KAFIN mu yi wannan hirar da Alhaji Ali Ɗansaraki ’Yankara, yawancin mutane sun ɗauka cewa tuni shahararren makaɗin kukumar ya kwanta dama. Dalili shi ne an daɗe ba a sake jin wata sabuwar waƙa ta fito daga gare shi ba, kuma ba a ganin sa a wuraren bukukuwa kamar yadda aka saba a da.
Wasu kuma na cewa muryar mawaƙin ta mutu, kuma wai Alhaji Mamman Shata ne ya kashe ta saboda kishi. To, a game da batu na farko, na samu Alhaji Ali Ɗansaraki lafiya lau a garin su, ‘Yankara, cikin Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina. Na biyu kuma, babu shakka muryar sa ta “mutu”, ko kuma a ce ba ta fita sosai. To amma ba Shata ne ya “kashe” masa murya ba, kamar yadda shi kan sa ya faɗa. A cewar Ɗansaraki, “Ni wallahi ban yarda da cewa yana iya yi wa mutum wani abu ba, don ba zai tsaya yin haka ba.”
To, me ya sa muryar Alhaji Ɗansaraki ta daina fita? Shi kan sa bai san dalili ba. Yakan dai yi bakin ƙoƙarin sa don yin waƙar, amma ya fi mayar da hankali ga aikin gona inda har ya yi arzikin mallakar gidaje, gonaki, mota, da iyali tare da kwanciyar rai.
Alhaji Ali Ɗansaraki, wanda wasu suka riƙa kwatantawa da Shata don bunƙasar sa da gawurtar sa a fagen waƙa a da, ya tattauna da ni Ibrahim Sheme, a gidan sa da ke ‘Yankara a ranar 9 ga Janairu 1993, a kan asalin sa, sana’ar sa da rayuwar sa ta yau da kullum, kamar haka:
IBRAHIM SHEME: Alhaji Ali Ɗansaraki, shekarun ka na haihuwa nawa yanzu?
ALI ƊANSARAKI: Ina da shekara kusan sittin, don yanzu ba jikoki ba har yarinyar da na haifa ta haihu, ita ma (‘yar ta) ta haihu.
An haife ni a Unguwar Bagudu, hanyar zuwa Bilbil a nan ƙasar Zagami (wato ‘Yankara, cikin Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina). A lokacin babu mota. Uba na ya fito ne daga wani gari a ƙasar Safana (ta Katsina) ana ce da shi ‘Yar Tumɓurkai. Daga can da ya taso ya dawo Unguwar Bagudu, nan aka haife ni. Bayan mun fara wayo muka koma Unguwar Malam Shayau; shi Shayau wani riƙaƙƙen ɗan damfara ne wanda ya mutu a Legas.
SHEME: Mecece sana’ar iyayen ka?
ƊANSARAKI: Uba na bai da wata sana’a sai noma. Nan ya zo ya auri uwa ta a Unguwar Bagudu, amma ita mutumiyar Dogon Dawa ta Birnin Gwari ce. Sunan uba na Adamu, ita uwa ta Binta.
SHEME: Ko akwai wanda ke da rai a cikin su yanzu?
ƊANSARAKI: A’a.
SHEME: Shi yaya irin shaharar ka a wa}a take?
ƊANSARAKI: Na shekara ta kai arba’in ina waƙa. Na tashi da waƙar Shata (wadda ake kira) “Ahayye”. Dukkan maroƙin da ke nan ƙasar, da wuya a sami wanda ya girme ni: waɗanda ke gaba da ni, su (marigayi) Ibrahim Ɗanmani Caji a gidan shi na tashi. Daga nan na tafi Sakkwato. Ni da wani mawaƙi mai suna Hassan Gama-giwa da ya rasu a Maraɗi muka zauna a gidan Ɗanmani.
SHEME: Tunda sana’ar gidan ku noma, yaya aka yi ka fanjama cikin waƙa?
ƊANSARAKI: Uwa ta iyayen ta makaɗa ne, amma ban san wani da ke waƙa a ɓangaren mahaifi na ba. Shi (uba na) bayan rasuwar shi na je inda ya taso, na haɗu da wata ɗiyar wan uba na, wanda ya rasu bara.
SHEME: Shin da kukuma ka tashi?
ƊANSARAKI: A’a, da roƙo na tashi. Tun a Unguwar Bagudu, akwai wata yarinya ana ce mata Ba’u ‘Yar Inusa, in ina wasa takan yi min liƙi.
SHEME: Yaushe ne ka fara roƙon?
