• About
  • Contact
Monday, June 30, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Kannywood a 2019: Ko ta ina ba daɗi

IBRAHIM SHEME, ISAH BAWA DORO DA ABBA MUHAMMAD by IBRAHIM SHEME, ISAH BAWA DORO DA ABBA MUHAMMAD
January 3, 2020
in Da Hausa
0
Kannywood a 2019: Ko ta ina ba daɗi
Mai shagon finafinai na gyara hajar sa

Mai shagon finafinai na gyara hajar sa

KUSAN a kowace shekara sai harkar shirya finafinan Hausa, wadda aka fi sani da Kannywood, ta rikiɗa kamar hawainiya.

Wani lokacin kuma ta riƙa juyawa kamar ƙosai a tanda; yanzu za a ga ta yi fari, a lokaci guda kuma sai a ga ta koma ja jawur.

Kannywood dai babbar harka ce a arewacin Nijeriya, inda mutane daban-daban su ke kasa hajar su domin sayarwa, ta hanyar baje kolin basirar su.

MATAKAN CIGABA

A cikin shekarar 2019, an samu abubuwa da yawa na cigaba da kuma cibaya, wanda wasu an san su wasu kuma ba kowa ne ya san su ba.

Ɗaya daga cikin cigaban da aka samu shi ne ƙirƙirar sabuwar manhajar sayar da finafinan Hausa a intanet mai suna ‘Northflix’, wadda aka samar domin kasuwancin finafinan Hausa. Manhajar nan ta finafinan Amurka mai suna ‘Netflix’ ce ta bayar da tunanin ƙirƙirar ta.

Manufar manhajar ‘Northflix’ ita ce ta taimaka wa masu shaa’war kallon finafinan Hausa da ke zaune a ƙasashen ƙetare da ma na Nijeriya, waɗanda idan fim ya fita kasuwa su kan daɗe kafin su same shi, su samu sauƙin samun finafinan a ko’ina mutum yake a faɗin duniya ta hanyar intanet.

Sai dai ga dukkan alamu ita ma manhajar ba ta samu irin karɓuwar da aka so ba, domin har yanzu ba kowa ya san ta ba, sannan ba ko wane mai shirya fim ba ne ya ke bayar da sababbin finafinan sa a ɗora a kan ta ba. Bugu da ƙari, su kan su masu ita sun yi ƙarancin talla tare da wayar da kan mutane a kan yadda ya kamata a yi amfani da manhajar.

Cigaba na biyu da aka samu shi ne bayyanar gagarumin gyaran da aka samu wajen ƙoƙarin tantance duk wani ɗan fim ko ‘yar fim da ake nuna fuskokin su a cikin fim saboda a san asalin kowa domin samar masu da tarbiyya. Tuni Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta fara aikin tantancewar.

A da, Kannywood ta zama tamkar kasuwar daji wadda kowa zai iya shiga ba tare da an tantance sahihancin halayyar sa ko inda ya fito ba.

Ko da yake ita ma tantancewar ta bar baya da ƙura, inda wasu sun je an tantance su, wasu kuwa sun bayyana cewa babu wanda ya isa ya tantance su in dai ba aiki zai ba su ba. Wasu na cewa wannan aikin ba hurumin hukumar ba ne.

Fitattun jarumai mata a bikin taya Hafsat Idris murnar zagayowar ranar haihuwar ta

Akwai ma masu ganin cewa saboda ‘yan Kannywood waɗanda su ka yi jam’iyyar PDP ya sa aka ƙirƙiri aikin tantancewar don a samu damar taka duk wanda ya karya doka.

Sai dai hukumar ta yi iƙirarin sanya ƙafar wando ɗaya da duk wani ɗan fim tun daga kan masu rubuta labarin fim har zuwa masu tace shi, in dai har ba su je sun yi rajista ba.

A gefe ɗaya kuma akwai waɗanda ke ganin kawai salo ne na neman kuɗi hukumar ta fito da shi, saboda yanzu an daina yawan finafinai barkatai wanda su ne hukumar ta dogara da su wurin samun kuɗin shiga, shi ne su ka ɓullo da yin rajista.

