• About
  • Contact
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Apollo 11 Da Mawaƙan Hausa: Bayan Shekara 50

by IBRAHIM SHEME
July 21, 2019
0
Mamman Shata a gaban kumbon Apollo
Mamman Shata a gaban kumbon Apollo

Mamman Shata a gaban kumbon Apollo

0
SHARES
17
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

A jiya Asabar aka cika shekara 50 da zuwa duniyar wata da ɗan’adam ya fara yi. Kumbon Apollo 11 mallakar ƙasar Amurka ya sauka a kan farin wata a ranar 20 ga Yuli, 1969.

Na ga tashoshin talbijin irin su BBC World da CNN suna gabatar da shirye-shirye a kan cika shekara hamsin da zuwa kan wata.

Tun a wancan lokacin, mawaƙan Hausa sun shiga cikin ruguntsimin maganganun da aka dinga yi kan wannan al’amari. Na farko shi ne Alhaji Mamman Shata, wanda ya shirya waƙar nan ta “Kumbo Apollo Eleven” inda ya yabi wannan nasara da ƙasar Amurka ta samu. Waƙar ta nuna cewa lallai Shata yana “tafiya daidai zamani”, wanda hakan ne ya sa zaren sa bai tsinke ba.

Na biyu, idan kun tuna, shahararren mawaƙin nan ɗan ƙasar Nijar, marigayi Alhaji Muhammadu Gawo Filinge, shi ma ya yi waƙa kan zuwa duniyar wata da ma binciken sararin samaniya da Amurka da Rasha ke tseren yi a lokacin. Waƙar sa, wadda raddi ce ya yi wa Shata, amshin ta shi ne, “Ya Rabbi Sarki Mai Juma’a, Taimakan Mu Don Ranar Juma’a”. Dalilin waƙar shi ne kasa zuwa duniya da kumbon Apollo 13 ya yi saboda bayan an harba shi a ranar 11 ga Afrilu, 1970, tilas ya juyo ya dawo gida bayan kwana shida saboda fashewar da takin iskar oksijin ya yi a jirgin. Hakan ya faru ne watanni tara bayan nasarar Apollo 11. Gawo Filinge na ganin cewar ai ga irin ta nan, Allah ya hana su yi masa kutse a cikin sirrikan sa. A waƙar da ya yi, Filinge ya soki lamirin zuwa duniyar wata da sauran wurare da Allah ya girke a sama. A ganin sa, kamata ya yi ɗan’adam ya zauna a inda Allah ya aje shi, ya daina karambanin shiga cikin sararin samaniya.

Alhaji Muhammadu Gawo FIlinge yana waƙa

Amma Shata ne ya ci gari a wannan saɓanin ra’ayi na mawaƙan, domin kuwa masana kimiyya a ƙasashe da dama sun ci gaba da zurfafa bincike kan sama’u domin ƙara fahimtar yadda take.

Lokacin da su Alhaji Shata suka ziyarci Amurka a watan Mayu na shekarar 1989, sai da aka kai su wajen wannan kumbo ɗin na Apollo 11, suka gan shi, suka taɓa shi da hannun su.

Ga hoton Shata da na Filinge a nan, Shata yana kallon kumbon Apollo 11, na turo su domin tunawa da wannan babbar nasara da ɗan’adam ya samu, da kuma nuni da cewa mawaƙan mu na Hausa sun taskace tarihin wannan hoɓɓasan da Amurka ta yi na harba ‘yan’adam zuwa kan farin wata.

Loading

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading...
Tags: Apollo 11duniyarwatagawofilingemakaɗan Hausamamman shataNASAouterspacespace exploration
Previous Post

Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

Next Post

Kukah and I

Next Post
Kukah and I

Kukah and I

The Life of Bature Gagare (1958-2002), Author of the Novel ‘Ƙarshen Alewa Ƙasa’

The Life of Bature Gagare (1958-2002), Author of the Novel 'Ƙarshen Alewa Ƙasa'

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Tsokaci Kan Waƙar ‘Sarkin Bori Sule’ Ta Alhaji Mamman Shata Katsina
  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran at 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
 

Loading Comments...
 

    %d