Yusuf M. Adamu (YMA): Ko za ka gabatar mana da kan ka a ta}aice?
Ibrahim Sheme (IS): Ni haifaffen {aramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina ne. An haife ni a cikin 1968, amma a takardu na ina amfani ne da 1966.
Dangi na duk Fulani ne na daji. Ban da ƙasar Mashi, sun zauna a yankin Jibiya su na kiwon shanu da noma, har su ka yi kakagida a can. Yanzu haka akwai rugagen mu a yankin Mashi da na Jibiya, da ‘yan’uwa na masu yawa.
Mahaifi na shi ne mutum na farko a rugar su da ya shiga gari ya zauna har ya yi karatun boko. Ya zauna a wurare da dama, yana sana’ar noma da kasuwanci, kuma ya yi aikin gwamnati.
Na yi makarantar firamare a garuruwan Maigamji da Ruwan Godiya da ke {aramar Hukumar Funtuwa a lokacin, na kammala a cikin 1979.
Na yi karatun sakandare a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna, 1979-1984, sannan na yi karatun digiri a fannin yaɗa labarai (Mass Communication) a Jami’ar Bayero, Kano, daga 1985 zuwa 1989. Ina alfahari da cewa lokacin da na gama karatun sakandare ni ne ɗalibin da ya samu sakamakon jarabawa da ya zarce na kowa a duk Jihar Kaduna, har aka kai ni wajen Kwamishinan Ilimi ya ba ni kyautar karramawa. Kuma ina alfahari da cewa lokacin da na kammala karatun digiri, ni ne aka ba kyaututtukan karramawa biyu mafi daraja a Jami’ar Bayero, wato kyautar ɗalibin da ya zarce kowa a sashen mu na Mass Communication da kuma ta jami’ar baki ɗaya.
A cikin 1993 na tafi ƙasar Birtaniya inda na yi karatun digiri na biyu (Masters) a fannin Communication Studies.
Na yi aikin jarida a yawancin tsawon rayuwa ta, inda na ri}e manyan mu}amai daban-daban. Misali, na yi Mataimakin Editan jaridar Nasiha ta kamfanin The Reporter; na yi Editan mujallar Rana ta kamfanin Hotline, na yi Editan ra’ayoyin jama’a da na adabi da na labaran }asashen waje na jaridar New Nigerian, na yi Mataimakin Editan jaridar New Nigerian Weekly, na yi Editan jaridar Leadership (inda daga baya na zama Editorial Director na farko), na yi Babban Editan jaridar Public Agenda, na yi Edita da Babban Editan jaridar Blueprint, na yi Babban Edita kuma mawallafin mujallar Fim da mujallun Bidiyo da Bahaushiya. Haka kuma na ri}e matsayin editan adabi na jaridar Weekly Trust na tsawon shekaru, amma aikin sa kai ne, ba ma’aikacin su ba ne. Sannan na kasance mawallafin littattafai a kamfanin Informart Publishers Limited, wanda nawa ne. Bayan haka, na ta~a ri}e mu}amin Mataimakin Darakta a gidauniyar tunawa da Janar Shehu Musa Yar’Adua, wato wurin da ake kira Yar’Adua Centre a yau. Daga shekarar 2016 zuwa yanzu kuma ni ne Daraktan Yaɗa Labarai a Bu]a]]iyar Jami’ar Nijeriya (National Open University of Nigeria, NOUN).
Bayan haka, ni marubucin littattafai ne a harshen Hausa da Turanci. Kuma na ziyarci }asashe da ]an dama a nahiyoyin Afrika, Asiya, Turai da Amurka.
YMA: Me ya fara jan hankalin ka ga karance-karance kafin ka shiga rubuce-rubuce?
