• About
  • Contact
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Cikar Shata shekara 20 da rasuwa

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
June 18, 2019
in Da Hausa
0
Cikar Shata shekara 20 da rasuwa
Katin gayyatar taron daren yau

Katin gayyatar taron daren yau

Allahu Akbar! A yau ne Alh. Dakta Mamman Shata Katsina ya cika shekara 20 cur da rasuwa. Abin ba wuya, har an yi shekara ashirin! Allah ya jiƙan Baba Shata, ya yafe kurakuran sa, amin.

A daren yau, domin juyayin wannan ranar, za a yi taro na musamman a Katsina, inda za a yi jawabai tare da bada kyaututtuka. Wata ƙungiya mai zaman kan ta, mai suna Kakaki Unique Awards Limited, ita ce ta shirya taron mai taken “Dr. Mamman Shata Katsina Remembrance Day”, wato Ranar Tunawa Da Dakta Mamman Shata Katsina”.

Can a wani guruf na ci karo da rubutun da wani masoyin Shata, Hussaini Hamisu Maigoro (Dogo), ya yi, inda ya kawo shawarar cewa ya kamata a kafa ƙungiya guda ɗaya domin gabatar da al’amuran da su ka jiɓinci Shata, kama daga tattara waƙoƙin sa da kayan tarihin sa.

Wannan shawara mai kyau ce. To amma ba sabuwa ba ce. Domin kuwa tun a ranar 18 ga Yuni, 2013 (a daidai ranar da Alh. Shata ya cika shekara 14 da rasuwa) aka kafa ƙungiya mai suna Ƙungiyar Tunawa da Dakta Mamman Shata Katsina (“Dr. Mamman Shata Memorial Association”). Ina daga cikin waɗanda su ka kafa ta a Arewa House a Kaduna. Kuma an zaɓa mata shugabanni na wucin-gadi kafin a yi babban taro na ƙasa.

Idan mutum na da kwafen littafin mu na “Shata Ikon Allah!” to ya duba shafi na 884 – 885 da 893 – 896, zai ga tarihi da musabbabin kafa ƙungiyar har da hotuna.

Matsalar abin ita ce akwai wasu waɗanda ke ganin idan ba su ne su ka yi abu ba, to ba za su bi kowa ba ko su ɗauki shawarar kowa ba. Shi kuma abu irin wannan, tilas ne wasu su fara shi, daga nan a ɗora daga inda aka tsaya.

Saboda haka dai in dai ƙungiya ce, to an kafa ta, sai dai ko a farfaɗo da ita, a yi zaɓen shugabanni. Idan kuma irin waɗannan mutanen da na ambata ba su yarda da ƙungiyar da mu ka kashe lokaci da kuɗi mu ka kafa ta ba, to sai su kafa tasu. Mu dai da abin ya rataya a wuyan mu ɗin tun a wancan lokaci, mun riga mun sauke nauyin mu.

Allah ya jiƙan Baba Shata, ya kyautata abin da ya bari, amin.

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: ƙungiyamamman shatamemorial
Previous Post

Taƙaitaccen Tarihin Malam Ibrahim Ɗanmani Caji

Next Post

Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

Next Post
Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100
  • Wanda Ba Ya Fushi Da Yin Allah

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d