Cigaba na uku da aka samu shi ne yadda ake ta fafutikar neman ilimin harkar, tare da mayar da harkar zuwa yanar gizo, wato “online”.

A yanzu haka kusan kashi 80 cikin ɗari na ‘yan Kannywood za ka same su da shafin YouTube inda su ke ɗora mabambantan shirye-shiryen da su ka yi na baya da kuma sababbin da su ka yi.
Bugu da ƙari, wasu daga cikin su sun zage dantse wurin fafutikar neman ilimin harkar ta hanyar halartar makarantun Nijeriya da kuma na ƙasashen waje, gami da taron bita da kuma ƙara wa juna sani irin wanda ake gayyatar takwarorin su na kudancin Nijeriya.

Cigaba na huɗu da aka samu shi ne ƙoƙarin yin wani kasuwancin na daban da ‘yan Kannywood su ka zage dantse a wannan shekarar. Sanin kowa ne cewa yawancin jarumai sun dogara da fim ɗin Hausa kaɗai ne, ba su da wani kasuwancin na daban. Amma a shekarar 2019 jarumai da dama sun buɗe shaguna: misali, Ali Nuhu da Adam A. Zango kowanne ya buɗe shagon sayar da kayan sawa na zamani; Sani Danja da Yakubu Muhammad sun buɗe gidan ɗaukar hoto; Maryam Isah Abubakar (Ceeter) da Maryam Yahya da Samira Saje kowacce ta buɗe shagon gyaran gashi da sayar da jakunkuna da takalma da sauran kayan mata; Muhibbat Abdulsalam na sayar da man shafawa da magungunan gyaran fata, a yayin da kwanan nan Rahama Sadau ta buɗe katafaren gidan sayar da abinci da sashen yin kwalliya.

“Kasuwar finafinan Nijeriya”

CIBAYA

Wasu manyan matsaloli da Kannywood ta fuskanta a cikin 2019, waɗanda kuma aka yi ittifaƙin za ta ci gaba da fuskanta a shekara mai kamawa, sun sa ana ganin kamar cigaban mai ginar rijiya aka samu a wannan shekarar da ke shuɗewa.

Da yawa ana ganin cewa 2019 ita ce shekara mafi koma-baya da ‘yan Kannywood su ka tsinci kan su a ciki, sakamakon durƙushewar da kasuwancin finafinai ya riska. Babbar matsalar da masu shirya finafinan Hausa su ke fuskanta ita ce ta durƙushewar kasuwanci, sakamakon dogaro da su ka yi da kasuwar sidi ta Ƙofar Wambai a garin Kano, wadda ita ce babbar kasuwar hada-hadar finafinan.

Mujallar Fim, wadda ita ce kan gaba wajen bada labaran industirin finafinan, ta daɗe ta na jan hankalin masu shirya finafinai da su lura da cewa kasuwar sidi ta Ƙofar Wambai ta na kakarin mutuwa, amma sai wasu daga cikin ‘yan fim ɗin su ka ɗauki abin kamar almara. Sai a yanzu su ka fahimci hasashen da aka yi ya tabbata.

In ban da Kannywood, duk duniya babu inda ake sakin finafinai barkatai. An yi lokacin da sai a saki sama da guda 40 cikin mako biyu. Haka kuma idan ka kalle su za ka ga duk kusan labarai iri ɗaya ne, kuma jaruman iri ɗaya ne. Idan Ali Nuhu da Jamila Nagudu ne a cikin fim ɗin wane, to shi ma wancan in ya tashi shirya fim su zai saka saboda wai su ake tashe. Da haka aka gundiri ‘yan kallo, su ka riƙa ja baya da sayen finafinan. Wannan ya na ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa kasuwar ta mutu.

Jigon finafinan ma ya zo ya riƙa yin kama da juna. A Kannywood ne idan furodusa ɗaya ya yi fim a kan kishi ya samu karɓuwa, to sai a samu aƙalla mutum goma da za su yi makamancin sa; sun kasa buɗe ƙwaƙwalwar su ta yadda za su taɓo abin da ya shafi Malam Bahaushe.

