A ranar Lahadi, 24 ga Fabrairu 2008 da safe ina ƙoƙarin barin Zaranda Hotel, a Bauchi, sai ga tes daga Dakta Yusuf Adamu mai ɗauke da kalma ɗaya rak, “Congrats.”
Na mayar masa da, “For what?” A rai na, ina jin wata tsokanar ce. To amma gaba na ya na faɗuwa: Ko an ba ni sadakar aure ne, ban sani ba?
Can sai ya maido da amsar cewa ban ga abin da aka buga a shafi na 7 na Sunday Trust ta ranar ba?
Na buga tes, na ce wallahi ban gani ba. Me su ka rubuta ne? Nan ma a rai na ina ta wasiwasi. Kai, ko an naɗa ni Ministan Harkokin Fetur ne?! (Wai ma!!!)
Gaba na ya na ta faɗuwa, ina jiran amsa. Can sai Yusuf ya maido da amsar cewa ai ina daga cikin mutanen da ALUMNI (ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Bayero) za ta karrama a wurin gagarumin bikin saukar karatu da za a yi a mako mai zuwa. Malamin ya nanata cewa ina daga cikin MANYA irin su wane da wane da wane fa da za a karrama (har da tsofaffin gwamnoni).
To fa! To kuma ni me na yi da har za a karrama ni? Tambayar da na shiga yi wa kai na kenan lokacin da na bar otal ɗin, ni da aboki na, Badamasi Shu’aibu Burji (wanda ya raka ni birnin Bauchi don ganawa da Gwamna Malam Isa Yuguda, wanda mun gana da shi a daren ranar Asabar).
Mu ka shiga garin Bauchi, mu ka sayi jaridar Trust. A shafi na 7, mu ka ga sanarwa har shafi ɗaya. An lissafa jiga-jigan ƙasar nan da su ka taɓa yin BUK har mutum 50; ni ne na 15 a jerin: ”Alhaji Ibrahim Sheme, Editor, Leadership Newspaper.” To fa! Duk a jerin, babu yaro ko talaka kamar ni. Ana maka maganar jan wuya ne irin su:
– Alh. M.D. Yusufu (tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda)
– Col. Ɗangiwa Umar (tsohon Gwamnan Jihar Kaduna)
– Gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida
– Brig. Gen Yusuf Bomoi (shugaban hukumar NYSC ta ƙasa)
– Ambassador Usman Baraya (Ambasadan Nijeriya a Amurka na yanzu)
– Amb. Hassan Tukur (Fitaccen Jakada)
– Prof. Nuhu Yakub (VC, UniAbuja)
– Prof. Attahiru Jega (VC, BUK)
– Prof. Abdullahi Zuru
– Prof. Tijjani Bande (VC, UDU)
– Prof. Ruqayya Rufai (BUK)
– Senator Ahmed Sani Yarima (tsohon Gwamnan Zamfara)
– Hon. Farouk Lawan
– Haj. Aishatu Jibril Dukku (Ministar Ilimi)
– ds
Za a karrama mu a ranar 1 ga Maris, 2008 a Kano.
Har yanzun nan, idan na dubi gaggan manyan mutanen da ke cikin shafin jaridar nan, na kan yi tunanin: wace nasara na cimmawa a rayuwa da har na shiga ƙwaryar manya haka?
Babu shakka sai godiya ga Allah (SWT), mai kowa mai komai.
Shata ma ya faɗi:
“Ni ko yanzu kasuwa taw watse,
Ɗankoli da fura goran shi,
To shi ko kasuwa tai riba..”
Alhamdu lillah.
A KULA:
Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Abuja, Dr Emman Usman Shehu, shi ma ya na cikin jerin waɗanda za a karrama! Shi ne na 7 ma a jerin. Kai, mun gode Allah. Ni ban ma san BUK ya yi ba sai a ranar.