IS: Lokacin da mu ke firamare a Ruwan Godiya, akwai wani malamin mu na Hausa mai suna Malam Ba}o Daudawa. Shi ne ya ri}a karanta mana littattafan Hausa na }ir}irarrun labarai, musamman ma dai Magana Jari Ce. Daga nan na fahimci cewa ashe akwai wata duniyar ban da tamu, wato duniyar da ke cikin littafi. Akwai mutane da garuruwa da }auyuka da dabbobi da tsuntsaye da aljannu da dodanni a waccan duniyar ban da tamu. To, kuma na san akwai wata duniyar, wato ta cikin tatsunniyoyi. Sai na za}u da son sanin wasu abubuwan game da duniyar cikin littattafai, don haka ina da]a girma ina da]a son karanta ta. Kuma sai na yi sa’a, mahaifi na ya ri}a sawo mani littattafan Hausa masu ]auke da labaran hikaya irin su Ruwan Bagaja, Iliya [an Mai}arfi da sauran su. Daga baya sai da na kasance kamar babu kamata wajen karance-karance a duk karkarar mu.
YMA: Me ya ja ka sha’awar rubuce-rubuce?
IS: Karance-karance ne ya ja hankali na zuwa ga rubuce-rubuce. Akwai wani abu da na gano game da duniyar da ke cikin littafi, shi ne ita duniyar littafi ashe mutum na iya }ir}irar tasa, ya bayyana ta a yadda ya ga dama kamar yadda Malam Ba}o ya ke fa]a mana cewa Alhaji Abubakar Imam ne ya rubuta dukkan abin da ke cikin Magana Jari Ce. Da na }ara girma ka]an sai na gano cewa ni ma zan iya }ir}irar tawa duniyar a rubuce har wani ya karanta ya fahimce ta. Saboda haka tun ina yaro }arami na fara rubutu. Duk littafin da na karanta – na rubutun zube ne ko wa}e ko wasan kwaikwayo – sai in ga lallai zan iya rubuta makamancin sa.
YMA: Ta yaya inda ka taso ya yi tasiri a kan ka dangane da harkar rubuce-rubuce?
IS: Rayuwar }auye ta yi matu}ar tasiri a kan harka ta ta rubutu. Ka ga dai a }auye akwai luggar sarrafa harshe, akwai ]imbin labarai, akwai yanayin iska da koke-koken dabbobi da na tsuntsaye, da rafuka da kwazazzabai da dazuzzuka. Rayuwar karkara ta kaifafa mani zuciya da basira ta matu}a.
YMA: Wane littafi ka fara rubutawa, ta yaya ka rubuta shi kuma menene makomar sa?
IS: Ban iya tuna littafin da na rubuta, domin su na da yawa. Wallahi, ko kwanan nan a cikin komatsai na irin na da sai da na ci karo da wani littafi da na rubuta da rubutun hannu, mai tsawon gaske, kuma kammalalle. Yanzu haka ban san labarin da ke cikin sa ba, sai na sake karantawa. To akwai irin su da yawa. Akwai na zube da na wa}e da na wasan kwaikwayo. Kuma na rubuta su ne a wasu lokuta can baya lokacin ina rayuwar ka]aici, domin ni a gidan mu ba mu da yawa, saboda ni ka]ai ne ma yaro a gidan, ba ni da abokin wasa ko hira sai littafi, don haka in dai ina so in yi maganin ka]aici, to ko dai in fita in je yawo ko kuwa in rufe kai na cikin littafi – in karanta ko in rubuta.
YMA: Wa]anne marubutan Hausa ne su ka yi tasiri a kan kan da rubutun ka?
IS: Duk marubucin da ka san ya rubuta littafi daga zamanin su Imam har zuwa zamanin su Bature Gagare, da wuya idan akwai wanda ban karanta littafin sa ba. Amma wa]anda su ka yi tasiri a kai na babu kamar Imam da wan sa Walin Katsina Muhammadu Bello Kagara da Gagare da Umaru Dembo da Aliyu Namangi da Sa’adu Zungur da A}ilu Aliyu da kuma littattafan da ba a san marubutan su ba irin su Dare Dubu Da [aya. Akwai kuma wa]anda ba na }ir}ira ba ne, irin su Hausawa Da Ma}waftan Su, Ibada Da Hukunci da sauran su.
YMA: Wa]anne marubutan Ingilishi ne suka yi tasiri a kan kan da rubutun ka?