Kullum dai labarin soyayya ko aure ne, sai lafta rawa da waƙa a ciki! Ta haka aka riƙa bai wa jaruman laƙabi, a ce wance ta fi dacewa da jigon mugunta, wane ya fi iya fim na soyayya, wance kuma gwanar kisisina ce, wane kuma gwanin rawa ne. Hakan ya sa da an ga fostar fim da hotunan wane da wane, to an san inda labarin ya dosa.

Amma duk da haka, za ku ga finafinai masu dogon zango (wato ‘series’) irin su ‘Daɗin Kowa’, ‘Kwana Casa’in’ da kuma ‘Gidan Badamasi’ da ake nunawa a talbijin sun samu karɓuwa a wurin mutane saboda bambance-bambance da ke tsakanin su da irin finafinan da aka saba kaiwa a kasuwar sidi ta Ƙofar Wambai.

Darakta Falalu Ɗorayi (sanye da haɓar kada) na bada umurni a wurin ɗaukar wani fim

Sai dai wasu na ganin wannan yanayin na taɓarɓarewar kasuwancin fim da masu harkar su ka tsinci kan su a ciki lokaci ne ya zo da masana’antar za ta yi tankaɗe da rairaya inda za ta wankacalar da wasu jaruman da daraktoci har ma da furodusoshi da duk wanda ya ƙi tafiya daidai da zamani.

Tun a yanzu ma ta fara wankacalar da wasu furodusoshin idan aka yi la’akari da cewa an rage yawan fita aikin fim. A yanzu in ban da irin su Abubakar Bashir Abdulkareem, wanda aka fi sani da Maishadda, da irin su Naziru Ɗanhajiya, ba kowa ne ke iya fita lokeshin ba. Tuni dai gwiwoyin wasu daga cikin masu harkar fim su ka yi sanyi, kuma sun shiga tsaka mai wuya.

Saboda idan sun yi fim ɗin ma babu yadda za su yi da shi. A ƙa’ida, duk bayan sati biyu ya kamata a saki finafinai 12, amma yanzu sai a kai wata biyu ba a saki fim 10 ba. Akwai ma makwannin da su ka zo su ka wuce ko fim ɗaya ba a saki ba. Hakan kuma ya kan shafi ‘yan wasan, waɗanda da yawan su fatara ta addabe su. Wasu sun fara neman wasu hanyoyin na neman abinci. Babban misali shi ne Adam A. Zango, wanda kwanan nan ya bayyana cewa shi fa ya koma Legas da zama don ya riƙa halartar bukukuwan ‘yan Arewa mazauna kudu, ya na samun kuɗi.

Akwai kuma masu ganin zamani ne kawai ya durƙusar da kasuwar sidi, saboda a yanzu za ka iya shiga gida goma ba ka samu uku masu na’urar sidi ba; kowa tauraron ɗan’adam ya ke amfani da shi.

A wani ƙwaƙƙwaran bincike da mu ka yi, mun gano cewa a yanzu haka ba a iya buga kwafen sidi sama da dubu biyar a fitar da shi kasuwa. Ko an buga su ɗin ma sai an maido maka da ragowa da yawa. Hakan ya sa furodusoshi da yawa sun kasa ba ‘yan kasuwa finafinan su.

Akwai ma wani da ya tabbatar mana da cewa yanzu duk kyan fim a Kasuwar Ƙofar Wambai bai wuce a saye shi N100,000 ba, ko nawa ka kashe wurin buga shi.

Bikin ƙulla yarjejeniyar talla tsakanin Ali Nuhu da kamfanin wasu Indiyawa

Fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Adam A. Zango, Sadiq Sani Sadiq, Sani Danja da sauran su kowannen su ya na da sabon fim a ƙasa, amma sun kasa fitar da shi kasuwa saboda tsoron asarar da za su yi, da tunanin maƙudan kuɗaɗen da su ka narkar wurin shirya finafinan.

Ali Nuhu ya na da ‘Kar Ki Manta Da Ni’, Adam A. Zango ya na da finafinai irin su ‘Gwaska Return’, ‘Gudun Mutuwa’, ‘Haseena’ da ‘Ramakon Gayya’; Sani Danja na da ‘Akeelah’, Sadiq Sani Sadiq da Rahama Sadau su na da ‘Mati A Zazzau’. Duk wanda ka tunkara a Kannywood zai ce maka ya na da fim a ƙasa, amma tsoron yadda kasuwar ta koma ya hana shi fitarwa.

