• About
  • Contact
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Ashe Narambaɗa bai mutu ba!

Wani manazarcin adabin Hausa ya na nan ya duƙufa kan tattara kammalallen tarihi da waƙoƙin ɗaya daga cikin shahararrun makaɗan Hausa, wato marigayi Ibrahim Narambaɗa

Ibrahim Sheme da Ashafa Murnai Barkiya by Ibrahim Sheme da Ashafa Murnai Barkiya
August 29, 2007
in Da Hausa
0

Duk wanda ya san abin da ake kira “waƙar Hausa,” to ya san Makaɗa Ibrahim Narambaɗa. Hasali ma dai akwai muhawara ƙwaƙƙwara kan waye ya fi fasaha tsakanin Narambaɗa da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Narambaɗa yawan waƙoƙi ne kurum amma Narambaɗa ya fi zalaƙa da fasaha, wasu na cewa ai shi Shata ya kere Narambaɗa, musamman da yake shi waƙoƙin sa kowa zai iya fahimtar su – Basakkwace da wanda ba Basakkwace ko Bazamfare ba.

A bara, wasu matasa sun ƙaddamar da kammalallen tarihin Shata, wanda hakan ya ƙara taimakawa wajen fahimtar ko waye mawaƙin. Shi kuwa Narambaɗa, yawancin waɗanda su ka san shi, sanin shanu su ka yi masa. Kuma yawancin Hausawa su kan kasa gane wasu kalamai na waƙoƙin sa, musamman waɗanda ba su fito daga tsohon yankin ƙasar Sakkwato ba. Bugu da ƙari, in ban da taƙaitaccen tarihin sa da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jami’ar Bayero ta Kano ya rubuta a littafin sa ‘Makaɗa Da Mawaƙan Hausa’, ba kowa ba ne zai ce maka ya san tarihin wannan fasihin mawaƙin.

To, yanzu dai an taki sa’a, domin kuwa aiki ya yi nisa wajen tattara kammalallen tarihin Narambaɗa. Kuma sai aikin ya faɗa a hannun ɗan gida, wanda ya san kan al’amarin, wato Farfesa Aliyu Bunza.

Shi dai Farfesa Bunza, fitaccen manazarci ne a ƙasar Hausa. Ya yi rubuce-rubuce kan adabi da kuma al’adun Hausawa, har ma da wasu waƙoƙi na baka da kuma rubutattu. A yanzu shi ne ke rubuta tarihin Makaɗa Narambaɗa.

Shin yaya wannan aiki nasa ya ke ciki? A ranar Lahadi da ta wuce, an yi hira da Farfesa Bunza, wanda babban malami ne a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, a sashen Hausa na gidan rediyon BBC. Wakilan gidan rediyon sun zanta da shi lokacin da ya je London kwanan nan. Mu a nan Leadership Hausa mun kalato maku wasu muhimman bayanai daga cikin wannan zantawa tasu ta musamman kan aikin da ya ke yi na rubuta tarihi da waƙoƙin marigayi Alhaji Ibrahim Narambaɗa.

Tun da farko sun sako waƙar Narambaɗa mai taken, “Masu Gari Mazan Tabas Tsayayye, Sarkin Rwahi Ya Wuce A Ram Mai.” Idan kun tuna, a wannan waƙar ce makaɗin ke cewa, “Ga wani ɗan sarki da kunnuwa da hwaɗi…”

An tambayi Malam Bunza ya faɗi wani abu kan waƙar. Sai ya amsa, “Sarki ne aka wa waƙai na Kuryar Dambo, ba Kurya ta Madaro ba. Ma’ana, Kurya guda biyu mu ke da su a Zamfara: akwai wannan Kurya ta Madaro, akwai waccan Kuryar Dambo. To hakimin Kuryar Dambo ne ya ka wa waƙa. Kuma wannan cewa ‘Da takobi da garkuwa da yaƙi,’ daga cikin ƙa’idar nazarin waƙa, ‘lugude’ mu ke kiran sa – luguden tarihi. Wani tarihi ne ya narke wurin, tarihin wani sarkin ɗan tauri ne da aka yi a Kurya mai suna Mamman Ina, da ya kashe wani Bature. To shi ya sa ya ke cewa ‘Kurya akwai mazan hwaɗa da arna’.”