ƊANSARAKI: Lokacin ana waƙar Shata, ‘Ahayye Alewa’. Ina da wani mutum mahauci, ana ce da shi Ɗalladi. Sai in zo ina waƙa ta, ‘yan mata suna amsawa har a tashi. Sai Ɗalladi ya zo ya tada mu in muna barci a kan layi, ya ce in zo in yi waƙa. Muna yi har muka riƙa zuwa ƙauyuka muna yi a gidajen biki. Da Allah ya taimake ni, sai muka gane cewa bin ƙauyuka wawanci ne. Daga nan sai mu je mu sauka a gidan mutum, a ce Ɗansaraki ya zo wajen wance.
SHEME: Shin ko kana da malamin waƙa?
ƊANSARAKI: Na taɓa bin wani ana ce mashi Garba Maiganga, mutumin ƙauyen Zagami. Shi na fara bi yawon waƙa, lokacin duniya tana kwance.
SHEME: Me ya sa ake ce maka “Ɗansaraki”?
ƊANSARAKI: Laƙanin Saraki, asalin sa wata uwa ta ce, ‘yar’uwar uwar mu, ta zo ƙauyen Unguwar Bagudu wajen ‘yar’uwar ta, sai aka haife ni a ranar da ta sauka. Daga nan aka sa min “ɗan Saraki”, sunan kuma ya bi ni.
SHEME: Shi Garba Maiganga, kukuma yake yi?
ƊANSARAKI: A’a, makaɗi ne na dule ƙwairama. Ba za ka gane ta ba, ta yi kama da irin gangar nan ta noma. Shi ke kiɗin, ni ke waƙa. Ni na yi waƙar ‘Alhamdu Lillahi, Na Ci Na Sha, Na Yi Bikin Dangi, Har Na Yi Aure.’ Muna tare da wani wai shi Tunau, da wani makaɗi shahararre ana ce mashi Adada na Ali Baban Sani, ya rasu. Tunau da wani Maigiya suka saci fam hamsin na Adada, aka kai su Katsina suka yi fursuna. Da aka sako su, sai Maigiya ya dawo nan, Tunau ya zauna a Dutsin-ma, ya yi tashe sosai har ya rasu. Da suka yi satar ne muka rabu, lokacin ban taɓa zuwa Dutsin-ma ba.
Abin da ya sa na rabu da waƙar Shata shi ne, ‘yan amshi na da masu kalangu suka fara yi min yawo da hankali. In na neme su mu je wasa sai su ƙi. Da rai na ya ɓaci, sai ni da wani yaro na, Zabo, muka tafi kasuwar Tumɓurkai tare da wani mawaƙi na ana ce mashi Wutar Kargo; yana nan da ran shi. Ana taron siyasa a Mahuta, muka tafi can muka haɗu da maroƙa aka yi abin arziki. Muka je wurin wani mawaƙi, Ali Maifamis, da Ɗandaura. Sai na ga Ɗandaura da kukuma, na ce ya sayar min. Sai ya ce, “Na ba ka kyauta.” Na ɗauka na dinga yi. Daga nan fa sai na fita maganar waƙar Shata, na shiga kukuma. Na samu yaro na Zabo muka riƙa yi mu biyu. Ran nan sai na samu wani yaro, Labbo Maikalangu, da Ɗan’auta wanda ya zo daga Dabai.
SHEME: Bayan ka haɗu da wannan ƙungiya, sai kuka ci gaba da kukuma gadan-gadan?
ƊANSARAKI: E, lokacin da aka naɗa Sarkin Maska Hakimin Funtua, Shehu. Ina zuwa wurin Makama na Bakori, Idi, a garin Guga, ya ba ni doki. Lokacin ya zo da Bishir Fiyafiya, Shugaban Ƙaramar Hukumar Funtuwa da aka tuɓe kwanan baya, lokacin yana ƙarami yayayye, Makama ya zo da shi rangadi, ina yi wa Makama waƙa ina cewa, “Kada Hana Wanka Uban Malam Sule, Uban Su Talatu Da Muɗɗaha”.
SHEME: Wato dai sai abu ya kankama, har ka fara shafe sauran masu kukuma?
ƊANSARAKI: E, ita kukuma yadda take shi ne, wanda duk ke yin ta, in ba Ibrahim Nahabu ba, babu wanda ya kai ni. Har marigayi Habibu Sakarci ni maigidan sa ne. Ina yi mashi alheri, saboda shi mutum ne mai biyayya. A sana’ar nan, duk inda muka haɗu a taro, Habibu sai ya tsugunna ya gaishe ni.
