A JIYA, 5 ga Yuni, 2023, marubuciya Hafsat Umar Azare ta wallafa wani saƙo a guruf ɗin WhatsApp mai suna Gidan Marubutan Hausa wanda ya ɗan sosa ran wasu membobi. Ta kawo shawara ne inda ta ce ya kamata marubutan Hausa su yauƙaƙa zumuncin da ke tsakanin su ta hanyar haɗa aure a tsakanin ‘ya’yan su.
Hafsat ta ce: “Don Allah, marubuta ina ba ku shawara in za mu yi hidimar biki ko wani taro mu na zuwa (da) yaran mu samari da ‘yan mata saboda ko za mu dace wajen haɗa zumunci. Abin nufi, mu fara haɗa su aure.
“Sannan ‘yan mata da samari marubuta su ma su yi duba ga wannan su ƙaunaci junan su, in Allah ya shiga lamarin sai su yi aure.
“Ina son mu yi zumunci na har abada. In auratayya ta shigo lalle haɗin kai zai tabbatu sosai. Allah ya sa za ku yi min kyakkyawar fahimta.”
Ta ƙara da cewa ta na da “hujjoji masu ƙarfi”. A yayin da aka fara mara mata baya kan wannan shawara da ta kawo, sai malamar ta jero waɗannan hujjoji da ta ce ta na da su. Ta ce: “Na yi nazarin abubuwa masu yawa. Marubuta mu na son juna. Mu na tare da juna kullum, babu dare ba rana. A zahiri da baɗini.
“Abin da ya tsaya min a rai da zuciya wasu daga cikin mu su na mutuwa, mu na shiga tashin hankali sosai, shekaru kaɗan sai mu manta su saboda ba mu surka dangantakar komai tsakanin mu ba. Dukkannin kusanci da soyayya ya na tashi a banza. Ina takaicin hakan.
“Wannan ya mutu, waccan ta mutu. Wata rana za mu ƙare, yaran mu ba za su san wannan ba. Amma in mu ka daure za mu yi nasarar samun zumunci mai ɗorewa, saboda marubuci mutum ne mai son ɗan’uwan sa. Kuma za a yi gadon fiƙira da hazaƙa sosai.”

Ba na tsammanin ana “gadon fiƙira da hazaƙa,” to amma ba shakka batun zumunci da ɗorewar dangantaka dahir ne. Na jima ban ji wata shawara da aka ba marubutan Hausa mai ma’ana kamar wannan ba.
Zumunci shi ne madarar rayuwa. Ƙulla shi alheri ne, kuma wani ginshiƙi ne na addini. Zumunci ke haifar da ƙauna da haɗin kai da cigaban al’umma da ɗorewar ta. Aure kuwa, jigo ne na zumunci; shararriyar hanya ce da ake bi a yauƙaƙa zumuncin.
Babu mamaki, kowa ya amince da cewa shawarar da Hajiya Hafsat ta kawo mai kyau ce. Ni kuma na ƙara da cewa su ma marubutan, su ya su, ya kamata su riƙa auren junan su, wato bazawara ko budurwa marubuciya ta auri ɗan’uwan ta marubuci.
Tuni ‘yan fim sun daɗe da wuce wannan zangon, wasu har sun hayayyafa. ‘Yan fim da su ka auri juna su na da yawan gaske, amma marubutan da su ka auri juna ba su fi a ƙirga su da tafin hannu biyu ba. Mun san dai soyayya na ratsawa a cikin marubuta, su ya su. Zan iya lissafa biyar. To me ya sa ma’auratan marubuta ba su da yawa kamar ‘yan fim? Ban iya ƙirga uku. Ruwa ba ya tsami banza!
Ba a yanzu aka fara maganar dacewar auren juna tsakanin marubuta ba. Tun a watan Yuni, 2011, mujallar Fim ta wallafa wani rahoto mai taken “Me Ya Sa Marubuta Ba Su Auren Junan Su?” Su marubutan da kan su sun kawo dalilai daban-daban, sai dai ba zan maimaita su a nan ba, to amma zan kawo wani guda ɗaya wanda babu wanda ya faɗe shi a wancan lokacin; na yi la’akari da shi, amma ba na cikin marubutan da mujallar ta tattauna da su domin haɗa rahoton.
Wannan kuwa shi ne aibanta juna. E, ɓata wa juna suna. Ni shaida ne. Na sha ji da kunne na marubuta na aibanta junan su, ban da waje na har wajen wasu makusanta na. Kusan kowace marubuciya sai ka ji an shafa mata baƙin fenti. Su ma mazan haka ake masu, kuma su na yi wa juna.