BBC: Abin da ya sa na yi maka wannan tambaya, a da a Zariya idan mu ka ji wannan waƙa akwai wani gari Kauru a kusa da Zariya, mun ɗauka shi ake wa waƙar da ya ke cewa Makauru. Ashe ba Kauru ba ne. Wai me ake cewa ne a wurin? Ka san wani ɗan sarƙe-sarƙe ne.

BUNZA: Ai da ya ke cewa ya ke yi, “Ai Kurya ta Dambo ta Makauru an nan, / Zamfara babu makaye kama tai.”

BBC: Za mu so ka ɗan ba mu tarihin Narambaɗa, wataƙila mutanen zamani ba su san ko wanene ba.

BUNZA: Marigayi Narambaɗa shahararren mawaƙi ne a duniya. Kuma idan za a yi tarihin Ibrahim Narambaɗa, bisa ƙa’idar ilmi sai an wa mutane da yawa tambaya waɗanda su ka gabace ni a cikin wannan fagen, kamar Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, ya yi bincike musamman a kan Narambaɗa; Bello Sodangi ya yi bincike musamman a kan Narambaɗa; Sama’ila Yawuri Mazawaje shi ma ya yi bincike musamman a kan Narambaɗa.

To, sunan Narambaɗa na yanka Ibrahim. Sunan uban sa Maidangwale, shi kuma Maidangwale mutumin Nijar ne, cikakken ɗan kokawa ne. Amma Narambaɗa ya gaji kiɗi wajen uwar sa. Don haka shi karen makaɗa ne kenan; uban sa bai yi kiɗi ba. An haife shi a garin Tubali, ya yi karatu a nan, ya rayu a nan, ya tashi a matsayin ba ɗan gadon waƙa ba. Ya iske kayan kotson kiɗin kakan sa na wajen uwa a ɗakin mahaifiyar sa. Mahaifin sa mutumin ƙasar Filinge ne, ya zo a garin Tubali, ya auri uwar Narambaɗa. Kuma ga shi shahararren ɗan kokawa ne.

Sai Narambaɗa ya ɗauki kayan kiɗin mahaifin uwar sa ya fara kiɗan noma. To, wata shekara a fadar Sarkin Gobir na Isa ya yi kiɗin noman ƙauyen su. Da jin yadda daɗin waƙa ya ke da zalaƙa da ƙwarewa, su ka ce ya fi ƙarfin ƙauye, sai aka mai da shi birni. Ya tashi daga mawaƙin noma ya koma makaɗin Gobir. Ka ji tarihin zuwan sa.

BBC: Wato wannan ne kenan ya sa ya koma makaɗin na fada, na sarakuna.

BUNZA: Gaba ɗaya saboda an ga hikimar ta hi ƙarhin ta manomi, dole sai an mai da shi fada. Don haka ya dawo ya ci gaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir waƙa.

(BBC sun sako waƙar “Ya Ci Maza Ya Kwan Ya Na Shire, Uban Zakara, Dodo Na Ummaru”)

BBC: To Farfesa Bunza, me za ka ce dangane da wannan waƙa?

BUNZA: Wannan waƙa ta Sarkin Gobir ta na cikin manya-manyan waƙoƙin da ya yi masa. Kuma wannan waƙa ce wasu su ke ganin gabanin Narambaɗa ya yi bakandamiyar waƙar sa. Don a ciki har Narambaɗa na cewa duk abin da zai faɗa ga Sarkin Gobir daidai ne, ba kure ba ne:

“Na aje ƙarya ko ina kiɗi,

Na bar ƙarya ko ina kiɗi,

Nai sittin, saba’in ni ka hwaɗa,

Mai saba’in yai ƙarya ana ta zunɗe nai,

Ko yaran da ag garai duw wawwatse mashi su kai,

Ya na yawo shi ɗai baram-baram.”

