• About
  • Contact
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa Waƙa

Kassu Zurmi Kan Nasarar Tinubu A Kotun Ƙoli

by IBRAHIM SHEME
October 26, 2023
0
Kassu Zurmi Kan Nasarar Tinubu A Kotun Ƙoli
0
SHARES
32
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

 

Tankwahau na Remi,

Asiwaju maci-maza, sai mame na Remi,

Na- Sheyi sai dubu ta taru!

Asiwaju ban bar ka gudun maza daji ba!

 

(Dino) yac ce, “Babu komi Sheme,

Yac ce, “Ɓanna ce dai ka ga an hwara ta,

Na lura da kai ido na ƙaiƙal!”

Yac ce, “An hwara, amma ban ga ta ƙare ba.”

 

Nac ce, “Assha! Dino, da wa da wa ak kwance?”

Bai koma tanka man ba.

“Ka ga an buge Kashim?”

Sai yay yi man na bisashe, yag girgiza man kai nai.

“Dino, Ribaɗu sunka sabatta?”

Kuma sai yag gaggaɓan kai nai.

“Kai ko Ganduje na Gwaggo na Gawuna?”

Yab bi yag girgiza man kai nai.

“Asiwaju sunka kashe?”

Yac ce, “Shin Sheme wai had da ba’a?

“Ka san duk ba naku an ka kashe ba.”

 

Nac ce, “Assha! Da wa da wa ak kwance?”

Yac ce, “To na ga Obi kwance.

Hak kau Datti sun sarai.”

Nac ce, “Uban tahiyah hwa?”

“Wane a’ uban tahiyad?”

Nac ce, “Atiku.”

Yac ce, “Ai shi sunka hwara bugewa!”

 

Na Remi sai dubu ta taru!

Asiwaju sai dubu ta taru!

😂

 

(Baddalawa daga waƙar Kassu Zurmi ta Labbo Na-Magaji)

Ga asalin waƙar:

 

Tankwahau na Magaji,

Labbo maci-maza, sai mame na Magaji,

Na Amadu sai dubu ta taru!

Labbo ban bar ka gudun maza daji ba!

 

Yac ce, “Babu komi Kassu,

Yac ce, “Ɓanna ce dai ka ga an hwara ta,

Na lura da kai ido na ƙaiƙal!”

Yac ce, “An hwara, amma ban ga ta ƙare ba.”

 

Nac ce, “Assha! Roƙo, da wa da wa ak kwance?”

Bai koma tanka man ba.

“Ka ga an buge Gandau?

Sai yay yi man na bisashe, yag girgiza man kai nai.

“Roƙo, Dasaƙare sunka sabatta?”

Kuma sai yag gaggaɓan kai nai.

“Kai ko Dutse na Garugaru na Mande?”

Yab bi yag girgiza man kai nai.

“Labbo sunka kashe?”

Yac ce, “Shin Kassu wai had da ba’a?

“Ka san duk ba naku anka kashe ba.”

 

Nac ce, “Assha! Da wa da wa ak kwance?”

Yac ce, “To na ga Arne kwance.

Hak kau Bala sun sarai.”

Nac ce, “Uban tahiyah hwa?”

“Wane a’ uban tahiyad?”

Nac ce, “Sharu.”

Yac ce, “Ai shi sunka hwara bugewa!”

 

Na Amadu sai dubu ta taru!

Labbo sai dubu ta taru!

Loading

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X

Like this:

Like Loading...
Tags: AtikubaddalawaKassu Zurmikiɗin gargajiyaKotun ƘoliPeter ObisatireShari'aTinubutsokanazaɓen 2023
Previous Post

A Bibliophilic Tour

Next Post

From the Atta to the Ohinoyi: A Glimpse of Ebira History

Next Post
From the Atta to the Ohinoyi: A Glimpse of Ebira History

From the Atta to the Ohinoyi: A Glimpse of Ebira History

Marubuta irin su Ibrahim Sheme…

Marubuta irin su Ibrahim Sheme...

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Tsokaci Kan Waƙar ‘Sarkin Bori Sule’ Ta Alhaji Mamman Shata Katsina
  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran at 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d