IS: A gaskiya, su ma suna da yawan gaske. Ni fa duk littafin da na gani sai na karanta shi, ko da na wani addini ne. Akwai ma na wasu yarukan da aka yi aka fassara su zuwa Turanci. Fitattun sun kama daga kan su Shakespeare, Chaucer, Dickens da Milton har zuwa kan su James Hadley Chase, Jackie Collins, Nick Carter, Sidney Sheldon, Chinua Achebe, Cyprian Ekwensi, Labo Yari, Naguib Mahfuz da sauran su. Bugu da }ari, akwai littattafai da dama da ba na adabi ba, masu magana kan tarihi, falsafa, siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa.
YMA: Zuwa yanzu littattafan Hausa da na Ingilishi nawa ka rubuta?
IS: Ban san iyakar su ba, a gaskiya. Sai na bincika.
YMA: Guda nawa aka buga?
IS: An buga wasu a jarida ko mujalla, wasu kuma an buga su a littafi. Wa]anda aka buga a matsayin littafi su ne: Kifin Rijiya da ‘Yartsana da kuma The Malam’s Potion, Ilmi Mabu]in Tafiya, Shata Ikon Allah, sai kuma littafin tarihin rayuwar Janar Shehu Yar’Adua wanda Yar’Adua Centre ta wallafa.
Wa]anda aka buga a jarida su ne: Kogin Barkono (a jaridar Nasiha), Sakin Wawa da Mudi Sarkin Wayo (mujallar Rana), da kuma Biba’s Yoke (a New Nigerian Weekly).
YMA: Me ya samu sauran littattafan da ka rubuta? Ina makomar su?
IS: Akwai wa]anda sun ~ace, wasu kuma sai yanzu na ke binciko su, wasu kuma na taskace su a fayil. Ban san makomar su ba illa in ce ina da burin buga su in da rai da lafiya. Idan kuma har na kasa buga su, to kila wata rana ‘ya’ya na ko abokai ko wasu masu sha’awar abin su buga su. A cikin su akwai na wa}o}in da na rubuta na Hausa da na Turanci da kuma na rubutun zube da na wasan kwaikwayo.
YMA: Da Kifin Rijiya da Ilmi Mabu]in Tafiya ga dukkan alamu tasirin Abubakar Imam ne. Me za ka ce game da wannan hasashe?
IS: Haka aka ce. Dalili shi ne saboda Imam ne ya fara yin irin su kafin in yi: Imam ya yi ‘Tafiya Mabu]in Tafiya’ kan zuwan sa Ingila a zamanin Ya}in Duniya na Biyu, ni kuma na yi ‘Ilmi Mabu]in Tafiya’ a kan zuwa na Isra’ila da Palas]inu, sannan ya yi littafin ‘Ruwan Bagaja’, ni kuma na yi ‘Kifin Rijiya’. Na biyu kuma an ce luggar harshen iri ]aya ce, har ana ganin in da Imam na da rai, to da an ce lallai wannan hannun sa ne.
To, ni abin alfahari ne a gare ni a kwatanta tsarin rubutu na da fi}ira ta da na Malam Imam, wanda shi rimi-kere-itace ne a fagen rubutun Hausa. Ba kowane marubucin Hausa ba ne za a iya yi masa wannan kwatantawar!
YMA: Littafin ka na Hausa da }agaggen labari da aka fara bugawa shi ne ‘Kifin Rijiya’. Me za ka ce mana game da shi?
IS: Lokacin da ina ]alibi a Jami’ar Bayero, na ga sanarwa cewa Cibiyar Raya Al’adun Gargajiya ta Jihar Kaduna saka Northern Languages Novel Writing Competition, wato “Gasar Rubuta Littattafan {ir}ira Cikin Harsunan Mu Na Gado”. Sunan gasar kenan. Sai na yi wuf, na nemi biro da takarda, na rubuta wannan littafin na Kifin Rijiya, na aika. Lokacin da ina aikin bautar }asa a Fatakwal sakamakon gasar ya fito. Ni na zo na biyu a wani sashe, yayin da Malam Mahmud Barau Bambale, shugaban kamfanin NNPC Zariya na yanzu, ya zo na ]aya. Ka ga ai na yi bajinta a nan, tunda ]aruruwan mutane ne su ka shiga gasar. Lashe gasar a wanan matakin ya }ara mani }warin gwiwa a matsayin marubuci.