Saboda haka, a cikin wannan waƙar ba mu zaton mu ji abin da ya saɓa wa gaskiya. Don haka ne mu ke ganin wannan waƙa ta Sarkin Gobir na cikin manyan waƙoƙin sa. Amma dab baya da yai bakandamiya, sai ta shahe hasken ta.

(BBC sun sako waƙar “Batun Da Akai Na Yau Babu Sarki Yau Irin Ka,/ Jikan Bello Arna Su Na Shakkak Ka”)

BBC: Farfesa, ko wanda bai san Narambada ba ya san mutum ne wanda Allah ya ba basira. To amma kuma kamar yadda kowa ya sani, akwai shahararrun mawaƙa waɗanda su ma sun yi suna. Ko dai kamar Narambaɗan ko kusa da shi. Me ya sa ka ɗauki Narambaɗa a matsayin wanda za ka yi bincike a kai?

BUNZA: Akwai dalilai da yawa. Na farko shi ne, fitattun mawaƙan Hausa da mu ke da su ƙasar Hausa an fara bincike a kan su – ko bincike ne na jami’a, ko ma na gida ne, duk dai an yi. Shata an yi aiki a kan sa. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya yi bincike kan Salihu Jankiɗi. To, na ke ganin a dukkanin ƙasar Zamfara ba a yi mawaƙin da ya kai Narambaɗa ba. Kuma ba a ƙasar sa kawai ya ke waƙa ba. Ma’ana, duk duniyar ƙasar Hausa. Amma abin takaici, idan an zo neman waƙoƙi nai babu, sun wawwatse, ba a samun su. Ba a san tarihin sa ba, ba a san ina ya hito ba, ba a san hikimar sa da zalaƙar sa ba. Sai na ga ya na da kyau a yi wani aiki da aƙalla zai fito da shi, zai fito da falsafar sa, zai fito da waƙoƙin sa, da waɗanda ya yi wa waƙoƙin, shi ma ya kasance wani taska daga cikin taskar adabin Hausa da za a aje.

BBC: Ban tari numfashin ka ba. Wasu kalmomi da Narambaɗa ke amfani da su a cikin waƙoƙin sa, idan ba fassara wa mutum aka yi ba, ba a fahimtar abin da ya ke faɗi. Ina ganin wannan ma ya na da mahimmanci a yi irin wannan bayani da ka yi. To zuwa yanzu ka rubuta waƙoƙin sa guda nawa?

BUNZA: Sai dai in ce na samu waƙoƙi guda nawa? In na samo su sai in rubuta su…

BBC: Ban tari numfashin ka ba, rubutawar ka na rubuta duk abin da aka ce a cikin waƙa?

BUNZA: E, zan yi ƙoƙari duk abin da ya ce, zan yi ƙoƙari in rubuta kuma a irin lafazin da ya faɗa. Kamar Sarkin Rafi, ai Sarkin Rwahi ya ke cewa. Ni ma Rwahi zan rubuta.

BBC: Waƙoƙi nawa ka samu zuwa yanzu?

BUNZA: Wasu su kan ce ya yi waƙoƙi sun kai ɗari ko ɗari da wani abu, amma iyakar binciken da mu ka yi, kusan sama da shekaru ashirin da wani abu, gaskiya ni hamsin na samu, waɗanda na rubuta da kai na, na saurara, na tabbatar sun rubutu, na ajiye.

BBC: Waɗanda aka ɗauke su da faifai kenan?

BUNZA: Ma’ana, shahararrun waƙoƙin da aka sani a kaset, ba dab bakin wani aka ji su aka rubuta ba.