SHEME: Da ina da ina ka je harkar waƙa?
ƊANSARAKI: A Nijeriya? Na san Katsina, don ita ce ƙasar mu. To lokacin Sardauna na san Sakkwato, Birnin Kebbi, Jega, kuma har Yawuri. Daga nan na san Wara da Kayama garin Minista Tukur, da Maiduguri, Jos, Bauchi, Garwa, Marwa, Mokolo, Gamdare, Yawunde. Lokacin da Sardauna ya mutu har Ahidjo shugaban ƙasar Kamaru ya aiko da mota aka ɗauke ni sai da na kwana talatin da uku a Kamaru.
SHEME: An ce Ahidjo mutum ne mai son mawaƙa.
ƊANSARAKI: E, kuma masoyin Sardauna ne.
SHEME: Shin ka taɓa haurawa ƙasashen waje?
ƊANSARAKI: Na san Ghana da Kwanni (a Nijar), sai da na je birnin Tawa da Agadas. To daga can koro mu aka yi, lokacin lafasai aka yi mana. Ka san lafasai?
SHEME: Kamar katin izini kenan?
ƊANSARAKI: E. Lokacin Jibbo yana adawa da (Shugaba) Jo Rahaman. Muna cikin wasa a Agadas, sai ga soja da mota. Da suka yi hon sai aka watse, sai mu. Aka kai mu bariki. Mu ba mu san Faransanci ba. In Bature ya yi mana magana, sai odali ya faɗi mana. A ƙarshe dai aka yi mana lafasai aka koro mu.
SHEME: Waɗanne ne manyan wasannin ka?
ƊANSARAKI: Ba wanda nake saurin tunawa kamar na Ahidjo ɗin nan. A nan birnin Garwa ya sa aka ajiye mu, sai a kawo mana abincin dare da rana har kwana takwas. Daga nan ya sauka, ya ɗauke mu zuwa rangadi, muna gaba muna waƙa. A lokacin da na baro, Ibrahim Nahabu bai je can ba ma. Daga nan sai wasan da na yi a Damagaran a gidan Alhaji Isa Maino, wani ministan Jo Rahaman.
SHEME: A wata babbar waƙa da ka yi, ka ambaci wani “taro na Sheme,” inda kake cewa ka ga sarakai ka ga idon daraja a wurin nan. Me ya faru ne?
ƊANSARAKI: Ita “Sheme” ɗin nan, ba Shemen ku ba ce. Shemen Baƙarya ce; tana nan gabas da ‘Yankara. Lokacin da ‘Yandoto Ali na Tsafe ya ce wai ‘Yarmalamai ƙasar shi ce, aka zo za a amshe ta. Aka zo da karuwai ba iyaka. A wannan karon na fara ganin Sarkin Fadan Katsina, Damale. Aka ce ga Sarkin Maska Shehu, lokacin yana Katuka kuma yana minista a Kaduna, da Ƙogo Ibrahim Hakimin Faskari, za su tafi wurin rabon iyaka. Sai ni da Zabo muka bi su, muka zo ‘Yarmalamai. Aka ce mana sunan garin Shemen Baƙarya. Ni ban san abin na ɓatanci ba ne. Muka je inda ‘Yandato yake. Akwai Sheme biyu: wannan ta Tsafe, wannan ta Katsina. Da dare, muka ji wasu ‘yan iska na zage-zage, suna cewa gobe Katsinawa sai sun ci kaza-kazan su. Da safe na je na gaida Sarkin Fada, na gaya mashi komai, sai na yi waƙa ina kambama shi tare da sukar sauran mutanen da ke ja da shi.
SHEME: A nan wurin ka yi waƙar?
ƊANSARAKI: A’a, sai da muka taho, ana ta yawo a dawa. Sai wani tsohon maharbi ya ba ni mamaki. In an zo cikin kufai sai ya ce, “A tona nan.” Idan an tona sai a ga gawayi na ƙirya, shaidar kan iyakar. Wai tun yana yaro ya ga iyakar! Muka turo garin ‘Yandoto kudu. Ban tashi tsiya ta ba sai da muka sauka! An tara karuwai, can sai suka ji waƙa ta. Sai murna suke, sun ji ina cewa, “Su wane murna ta koma ciki…” Sai wani ɗandoka ya je ya gaya ma ‘Yandoto (Hakimin Tsafe) abin da nake cewa. Ya ce, “Gobe a zo min da kai nai!” Aka zo aka gaya min, aka ce kar in je. To daga nan ban sake sa ‘Yandoto a ido ba.
