• About
  • Contact
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Balaguro A Isra’ila Da Palasɗinu

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
October 21, 2023
in Da Hausa
0
Balaguro A Isra’ila Da Palasɗinu
Bangon littafin

Bangon littafin

Littafi: Ilmi Mabuɗin Tafiya: Balaguro a Isra’ila da Palasɗinu
Marubuci: Ibrahim Sheme
Kamfani: Informart, Kaduna
Shekara: 2005
Shafuka: 112

Jiya a Facebook na ga shugabar ƙungiyar mu ta marubuta, Alƙalam, Hajiya Halima K Mashi , ta saka hoton bangon wani littafi da na rubuta mai suna ‘Ilmi Mabuɗin Tafiya: Balaguro A Isra’ila Da Palasɗinu’.

Wannan littafi an buga shi da Hausa a cikin 2005, to amma sai da aka fara wallafa shi da Turanci, mako-mako, a cikin jaridar New Nigerian Weekly a farkon shekara ta 1999.

Ya na ɗauke da labarin ziyarar da na kai ƙasar Isra’ila da yankunan Falasɗinawa waɗanda Yahudawa su ka danne da nufin ƙwace su baki ɗaya. Na kai ziyarar ne a cikin Disamba 1998 tare da wasu editocin jaridun Nijeriya guda shida da wani jami’in Ofishin Jakadancin Isra’ila a Legas (mu biyu ne Musulmi).

A balaguron, mun je wuraren tarihi waɗanda ban taɓa tunanin ƙafa ta za ta iya takawa ba, mun ga abubuwan mamaki, kuma mun tattauna da manyan jami’an gwamnati na ɓangarorin Isra’ila da Falasɗinu, da ‘yan kasuwa, ‘yan jarida, sojoji, ɗalibai, malaman addini, malaman jami’a, ‘yan siyasa, masu harkar nishaɗantarwa, da sauran su.

Wuraren da mu ka je sun haɗa da Masallacin Al-Aƙsa (wanda shi ne wuri na uku mafi tsarki a Musulunci); da ɗakin da aka haifi Annabi Isa (a.s.) da inda ya fara wa’azi da kotun da aka yi masa shari’a da inda Kiristoci ke cewa an gicciye shi (Calvary Hill / Golgotha) da kogon da su ka yi amanna da cewa ya tashi daga matacce (Stone of Anointment); da tsibirin Masada, da tekun Dead Sea, da Jami’ar Hebrew, da gidajen jama’a a ƙauyuka, da birane irin su Ƙudus (Jerusalem), Tel Aviv, Haifa, Nazareth, Canaan, Tiberias, Tabgha, da Capharnaum; da Ma’aikatar Tsaro, ma’aikatun gwamnati, Kotun Ƙoli, Tsaunin Hertz (inda aka yi maƙabartar manyan Yahudawa), da gidan tarihin kisan kiyashi na Holocaust (wato Yad Vashem), da wuri mafi tsarki a addinin Yahudawa (Wailing Wall), da hedikwatar addinin Baha’iyanci ta duniya, da babbar majalisar ƙasa (Knesset), da tsaunukan Golan Heights da Isra’ila ta ƙwace daga hannun ƙasar Siriya, da Ofishin Jakadancin Nijeriya, da dai sauran su. Mun je ofishin tsohon Firayim Minista Shimon Perez, mun gana da shi. Shi ma mugun nan, Firayim Minista Benjamin Netanyahu (wanda a yanzu ma shi ke riƙe da muƙamin), mun je ofishin sa domin mu gaisa da shi, to amma mun zauna jira sai ya sulale ta wata ƙofa ya bar mu ya tafi Majalisar Dattawa inda ake turka-turkar tsige shi saboda wata kwaɓa da ya tafka. Can mu ka je mu ka same shi, mu ka sha kallo.

Wannan littafi, mai shafi 112, ya ƙunshi bayanai kan asalin rikicin Falasɗinawa da Yahudawa wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, da al’amurra masu tarin yawa. A yau da azzaluman Isra’ila a ƙarƙashin Netanyahu su ke aiwatar da kisan kiyashi kan Falasɗinawa da ragargaza Birnin Gaza da wasu sassa na Falasɗinu da Lebanon, ina tuno da waɗannan wurare da na ziyarta, ina ganin su a rai na kamar jiya na je cikin su, da abubuwan da na ji daga bakin jama’ar ɓangarorin biyu.

Littafin ya shiga kasuwa a lokacin da ya fito shekaru 18 da su ka shuɗe (bayan an buga shi wata-wata a cikin mujallar Fim) amma wanda na bayar kyauta ya fi wanda na sayar yawa.

Idan mutum na buƙata, zai iya samun shi a waɗannan kantinan sayar da littattafai:

Arewa House Bookshop a Kaduna
2. Chapter One Bookshop da ke Gwammaja, Kano (tsallaken ƙofar shiga Asibitin Ƙashi na Dala)
3. Booksellers da ke Garki, Abuja

Wanda ya ci sa’a kuma, zan ba shi kwafe kyauta!

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Previous Post

Matriculation: Be worthy ambassadors of NOUN, VC tells 18,679 freshmen

Next Post

A Bibliophilic Tour

Next Post
A Bibliophilic Tour

A Bibliophilic Tour

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100
  • Wanda Ba Ya Fushi Da Yin Allah

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d