A dalilin wannan littafi, wata }ofa ta bu]e mani. A lokacin da za a kafa jaridar Nasiha sai ana na]a ni Mataimakin Edita, aka ce wai tunda har na ci gasar rubutu, to zan iya aikin jaridar Hausa! A lokacin, ni ]an rahoto ne a jaridar Turanci ta The Reporter, kuma kamfani ]aya ne. Aiki a jaridar Hausa kuma ya }arfafa ni a fagen rubutu da Hausa.
YMA: Duk da cewa ka da]e ka na rubutun }agaggun labarai, musamman a jaridu da mujallu, littafin ‘’Yartsana’ ne ya fito da kai. Me ya sa ka ke ganin haka ya faru?
IS: Anya kuwa? Idan ka tuna, na riga na yi fice a Nijeriya saboda aikin jarida. An san ni sosai saboda ina daga cikin masu yawan yin rubutu a jaridun Hausa da na Turanci. Har a jaridun Kudu irin su The Guardian da irin su Nigerian Standard ta Jos ina yin rubutu tun ina makaranta.
Shi dai ‘Yartsana, shi ne ya yi fice a matsayin littafin adabi, amma ya same ni da fice na. Dalili shi ne na farko jigon sa a kan karuwanci ne, wanda shi kuma ya ta~o batun tarawa tsakanin mace da namiji, wato ‘sex’. To duk maudu’in da ya shafo wannan al’amari sai ka ga an yi masa caa.
Na biyu, littafin ya fito a daidai lokacin da harkar intanet ta fara fa]a]a a arewacin Nijeriya. Babu kamar lokacin da Dakta (a lokacin) Abdalla Uba Adamu ya bu]e wani dandali na marubutan Hausa a cikin manhajar Yahoogroups, inda ake tattaunawa da muhawara kan adabin Hausa. Na uku kuma ana }ishirwar karanta littattafan Hausa da su ka sha bamban da na soyayya da su ka cika kasuwa wajen ingancin rubutu da jigo da kuma ]ab’i. Na hu]u, da aka ce “Ibrahim Sheme ne ya rubuta littafin”, to kowa na so ya ji menene a ciki. Na biyar, an yayata littafin a cikin kafafen ya]a labarai da wuraren hira fiye da kowane littafin Hausa na zamanin sa.
YMA: Tun kafin a buga littafin ‘Yartsana na karanta shi kuma yana cikin fitattun littattafan Hausa na kowane lokaci. Me ya sa ka rubuta shi?
IS: Na farko, littafin ya zo mani ne kwatsam ba don na shirya rubuta shi ba. A cikin mujallar Rana inda ni ne edita, na kan ba mutane labarin }ir}ira shafi biyu a duk mako biyu da ta fito. Na yi warwarar labarin ‘Mudi Sarkin Wayo’ da ‘Sakin Wawa’, kila ma da wani. To da su ka }are sai na yi tunanin wane labarin kuma zan bayar. To ma ina sane da damuwar da ake yi kan karuwanci a }asar Hausa, har fasihai irin su Aƙilu Aliyu da su Mu’azu Ha]ejia sun yi wa}o}in Allah-wadai da karuwai. To ni kuma na ]an san rayuwar karuwai ta hanyar zuwa kallon wasannin ajo ko na maka]a, da kuma ziyarar wata ‘yar’uwa ta ta jini da ke karuwanci a Kano. A matsayi na na marubuci, sai na ga zan iya tada labari mai jan hankali a kan su. Don haka na fara rubutun a mujallar Rana. Sunan littafin ‘Balaraba: Labarin ‘Yar Gagara’. Bacwai akwai littafin ba ne a aje. Duk mako biyu na ke rubuta wanda zai cika mana shafi biyu in bayar. Haka aka dinga gutsira wa masu karatu shi har aka zo zan tafi Ingila }aro karatu. Sai na rubuta na wasu makwanni, na ba wani aboki na wanda yanzu Farfesa ne, wato Ibrahim Malumfashi, na ce ya ri}a ba su. Bayan na tafi da wani lokaci aka rufe kamfanin. Har sai da na dawo sannan na }arasa labarin, kuma na himnatu wajen fito da shi a matsayin littafi. Ya fito a cikin 2003.