Idan ka ce ba ka san ana haka ba, to kai ba marubuci ba ne. Idan har kai marubuci ne, to ba za ka rasa jin mugun abin da wani ya ce game da wani marubucin ba – ko da kuwa kai ba ka ce uffan ba. Ba mazan ba, ba matan ba.
Ana aibanta ‘yan mata da zawarawa; ka ji an ce wance kaza, wance ma kaza. Hatta mata masu aure ba a ƙyale su ba wajen irin wannan sukar junan. Maza marubuta ma sai ka ji an ce wane kaza, shi ma wane kaza, shi kuma wane kaza.
Ba zan bayyana irin abubuwan da ake cewa ba, domin na san kun sani. Idan an ce aibantawa, to ai ba batun alheri ake kawowa ba!
Abin mamaki, makusantan juna ne ke aibanta junan su. Tunda kuwa haka ne, idan har ba ka gaskata su ba, to maganar wa za ka ɗauka?
E, mun ji ana haba-haba da juna ɗin, ana girmama juna, ana ƙawance, ana abota, ana menene, har idan biki ko taro ya tashi sai a yi kwamba a cika wajen, ana arerewa da nishaɗi da yaushe-rabo-da-gamo. Amma can a gefe kuma wasu na ɓata wasu da munanan kalamai. Wasu ɗin ma yardaddun juna ne.
Ba shakka, irin wannan mugunyar halayyar ta na da tasiri wajen daƙile yawaitar auren marubuta a junan su. Ta yiwu kuma ita ce ta ke hana marubutan su yi tunanin haɗa zuri’a a tsakanin su, sai su gwammace su haɗa aure da wasu gidajen can daban.
Shin ‘yan fim ba su aibanta juna? Su na yi, sosai ma kuwa. To amma da alama sun fi marubuta toshe kunne ga ɓatancin da su ke yi wa junan su, musamman idan har soyayya ta shiga tsakani. A ƙarshe, sai ka ga sun yi aure sun zauna da junan su har sun hayayyafa.
Ta yiwu marubuta sun fi ‘yan fim ɗaukar zuga da gaske. Akwai lokacin da wani marubuci ya so ya auri wata marubuciya; marubuta ne su ka zuge shi da labarai marasa daɗi har ya karaya. Ya canja zuwa wata marubuciyar, can ma ba su tsira ba. Aka tsorata su. A ƙarshe, ya auri wadda ba marubuciya ba. Hakan ta faru ga wani marubucin kuma da ya so auren marubuciya ‘yar’uwar sa, shi kuma ita aka zuge, ta ƙi yarda ta aure shi.
To, ina mafita? Akwai hanya ɗaya: marubuta su daina aibanta junan su. Girman da su ke ba juna a bayyane ya zama girmamawa ta baɗini. Su riƙa yi wa juna shaidar alheri. Su tuna, su ‘yangata ne a wajen jama’a domin ba mutanen gari ke ɓata su ba kamar yadda ake ɓata ‘yan fim. Su babu mai ɓata su sai su ya su. Dara ce ke cin gida! Don haka da zaran sun gyara cikin gidan su, komai zai tafi daidai.
Kada a kawo maki labarin marubuci zai auri marubuciya ki shiga sukar ta ko ɓata shi. Annabi (s.a.w.) ya ce ki faɗi alheri, ko ki yi shiru. Ki taimaka wajen haɗa sunna.
Mu tuna da hujjojin Hafsat Umar Azare: in mu ka daure za mu yi nasarar samun zumunci mai ɗorewa. Kada soyayyar ta zama ta fatar baki.
Wani abu da na fahimta ma shi ne sau da yawa sukar da marubuci ke wa marubuci ƙirƙira ce. Manufa, da yawa abubuwan da ake faɗi ba gaskiya ba ne. Ko da akwai ɓurɓurbushin gaskiya a wasu wuraren, shaci-faɗi ne ya fi yawa.
Zan rufe da ƙara shelanta alwashin da marubuciya Jamila Umar Tanko (JUT) ta sha jiya a Gidan Marubutan Hausa, inda ta ce: “Na ɗauki nauyin sadakin zawarawa 3 na farko da za su fara haɗa kan su aure.”
To, ya kamata a samu wani kuma ya biya wa wasu sadakin ‘yan mata marubuta guda biyu. Haka kuma ina fatan wasu za su yi kukan kura su warware wancan ƙullin, su karya ƙwarin juna. Ta haka sai a rage yawan marubuta marasa aure, maza da mata.