Kuma a wani ɓangaren na sayar da fim, samuwar gidajen talbijin irin su Arewa24 da Farin Wata da African Magic Hausa ta haifar da koma-baya ba kaɗan ba. Domin a shekarun baya gidajen talbijin da ke sayen fim su kan saya da tsada. Amma saboda son zuciyar wasu daga cikin ‘yan Kannywood su ka lalata harkar, inda su ka rinƙa bi su na karɓar finafinan mutane su na sayarwa da tsada sai kuma su ba masu finafinan kuɗi kaɗan.

Su kuma gidajen talbijin ɗin da su ka gane, sai su ka daina sayen finafinan da daraja. Wannan ya ƙara taɓa harkar fim ta kowane ɓangare.

Su ma ‘yan kallo, sai su ka gwammace su kalli finafinan da waɗannan tashoshin ke haskawa, maimakon su je kasuwa su sawo fayafayen sidi su kawo gida. Yanzu ba kowa ba ne ke saya wa iyalin sa fim, sai ya ce kawai su kalla a talbijin.

A ɓangaren gidajen sinima kuwa, bayan hankalin ‘yan Kannywood ya dawo jikin su, su ka fahimci cewa kasuwar sidi ta mutu, sai su ka rinƙa yin kwambar kai finafinan su gidan kallo na Film House Cinema da ke cikin cibiyar hada-hada ta Ado Bayero Mall, a Kano.

Adam A. Zango

Shekara biyu da su ka gabata lokacin mutane na ɗokin abin, an samu finafinai waɗanda aka yi tururuwar kallo irin su ‘Kalan Dangi’, ‘Mariya’, ‘Mansoor’, ‘Rariya’, da ‘Gwaska Return’. A lokacin, akan ɗauki tsawon kokaci kafin a haska fim, wanda hakan ya sa duk lokacin da aka tashi nuna fim sai mutane sun yi dandazo wurin kallon shi.

Amma a shekarar 2019, mun ga abin ya canza zani, domin kuwa an samu ƙarancin masu kallo; kusan duk sati sai an kai sabon fim, amma a satin idan mutum ya lissafa bai samun mutum 500 da su ka shiga.

Sai furodusa ya yi sa’ar gaske kafin ya samu kuɗin da su ka kai N200,000. Idan kuma aka gama kallon shi a can sai dai ka zuba masa ido domin babu wurin kai shi, ko da yake an samu waɗanda su ka haska finafinan su a lokacin bikin Babbar Sallah a Kaduna da Katsina, amma su ɗin ma babu wanda ya samu sama da naira dubu ɗari.

KALLO YA KOMA SAMA

A yanzu dai haka kasuwancin finafinan Hausa ya yi mutuwar kasko, kuma ba a san lokacin gyara shi ba. Kusan a ce harkar ta mutu murus, kuma har yanzu an kasa gano hanya mai ɓullewa.

A shekarar 2020, ana sa ran a ga abin da shugabannin Kannywood za su yi domin ceto sana’ar. Jama’a sun zuba ido su ga abin da Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato MOPPAN, za ta yi.

Kwanan baya dai aka zaɓi sababbin shugabannin ƙungiyar, da Dakta Ahmed Sarari a matsayin shugaba. Sarari ya ci zaɓe ne bisa alƙawarin zai gyara kasuwancin finafinai. To yanzu kallo ya koma kan sa, ana jiran a ga da wacce ya zo. Wasu na cewa Allah ya sa dai duk kanwar ba ja ba ce!

* An ciro daga gidan yanar BBC Hausa

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: finafinan HausaKannywoodKanokasuwanciKasuwar Ƙofar Wambaimatsaloli
Previous Post

Ɗanmaraya a London

Next Post

How My Friend’s Soldier Son Was Killed

Next Post
The late Usama Saminu

How My Friend's Soldier Son Was Killed

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Goron Sallah
  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
 

Loading Comments...
 

    %d