YMA: Ina dangantakar rayuwar ka da wadda aka bada labarin ta a littafin ‘Yartsana?
IS: Zainab ta cikin littafin, wadda ake kira Asabe, }ir}ira ce. Rayuwar ta kuma ha]e-ha]e ce ta labaran mutane daban-daban, wasu na san su, wasu kuma na ji ne, sannan wasu kuma na }ir}ire su ne.
YMA: Me ya sa ka yafe wa Bebi Sai-Tumoro amma ka }i yafe wa Asabe a cikin ‘Yartsana?
IS: Ba ni ba ne. Ni marubuci ne kawai. Babu wani tsari ko wata hanya da na aje domin bin ta wajen bada labarin. Kawai dai labarin ya zo, na aza shi a kan takarda. Ya rage ruwan ku, manazarta, ku fa]i ra’ayin ku ko fahimtar ku a kai!
YMA: Wa ka fi so a cikin taurarin da ka }ir}ira a cikin Kifin Rijiya da ‘Yartsana?
IS: Ban san wanda na fi so ba, a gaskiya.
YMA: Menene dangantakar ka da taurarin littattafan ka?
IS: Akwai taurarin da na san su a zahiri, akwai kuma wa]anda na }ir}ira. Su wa]anda na sani ]in, na sauya masu siga ko kuma na }aro wasu abubuwan da ba su ne suka yi su ba, na caku]a a rayuwar su ta littafin ta yadda su kan su ba su iya gane cewa su ne.
—–/
bambanci mai yawa. Da yawa daga cikin mutanen da ake bada labarin su a littafin, mutane ne da za a iya kira ‘yan iska. Ni kuma ba ]an iska ba ne, mai neman karuwai. To amma na fahimci rayuwar karuwai da maneman su ne saboda a zahiri na san wasu karuwan da maneman su ta hanyar abota da kuma bincike, da kuma ziyara. Idan mutum ya dubi rayuwa ta ko kuma ya san ni, to babu wanda zai ce maka ya san ni a gidan karuwai ko ya gan ni da wata karuwa.
——
YMA: A game da adabin Hausa na zamani, ka na ganin ya taimaka wa harkar rubuce-rubucen Hausa?
IS: {warai kuwa, ya taimaka. Ya kasance kadarko ko gada a tsakanin adabin wancan zamanin da ya shu]e. Adabi kamar hanya mai kwanoni da mi}ewa, kuma akwai gadoji a kan ta. Idan babu gada, ba za ka iya tsallaka wagegen rami ko wani kogi da ke kan hanyar ba. Saboda haka adabin zamani shi ne ya jona adabin da da wanda ke tafe. Shi ne ke haska mana rayuwar da ake yi a yau. In da babu shi, ba mu da taskar da za mu le}a mu ga abin da aka yi a yau, kamar yadda idan mun duba adabin da za mu iya fahimtar rayuwar da aka yi a da. Don haka amfanin sa ba ya misaltuwa.
YMA: Kai ]an jarida ne, kuma ka taka rawa muhimmiya wajen ha~aka harkar littattafan Hausa na zamani tun daga zaman ka a jaridar Nasiha da mujallar Rana da su New Nigerian da kuma Weekly Trust. Wane tasiri za ka iya cewa ka yi a adabin Hausa?
IS: Kamata ya yi wani daban ya amsa wannan tambayar. Ni dai na yi aiki na, na gama. Sai mutane su duba su gani, me na yi?
YMA: An tafka muhawara a kan littattafan soyayya a abin da aka fi sani da “The Great Soyayya Debate”. Wace riba aka samu a wannan muhawara dangane da nazarin }agaggun labaran Hausa?