BBC: Dangane da waƙoƙi ko mawaƙan Hausa, kamar Alhaji Mamman Shata ana cewa ya na tsayawa nan take ya yi waƙa, don an sha gwada shi, ba tare da ya zauna ya shirya ta ba. Shin Narambaɗa ya yake tsara waƙoƙin sa?

BUNZA: Wato ko wane irin mawaƙi da irin fasaha da hikima da zalaka da Allah ya hore masa. Allah ya hore masa waƙa, amma shi (Narambaɗa) ba a nan take ya ke yin ta ba. Idan zai yi maka waƙa, zai je gida ya tsara ta; a yinin da zai yi waƙar, ba zai yi hulɗa da kowa ba. Haka wasu yaran sa su ka shaida mana. In ya ƙare tsara ta, sai ya kira yaran sa, sai su rera. Waƙar Narambaɗa in zai yi ta, zuba waƙa ake zube-ban-ƙwarya.

BBC: Kamar yadda ya ce ta Alfazazi…

BUNZA: Cewa ya yi:

“Kullum ji ni kai azanci na hudo min,

Sai zuba waƙa ni kai kama da ta Alfazazi.”

BBC: Rubutawa ya ke yi?

BUNZA: Narambaɗa ba ya rubuta waƙa, sai ya samu gindin waƙa ya fara. Da ya ƙare abi nai cikin zuciya, sai ya kira yara nai ya ce, “To, ga amshin waƙa kaza,” su riƙa yi a sannu ana maimaitawa. Sai ya ƙare sai aje a yi ta.

BBC: Waƙar Alƙali Abu fa? Shin wanene Alƙali Abu ɗin nan?

BUNZA: Alƙali Abu asali mutumin Ƙauran Namoda ne, alƙalanci ya kai shi Moriki, kuma daga cikin ’ya’yan sa akwai wanda ke raye a Sokoto yanzu. Amma dai zuri’ar na can a Ƙaura. Ba Alƙali Abubakar Mahmud Gumi ba ne kamar yadda mutane su ke zato. Ya yi masa wannan waƙa a kan irin adalcin sa, gogewar sa da sanin shari’a.

(BBC sun sako waƙar “Alƙalin Alƙalai Ta Aiki Nai Da Tsari…”)

BBC: To amma akwai inda ya ke cewa “Narambaɗa ba ya zuwa lahira…” Kamar ya bugi ƙirji…

BUNZA: Ya ce ko ya je dawowa ya kai. Ya na da hujja a wannan wurin. Sai an kamo kan waƙar za a gane me ya sa ba zai je lahira ba! Ya ce:

“Hwadawa ku bugan in buge ku

Mui ta faɗan mu gidan duniya,

Kun san ba a hwaɗa lahira,

Kun san ku ka zuwa lahira,

Narambaɗa ba ya zuwa lahira,

Ko ya je dawowa ya kai,

Gama kun san ɗauke mai akai.”

Maganar sa ta tabbata: fadawa ke mutuwa; da bafade ya mutu, a fada an manta da shi. Da Sarki ya mutu, a fada an manta da shi, an yi wani. Amma idan zakaran mawaƙa ya mutu, ba mutuwa ya yi ba. Har yanzu ga Narambaɗa ba shi duniya, ana maganar sa, ana jin maganar sa. Ina fadawa su ke? Saboda haka duk wani mawaƙi da ya san kan sa, ya yi luguden waƙar, to bai mutu ba, ya na nan a raye!

BBC: To, Farfesa Aliyu Bunza, mun gode ƙwarai.

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Tags: adabin Hausabbc hausaFarfesa Aliyu Bunzamamman shataNarambaɗa
Previous Post

GYARAN GANGAR ABZINAWA!

Next Post

Ashe Narambad’a Bai Mutu Ba!

Next Post

Ashe Narambad'a Bai Mutu Ba!

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64
  • Cikar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi shekara 100
  • Wanda Ba Ya Fushi Da Yin Allah

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d