
Kwanan nan aka yi wani ƙasaitaccen biki na karrama marubutan Hausa uku waɗanda su ka yi zarra a gasar rubuta littattafan hikaya na Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir Ƙaraye, wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kano. Maiɗakin marigayin, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, wadda ita ce Sakataren Zartaswa ta Hukumar Aikin Shari’a ta Ƙasa (Executive Secretary, National Judicial Service Council), ita ce ta ɗauki nauyin shirya gasar. Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja, ita ce ta gudanar da bikin. A tarihin adabin Hausa, ba a taɓa yin gagarumin bikin karrama marubuta irin wannan ba. Taron da za a iya kwatanta shi da wannan shi ne wanda aka yi a kamfanin buga littattafai na Gaskiya Corporation da ke Zariya lokacin da aka ƙaddamar da sabon bugu na wasu daga cikin littattafan Alhaji Abubakar Imam, cikin 1981, wanda ba a daɗe da yin taron ba Allah ya ɗauki ran shi Alhaji Imam. To amma ko wancan taron na Zariya bai ko kama ƙafar wannan ba wajen bunƙasa da alfarma. Abin sai wanda ya gani!
Wani abu da ya ba mutane da dama mamaki game da wannan gasa shi ne yanayin su waɗanda su ka shirya gasar. Irin abin nan ne da ake cewa ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaƙa. Na farko, mutumin da ya fara kawo shawarar shirya gasar, ba Bahaushe ba ne. Inyamiri ne mai suna Mista Patrick Tagbo Ogujiofor. Ma’aikaci ne a wannan hukuma ta aikin shari’a, inda shi ne jami’in yaɗa labarai. A bayanin da ya yi a jarida kwanan baya, Ogujiofor ya ce tunanin shirya gasar ya faru ne a bara, lokacin da su ka je ta’aziyyar rasuwar Injiniya Bashir Ƙaraye. A lokacin, uwarɗakin sa Hajiya Bilkisu ta ɗan furta cewa mijin ta mai ƙaunar karance-karancen littattafan Hausa ne da kuma son haɓaka adabi. Wannan abu ne wanda kusan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar adabin Hausa ba su sani ba, domin kuwa yawancin su ba su yi mu’amala da shi Injiniyan ba.
To, inda kaya su ka tsinke a gindin kaba shi ne, shi Patrick wani ƙusa ne a harkar rubuce-rubuce, amma fa da Turanci. Ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar ANA ta Jihar Yobe, lokacin ya na aiki a can. Mutum ne mai son al’amuran Hausa, kuma ya na jin Hausa kamar jakin Kano. Kai, matar sa ma Bahaushiya ce!
Saboda haka sai ya ba Hajiya shawarar cewa ya kamata ta shirya wani abu wanda zai sa a riƙa tunawa da marigayin. Nan take sai ta amince da hakan. Su ka tsara cewa a shirya gasar rubutu ga marubutan Hausa. Wani abu da zai ba ka mamaki kuma shi ne, ita kan ta Hajiya Bilkisun ba Bahaushiya ba ce. ’Yar ƙabilar Igbirra ce daga Jihar Kogi. Amma wannan bai hana ta amincewa ta ɗauki nauyin shirya gasar ba.
Patrick kuma memba ne a ƙungiyar ANA ta Abuja. Sai ya shigo da ƙungiyar cikin al’amarin, inda shi da shugaban ƙungiyar, wato Dakta Emman Usman Shehu, su ka shiga fafutikar shirya gasar. Ina jin in ban da shi Emman Shehu da kuma wani lauya Bazazzagi, marubuci, mai suna Ahmed Maiwada, babu Bahaushe a ƙungiyar. Waɗannan bayin Allah sun yi aiki tuƙuru wajen shirya wannan gasa har Allah ya sa aka yi ta aka gama lafiya.