IS: Riba ta farko ita ce an samu }arin fahimta game littattafan wannan zamanin. Mutanen gari sun fahimci matsayar littattafan. Na biyu, manazarta ma sun fahimce su. Da farko wasu malaman jami’a da sauran manyan makarantu sun ri}a yi wa littattafan da marubutan kallon raini har ba su so au kula su. Sai su ka ga manazarta daga Turai da Amurka irin su Farfesa Graham Furniss sun zo su na nazarin su, don haka su ma sai su ka juyo su na nazarin su. Yanzu haka a nan Nijeriya an yi kundayen digiri a kan wa]annan littattafan. Kusan ma a ce ba a yi nazarin littattafan adabin Hausa na da kamar yadda aka yi nazarin na yanzu ba.
YMA: Kai da su wa kuka kafa mujallar Fim?
IS: Ni da Ado Ahmad Gidan Dabino, Yusuf M. Adamu, Abba Lawan Daneji, [an’azimi Baba Ce]iyar ‘Yangurasa, Bashir Mudi Yakasai, Garba [angida da wasu. Wa]ansu, da su muka zauna muka kafa ta, amma wasu mun shigo da su ne kawai. Ni ne mawallafin ta tun tashin farko domin jarin da na zuba ya fi na kowa, sannan ni ne wanda ke da lokacin yin ta a matsayi na na ]an jarida. Bayan kamar shekara ]aya, a shekarar 2000, aka samu rashin fahimtar juna wanda ya sa kowa ya janye, na biya su ku]i, aka bar daga ni sai [angida. Shi ma [angida, daga baya na biya shi ku]i ya fita, mujallar ta zama tawa ni ka]ai.
YMA: Wane tasiri ta yi a Kannywood?
IS: Bana shekarar mujallar 21 tana fitowa. Ta yi shekara 20 buga ta a kowane wata. Amma a bara sai na dakatar da buga ta, ta koma ana fitar da ita a gidan yanar ta a intanet, amma ana rarraba labaran a shafuka daban-daban na soshiyal midiya. A tsawon wa]annan shekaru, ta kasance hanya mafi inganci wajen samun labaran harkar finafinan Hausa. Ta yi tasiri matu}a musamman wajen taskace labaran abubuwan da su ka wakana a harkar, daga tarihin ‘yan wasa har zuwa aikace-aikacen su na shirya fim, ko wani cigaba, ko cibaya, da rigingimun su, haihuwa, aure, taro, tafiye-tafiye, mutuwa da sauran su. Yanzu duk mai neman tarihin harkar fim idan bai duba mujallar ba to, ya bar aiki baya.
YMA: Me ya samu mujallar Bidiyo da Bahaushiya ba su da]e ba?
IS: Na kafa mujallar Bidiyo me da nufin bada labarai da dabarun shirya fim ka]ai, da sharhi kan finafinan. Babu ruwan ta da rayuwar ‘yan fim ]in kamar mujallar Fim. Bayan kamar shekara ]aya ta na fitowa sai na daima buga ta saboda abu biyu: babu kasuwa sosai domin mutane sun fi son su karanta gulmar ‘yan fim, na biyu kuma ba ni da isasshen lokacin cigaba da aikin ta.
Ita kuma Bahaushiya, manufar kafa ta ita ce a ri}a bada labarai kan al’adun Hausawa da Fulani ne ka]ai, wanda ya ha]a da tarihi, littattafai da marubuta, ki]a da wa}a, sana’o’i, sarautu, bukukuwa da makamantan su. Guda ]aya ka]ai aka buga. Ita ma na daina ta ne saboda wa]ancan dalilai biyu da su ka ci Bidiyo. Amma ita sai na fitar da wasu shafuka a cikin mujallar Fim, can wajen }arshe, na ci gaba da buga abubuwan da na ke so in gani a cikin Bahaushiya ]in. Wato kenan Fim ta goya Bahaushiya. Har yau ]in nan kuwa haka ake yi; duk kwafen Fim akwai Bahaushiya a ciki.
YMA: Bayan rubutu sai kawai ka fantsama harkar shirya fim. Me ya faru?