SHEME: Shi marigayi ‘Yandoton Tsafe jam’iyyar NPC yake?
ƊANSARAKI: E, shi ne Sarkin Yaƙin NPC ma. To saboda wahalar da NPC ke ba mutane, sai na riƙa ɓoyewa. Wata rana ‘Yandoto ya zo nan ‘Yankara, sai na aika aka ɗauko min kukuma ta na shiga waƙa, har ya ba ni fam uku, ya ce, “Ka taho Tsafe.” Na je, ya ba ni kwakwata da hula da sauran su. Muka shirya dai daga nan.
SHEME: Su wanene manyan iyayen gidan ka?
ƊANSARAKI: A wancan lokacin ba ni da wani babban ubangida a nan Nijeriya kamar Sardauna da ministocin shi, musamman ma dai Minista na Shari’a, Mamman Nasir Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi na yanzu. Amma Wamban Daura Muhammadu Bashar bai ɗauke ni da girma sosai ba, a yanzu ma ba garin da na tsarga kamar Daura. Ban taɓa samun wani abin kirki a can ba, sai lokacin da Bashar ya auro ‘yar Sarkin Katsina.
SHEME: Hajiya Kilishi?
ƊANSARAKI: E, ita. Na fi ƙaunar in je ƙauyuka da in je Daura! Amma Nasiru har yanzu muna tare. In yau ɗin nan na je Malumfashi, yana ji na zo zai ba da kuɗi da riguna a kawo min. Ko kwanan nan ya yi min alheri. In ba su Mamman Shata ba babu wani maroƙi mai jin daɗin Sarkin Daura, sai ko Musa Ɗanƙwairo kafin ya rasu.
SHEME: To shi Shata kana shiri da shi sosai ko?
ƊANSARAKI: A’a, sai dai muna gaisawa yanzu. Saboda ni dai ban son abin da zai ɓata min rai.
SHEME: Kuna gaisawa da shi?
ƊANSARAKI: E to, sai dai in wuri ya ƙure.
SHEME: Wane abu ne ya faru a tsakanin ku?
ƊANSARAKI: Sai dai halin sana’a da mutane masu yi mana haɗe-haɗe. To duk sun mutu; akwai wasu da ake ce ma Safce da Tsangaya. Wato zuwan mu Damagaram ɗin nan aka haɗu, ga Shata ga Ɗansaraki. Sai mutane suka baro Shata suka yo waje na, ana cewa, “Ga Ɗansaraki!” Tun daga nan ba mu daɗi sosai.
To wata rana na dawo daga Askira na zo Kano, lokacin da Shugaba Ibrahim Babangida ya je can, a nan ma na ga ba mu jin daɗi sosai. Kai, ko a Daura ɗin ma ba wanda ya matse ni sai Shata, saboda shi ke da fada a wurin Sarki. A da, Shata ba shi da wani mai ji da shi kamar ni. Duk waɗanda ba su son shi na waƙe su da zambo. Sai suka zo suna suka ta a wurin sa.
A wani biki a Funtuwa ya yi min wani wulaƙanci. Akwai wani ƙato da ake ce wa Bakadaɗi, ya zo ya ce, “Ba wanda zai yi wa Ɗansaraki wulaƙanci!” Aka sa ni a mota na bar wurin.
Kuma shi Shata mutum ne mai son yi ma mutane habaici (a waƙa). Ka san yana cewa a Bakandamiya ya “ƙyale banjo da kukuma wargin yara ne.” Sai Ahmadu Doka ya ba shi amsa ya ce, “Kukuma ba ƙanƙanin kiɗa ne ba”. To, Ahmadu Doka amini na ne.
SHEME: Amma kai ba ka ba Shata amsa ba?
ƊANSARAKI: Me zan ce? Ai ba daidai ba ne. Yanzu ka ga ban ji daɗin wasu abubuwa da suka faru tsakanin shi da wasu ba. Wata rana a Maigana, Shata na cikin wani ɗaki, sai marigayi Mammalo ya ce, “Ko lahira kada Allah ya haɗa ni da Shata.”
Ka san lokacin da Mammalo ya mutu, an ce wai ja da manya ya kashe shi. To ni ban yarda Shata na iya yi wa mutum makaru ba; ban san ya taɓa zuwa wurin wani malami da neman taimako ba.