Na ba ku wannan dogon tarihin ne don ku fahimci cewa ba Hausawa kaɗai ba ne su ke da kishin cigaban adabin Hausa. Za ma mu iya cewa su Hausawan, musamman Musulmin cikin su, ba su damu sosai da cigaban al’adun su ba; sau da yawa su kan bari wasu can su shirya musu hanyoyin haɓaka al’adun su, musamman a fannin rubutu.
Ga hujja. Gasar rubutu ta farko da aka shirya, a cikin 1933, wani Bature ne jigon yin ta. Baturen, Mista Rupert M. East, jami’in ilmi ne a Zariya. Shi Turawan mulkin mallaka su ka ɗora a kan aikin. A wannan gasar ne aka samu marubuta zubin farko, irin su Abubakar Imam, Abubakar Tafawa-Balewa, Muhammadu Bello Kagara, Muhammadu Gwarzo da John Tafida Wusasa. Haka kuma gasar da aka yi a cikin 1982, Garba Asiwaju Malumfashi ne jagoran shirya ta. Bahaushe ne, to amma fa Kirista. Ya shirya gasar a matsayin sa na daraktan al’adu a Ma’aikatar Al’adu ta Tarayya, ba domin addini ba, sai don haɓaka adabin Hausa. A gasar ne aka samu marubuta irin su Sulaiman Ibrahim Katsina da Bature Gagare.
Ita kan ta wannan gasar da aka yi a bana, yawancin masu shirya ta ba Musulmi ba ne; ina nufin su Patrick, Emman Shehu da Ahmed Maiwada. Biyun ƙarshe Hausawa ne, to amma ba Musulmi ba ne. Sun shirya gasar ne ba tare da sun sa tunanin addini a ran su ba, a’a sai don su ga yadda za a yi a inganta adabin Hausa, tare da maƙudan kuɗin da Hajiya Bilkisu ta bayar.
Shin ina Hausawa su ke? Ina Musulmi? Waɗannan tambayoyin su na daga cikin waɗanda ni da Farfesa Abdalla Uba Adamu, ɗaya daga cikin alƙalan da su ka yi hukunci kan wannan gasa ta Injiniya Bashir Ƙaraye, mu ka yi wa kan mu ita lokacin da shi Malam Abdalla ya zo Abuja don halartar taron karrama marubutan da su ka yi zarra a gasar. Gaskiyar magana ita ce Hausawa Musulmi ba su damu da haɓaka al’adun su ba, musamman ma dai a wannan zamanin. Ba su ɗauki rubutu da wani muhimmanci ba.
Sau da yawa, Hausawa Musulmi so su ke a ma daina rubutun. Kamar yadda Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, ɗaya daga cikin zakarun gasar Injiniya Ƙaraye, ta faɗa a hirar ta da aka buga a jaridar Leadership Hausa a makon jiya, a Kano an daɗe ana ƙoƙarin durƙusar da rubutun hikaya na Hausa na wannan zamanin. An yi tsinuwa da zage-zage a masallatai; an ce marubuta ne manyan masu gurɓata tarbiyya a ƙasar Hausa. Kuma abin sai ƙara gurɓacewa ya ke yi. Misalin hakan shi ne yadda kwanan baya Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano ta shirya gangamin ƙona littattafan Hausa, inda har Sarkin Kano sai da ya halarta kuma ya jagoranci cinna wa tarin littattafan wuta.
Kwanan nan kuma Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta fito da wata doka mai ban-dariya da takaici, inda ta ce tilas ne duk littafin da za a buga a Jihar Kano sai an kai mata shi ta karanta ta amince tukuna, bayan kuwa ga shi ba ta da masana masu lokacin yin wannan aiki. A kaikaice, manufar dokar ita ce ta hana yin rubutun kwata-kwata.