IS: Da ma can rubutu da fim [anjuma ne da [anjummai. Kuma tun ina sakandare na ke sha’awar finafinai, shi ya sa ma mu ka ri}a zuwa kallon fim a gidan sinima. To da na tsinci kai na a matsayin ]an jarida a Kannywood, sai kuma harkar fim ta mamaye ni. Da yake ni marubucin labari ne, sai na yi sha’awar ni ma in shirya fim a matsayin furodusa.
YMA: Wace rawa ka taka a harkar shirya fim bayan rubuta labarin fim, wato “script”?
IS: Babbar rawar da na taka dai ita ce wallafa mujallar Fim. To kuma na shirya finafinai nawa na kai na da su ka ha]a da ‘Gagarabadau’, ‘Artabu’, ‘Daren Farko’, ‘Fargaba’, ‘Jaraba’ da wani wanda na manta sunan sa. Na yi aiki da manyan jarumai da su ka fito a finafinai na, irin su {asimu Yero, Hajara Usman, Hamisu Iyan-Tama, Ibrahim Mandawari, Musa Mohammed Abdullahi, Maryam Mohammed [anfulani (Mashahama), Hindatu Bashir, Ali Nuhu, Adam A. Zango, Ahmed S. Nuhu, Misbahu M. Ahmad, Shu’aibu Kumurci, Saratu Gi]a]o, Hauwa Maina, Sani Mo]a, Farida Jalal, da wasu ma. Bayan haka, na rubuta irin wa}o}in nan da ake sakawa a finafinai. Manyan mawa}a da su ka rera wa}o}in da na rubuta sun ha]a da Yakubu Muhammad, Abubakar Sani, Rabi Mustapha, Murja Baba, Maryam A. Baba, Maryam Fantimoti, Misbahu M. Ahmad da sauran su. Hatta aikin daraktin na ]an ta~a a Kannywood.
YMA: Ko wa ya san ka, ya san kai marubucin tarihin Alhaji Mamman Shata ne. Me ya ha]a ka da Shata?
IS: Mahaifi na ne ya fara ha]a ni da Shata domin su aminan juna ne. Kuma shi ne ya ba ni }warin gwiwar in rubuta tarihin Shata bayan na yi tunanin dacewar hakan. Sai na yi sa’a, Shatan ya amince. Hira ta ta farko da shi wadda na ]auka a faifai, min yi ta ne a cikin shekarar 1992. Bayan na yi shekaru ina aikin, har na je Birtaniya na }aro karatu, sai wani aboki na ya kawo Aliyu Ibrahim {an}ara waje na a cikin 1997, a bisa bu}atar sa ta mu ha]e mu yi littafi ]aya. Ni kuma na amince a kan tunanin cewa zai taimaka mani wajen bincike domin shi Shata teku ne, kuma hannu ]aya ba ya ]aukar jinka. Bayan haka kuma sai mu ka ha]e da wasu mutanen Kano su biyu, mu ja zama mu hu]u a kan aikin. Amma ni ne jagoran aikin, kuma mai rubuta littafin, har mu ka }are, aka }addamar da littafin a Gidan Arewa a Kaduna a cikin 2006.
YMA: Ba mu labarin ‘Shata Ikon Allah!’ a ta}aice.
IS: Na fa]a maka yadda aka rubuta shi. Ni na rubuta shi, amma mu hu]u ne muka yi binciken tarihin Shatan. Kowannen mu ya yi hira da mutane, musamman wa]anda Shata ya wa}e ko ya yi wata mu’amala da su. Amma ni ka]ai ne wanda ya yi hira kai-tsaye da Shata, domin ni ka]ai ya sani a cikin mu hu]un. Idan wani ya ce maka ya ta~a yin hira da Shata, to ka ce ya nuna maka ita!
Littafin ya }unshi tarihin Alhaji Shata tun daga asalin }asar Hausa har zuwa haihuwar Shatan da rayuwar sa baki ]aya zuwa mituwar sa da ma bayan rasuwar sa. Ta cikin tarihin nasa kuma za ka ci karo da tarihin wasi mutanen da su ka shafe shi, kamar wa]anda ya wa}e da kuma iyalan sa.
