Yero da hannun sa ya miƙa kyautar ga iyalin Shata. An ba da irin wannan karramawar ga Ɗanmaraya Jos, wanda ya halarci bikin. Hasali ma dai, ba a daɗe da wannan taron ba Ɗanmaraya ya rasu sakamakon rashin lafiya.

Bayan rasuwar Shata, an samu ƙarin masu amfani da Intanet a Nijeriya, musamman matasa. Hakan ya haifar da ƙaruwar sababbin masoyan Shata ta hanyar zaurukan tattaunawa a Facebook da kuma WhatsApp. Ta hanyar soshiyal midiya, akan samu waƙoƙin Shata na ji da na gani a YouTube da sauran wurare. Daɗin abin shi ne ba waƙoƙi na ji kaɗai ba, har ma na kallo akan yaɗa su a waɗannan kafafe. Sannan ƙarin daɗin shi ne za ka iya tura waƙa ta tafi nisan duniya, ta iske miliyoyin mutane kuma duk a kyauta. Ni ne mutum na biyu da ya buɗe zauren Shata a Facebook, mai suna ‘Dandalin Mamman Shata’, wanda a bara na sauya masa suna zuwa ‘Shata Ikon Allah!’ don ya yi daidai da sunan littafin mu.

AMINIYA: Ko akwai wanda ya gaje shi cikin ’ya’yan sa?

SHEME: A zamanin sa, Shata ya hana duk wani ɗa nasa ya gaje shi a wajen waƙa. Ya fi son su yi makaranta. Dalili shi ne ya lura da ɗimbin alfanun karatun zamani ga mutum da kuma al’umma baki ɗaya, musamman idan ya tuno da yadda waɗansu suka riƙa yi masa kallon raini saboda wai shi “maroƙi” ne. Lokacin da babban ɗan sa Lawal (Magaji) ya fara waƙa, uban bai so ba. To, bayan rasuwar Shata, ɗan sa Sanusi ya shiga harkar waƙa a cikin 2014 a matsayin ‘Halifan Shata.’ Yanzu haka Sanusi ya na bakin ƙoƙarin sa a fagen waƙa.

Haka kuma mutuwa ta ratsa gidan Shata har sau uku bayan rasuwar sa. Na farko shi ne ɗan sa Nura, wanda ya rasu a watan Maris, 2016 yana da shekara 41. Na biyu, mutuwa ta ɗauki uwargidan Shata, wato Hajiya Furera, bayan wata ɗaya. Shekarun ta 58. Na uku ɗan ta, Mamuda, ya rasu watanni 14 cur da rasuwar ta, a shekarar 2017.

AMINIYA: Daga ƙarshe, me za ka ƙarƙare da shi?

SHEME: Zan kammala da cewa dukkan abubuwan nan da suka faru bayan rasuwar Shata, manyan darussa ne ga kowa. Shata dai ya ba da muhimmiyar gudunmawa ga al’umma kuma an gode. Har yanzu ban ji wanda ya ce Shata ba mutumin kirki ba ne. Kuma farin jinin sa bai ragu ba. Kowa na so ya ji muryar sa ko ya gan shi a bidiyo. Hasali ma dai, a bara barar nan, an ji Shehu Ɗahiru Usman Bauchi na bayyana shi a matsayin “ɗan Aljanna.”

* An ciro daga cikin jaridar Aminiya

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: mamman shatatarihi
Previous Post

Cikar Shata shekara 20 da rasuwa

Next Post

Apollo 11 Da Mawaƙan Hausa: Bayan Shekara 50

Next Post
Mamman Shata a gaban kumbon Apollo

Apollo 11 Da Mawaƙan Hausa: Bayan Shekara 50

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100
  • Wanda Ba Ya Fushi Da Yin Allah

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
 

Loading Comments...
 

    %d