Wani abin juyayi shi ne yawancin masu sukar littattafan hikaya na Hausa ba masu karanta su ba ne. Ba su san abin da ke cikin littattafan ba. Su a ɗan ƙaramin tunanin su, babu abin da ke cikin littattafan sai labaran soyayya, sharholiya, batsa, zinace-zinace, shan muggan ƙwayoyi, da sauran su. Kawai idan an samu littafi ƙwaya ɗaya mai ɗauke da wani abu wanda bai yi musu daɗi ba, ko wata sheɗara a cikin wani littafi, shi kenan an samu makamin farfaganda, a shiga kafafen yaɗa labarai ana kumfar baki. Ba za a faɗi dalilin yin littafin da aka yi ba (misali, idan an ga batsa a wata sheɗara, a ce an yi ta ne don ta dace da muhallin ta). Kuma ba za a taɓa yin nuni da duk wani littafi mai ɗauke da irin koyarwar da su masu sukar su ke so a yi ba. Ba za su ba da misali da littattafan da su ka dace da tunanin su ba, a’a sai dai wannan ƙwaya ɗayan. Ka ga kenan ana yin alƙalanci cikin jahilci. Hakika, na san wani alƙalancin ana yin sa ne da gangan don a shafa wa marubuta kashin kaji.
Sannan kuma su masu sukar, daga hukumomi zuwa ɗaiɗaikun mutane, ba su yin komai don agaza wa marubutan. Ba su shirya taron wayar da kai, ba su yin wa’azantarwa, ba su ba da tagomashi na kuɗi, ba su shirya gasar rubutu su gindaya ƙa’idojin da su ke so, kuma ba su sayen littattafan. Hukumar A Daidaita Sahu ta alamta yunƙurin agaza wa marubutan, to amma abin da ta yi kamar ka ɗiga ruwa ne a hamadar rairayi. Wani rufin-ɗuwan-’yan bori (an rufe gaba, ba a rufe baya ba) kuma da hukumar ta yi shi ne gangamin ƙona littattafan marubuta da ta yi, waɗanda kamata ya yi ta ja su a jika, ta saka su kan hanyar da ta ga ya dace.
Abin mamaki, akwai daga cikin masu nazari da marubuta waɗanda ke yin furutan da ke ƙara iza wutar ƙyama ga marubutan. A marubuta, akwai ƙyashi da hassada da kuma tunanin in-ba-ni-ba-to-ba-wanda-ya-iya. Idan ka dubi surutan da ake yi wa juna a tsakanin ƙungiyoyin marubuta na Kano, to ka san lallai da sauran aiki.
Sannan manazarta/masana irin su Malam Ibrahim Malumfashi (wanda ke kan hanyar zama cikakken farfesa a fagen adabi) sun yi ayyukan da ke tabbatar da cewa manufar su ba ta kawo gyara ba ce; kawai su na yin sukar neman suna ne, ba tare da sun kawo tabbatattun hujjoji na sukar da su ke yi ba. Haka kuma abin baƙin ciki shi ne duk da yake wai a jami’a su ke, su ma a tsakanin su akwai ƙyashi da hassada irin ta malaman zaure. Babu shakka, Malumfashi shi ne kan gaba wajen ɓata sunan marubutan Hausa na wannan zamani; da gangan ya ƙi yarda ya fito rana a gan shi, ya laɓe cikin duhun tarihi, ya na bautar shudaddun shuɗaɗɗun gumaka. Idan wani al’amari ya taso na yadda za a yi a inganta adabin Hausa, to ba ya ciki.
Babu wata ƙasa mamallakiyar babban harshe da ya kai gawurtar harshen Hausa inda tsirarun manazarta da ’yan kazagin su masu ƙaramin ilmi su ke farfagandar jawo koma-baya a fagen adabi kamar ƙasar Hausa. Sai dai abin mamaki, da yake sukar adabi ba ta hana adabi yaɗo, har yanzu rubutun ake. Ya ƙi mutuwa ballantana a yi jana’izar sa. Masu jiran ganin kushewar sa sun haƙa kabari mai zurfi, su na riƙe da farin alawayyon yi masa likkafani, to amma akwai alamun cewa har su mutu shi adabin Hausar ba zai mutu ba. Wannan kabarin da su ka haƙa, su za a rufe a ciki.
(An buga wannan sharhin a filin Adabi na jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a ta makon jiya)