Bayan fitowar bugu na farko na littafin a cikin 2006, sai abokan binciken nawa kowa ya kama gaban sa, aka bar ni ni ka]ai. Don haka sai na koma ruwa, na ci gaba da binciken tarihin Shata. Hakan ya sa aka samu bugu na biyu na littafin, wanda ya fito a cikin 2018. Shi wannan na biyun, ya zu}e duk abin da ke cikin na farkon, tare da gyara kurakurai, sannan kuma ya }unshi }arin bayanan da na kalato a cikin shekaru 12 bayan fitar na farko. Ko a yawa ma, ya fi na farkon da shafi sama da 300. Kuma aikin ]ab’in sa ya fi na farkon inganci. Ya fito a kala biyu, mai laushin bango da mai }arfin bango.
YMA: Bayan Shata, ka yi aiki a kan wasu mawa}an, kamar su Ahmadu Doka da Barmani Choge da Uwani Zakirai, }ila ma da wasu. Me ya ha]a ka da su?
IS: Haka ne. Na lura da cewa akwai }amfar cikakken tarihin mawa}an mu na Hausa, kuma ga shi zamani na ta shafe tarihin, ba a taskace shi ba. Shi ya sa na ]aura ]amarar ganin na yi abin da zan iya.
Akwai babban }o}ari da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya yi ko yake yi na taskace tarihin mawa}a. Tilas mu yaba masa, kuma mu gode masa. Amma tsarin sa ba irin bawa ba ne, in ban da tarihin Abdu Karen Gusau da ya yi; shi, a ta}aice ya kawo tarihin mawa}a a littattafai biyu na ‘Maka]a Da Mawa}an Hausa’, ni kuma bu]awa na ke yi. Kowanne tsari ya na da ranar sa.
YMA: Duban yadda aka taimaka wa nazarin Hausa shekara da shekaru, me ka ke son gani masana da manazarta sun maida hankali a kan sa?
IS: A gaskiya, ban gamsu da manazartan Hausa ba. Sun yi sake da yawa. Akwai ]imbin al’amura na Hausa da ya kamata a yi bincike a kan su domin a taskace su. Ni da yake na fi maida hankali ga tarihi da rubutu, sai in ga akwai wagegen gi~i da ba a cike ba. Manazarta sun shantake, ba su motsawa su yi balaguro domin bincike. Kuma na ji an ce ana ware ku]i domin binciken, to me ya sa ba su yi? Sai ka ga an shafe shekaru ba a fito da wani abu mai }wari ba, an bar ire-iren mu ‘yan bayan fage, ciki har da kai, wato ba ‘yan cikin harkar nazarin harshe da adabin Hausa ba, mu na ta cizon yatsa tare da }o}arin yin abin da za mu iya. Na ma ji an ce wasun su ba su so mu yi aikin, wai fagen su ne; to amma kuma idan ba su yi ba, mu ba mu yi ba, wa zai yi?
Ina kira ga manazarta da su tashi tsaye, kowa ya ]auki abin da zai iya, ya yi, ba domin komai ba sai saboda ‘yan baya. Manazarta a nan ina nufin duk mai sha’awa, ba lallai sai ‘yan cikin harkar nazari a jami’a ko babbar kwaleji ba. Yanzu da a ce magabatan mu sun yi irin wannan aikin, ai ka ga da sun hutasshe mu.
YMA: Zuwa yanzu, menene a gaban ka?
IS: Ina aiki kan tarihin wasu mawa}a. Ka ambaci wasu ma. Bayan haka, akwai tsofaffin littattafai na da ba a buga ba, ina so in gyara su in fitar da su don a karanta. Akwai kuma littattafan wasu daban, kamar na mata ta, marigayiya Binta S. Mohammed, su ma ina so in fito da su. Amma idan na dubi girman aikin, sannan na dubi aikin ofis da na kula da iyali da na zumunci da ke gaba na, wallahi sai in ji kamar ba zan iya ba. Amma dai ko ma yaya ne, zan yi iya abin da zan iya kafin in amsa kiran Mahaliccin mu.
YMA: Mun gode da damar da aka ba mu.
IS: Madalla, ni ma na gode.
![]()