Wata rana muka haɗu da Musa Ɗanƙwairo a gidan Alhaji Baƙo Kontagora, a Kontagora. Sannan Shata yana shari’a da mutanen Birnin Gwari a kan wasu gonaki, ina cewa (a waƙa), “Ƙwairo ka sha ribar kiɗa, ka bar wasu na rigima da duwatsu!” Ɗanƙwairo ya ba ni riga.
A nan na fara maida martani ga Shata. Ina ganin ya ji. Wata rana na je gidan shi a Funtuwa. Ya fito, na ce, “Ran ka ya daɗe!” Sai ya leƙo, ya ce, “Sannu,” ya shige gida.
SHEME: To Alhaji Ɗansaraki, mutane za su so su ji abin da za ka ce game da hasashen da wasu ke yi cewa wai Shata ne ya kashe maka murya, har ba ka iya yin waƙa, wai yana kishi da kwarjinin ka a waƙa.
ƊANSARAKI: Ni ban yarda da wannan ba. Ni wallahi ban yarda da cewa Shata yana iya yi wa wani wani abu ba, don ba zai iya yin haka ba. Ka san sai da na shafe shekara goma ma waƙar buga-buga nake yin ta. A ƙasar Sakkwato, har Ƙwanƙwanbilo na je wajen aljanin Ƙwanƙwanbilo neman magani da zai sa murya ta ta sake buɗewa. Har Ƙwanni a Nijar wurin arnan nan na je. Ina fa iya yin magana, amma in na zo waƙa sai in kasa!
SHEME: Su malamai da bokayen da kake zuwa wajen su, ba su ce maka ga dalilin da ya hana muryar ka fitowa ba?
ƊANSARAKI: Akwai wani babban malami a Mayanci, ƙasar Sakkwato, wanda muka je wurin shi ya yi min istahara. Ya ce shi dai bai ga komai tare da ni ba. Amma ya ba ni rubutu ya fi ƙafa miliyan! Da jarka na riƙa zuwa ina kai mashi, sai bayan kwana bakwai in koma.
SHEME: Daga nan ne aka dace?
ƊANSARAKI: Wallahi ban sani ba. Ni dai yanzu ina yin waƙa da roƙo. Yanzu haka ina neman taimako. Ko jiya (8 ga watan ɗaya, 1993), wani malami ya zo nan ya ce zai kawo min taimako.
SHEME: A’a, to ai da muna hangen cewa tunda ga shi ka manyanta, sai ka yi ritaya daga waƙa, ka bar wa waɗansu! To ga shi kuma har yanzu kana da burin a dama da kai?
ƊANSARAKI: E, waƙa kusa nake da barin ta. Ina son in yi ritaya. Ina son daga nan zuwa baɗi, in na samu kuɗi zan yi zagaye zuwa wasu wuraren Nijeriya in yi masu bankwana. Ni kai na ina son in bari. Rabo na da in goga kukuma ya kai shekara uku.
SHEME: Ashe dai an daɗe. To su wanene a cikin ‘ya’yan ka kake so su gaje ka?
ƊANSARAKI: Ban son wani ya gaje ni. ‘Ya’ya na maza sun kai kusan goma sha uku. Ko yanzu ina da wani ɗa a ciki, ban san ko wane iri ba ne. Ina ganin yadda ake wulaƙanta mawaƙa, saboda haka ba ni fatan ɗan da na haifa ya yi roƙo. Abu ne ya ratso wani zamani yanzu, ban da wulaƙanci babu abin da ake son yi. In dai wata sana’a ce, in ba sata ba ce, su je su yi.
SHEME: Yanzu wace sana’a aka sa a gaba?
ƊANSARAKI: Yanzu daga noma, to sai ko ɗan roƙo haka, tunda ban cewa ban yi. Ko kwanan nan ina son in je wajen shugaban Ƙaramar Hukumar Kurfi.
SHEME: To iyali fa, kana da nawa?
ƊANSARAKI: Da, ina da mata huɗu masu haihuwa, ɗaya ta haifi ‘ya’ya shida muka rabu. Wata ta haifi ‘ya’ya biyu muka rabu. Yanzu akwai mai ‘ya’ya takwas. Wata ta yi biyu mun rabu. Akwai mai ‘ya’ya takwas, wata ‘ya’ya shida.
SHEME: ‘Ya’yan ka sun kai ashirin?
ƊANSARAKI: Sun haura ashirin.
SHEME: To za mu dakata a nan, mun gode.
* An wallafa wannan hirar a mujallar Rana, ta kamfanin Hotline, Kaduna, cikin Janairu 1993, lokacin ina riƙe da muƙamin Editan mujallar.