SUNA: Masoyi Zaki
MARUBUCIYA: Nabeela Ibraheem Khaleel
SHEKARA: 2006
SHAFUKA: 65
FARASHI: Babu bayanin
LABARIN: “… Yadda za ki gane tauraruwarki shi ne, ki kalle su gaba ɗaya, ki ƙura musu ido. Duk wadda kika ji ta yi daidai da ke ruhi da jiki, wacce kika ji ta yi maki kyau, ta kuma dace da ke, to ita ce tauraruwarki. Yanzu ki kalle su ki gano taki ki nuna mani ita!”
Inno ta kalli taurarin nan tsaf. Zuwa can sai ta yi farat ta nuna wata daga can gefe, ta ce, “Yaya, ga ta nan!”
Adamu ya kalli wadda ta nuna ɗin, sa’annan ya yi murmushi, ya nuna wata tauraruwar, ya ce, “Ni kuma kin ga tawa nan kusa da taki.”
Ita ma ta yi murmushi, ta ce, “Allah kuwa, Yaya?”
Ya sumbanci goshinta, ya ce, “Allah kuwa, ƙanwata!”
Sa’annan suka yi dariya tare da rungume juna. A daidai nan kuma sai iska mai ƙarfi ta taso, aka tsuge da ruwa kamar da bakin ƙwarya.
Adamu ya yi wuf ya sungume ta, suka shige cikin bukkar da ya gina a dajin nan, inda a karo na farko suka ɗanɗani daɗin madarar soyayya.
An yi wa Inno da ɗan’uwanta Adamu auren zumunci, auren soyayya. Sun fara shan daɗin auratayya sai wani abin baƙin ciki ya faru: Adamu ya ɓace. Kowa ya zaci ya mutu, in ban da Inno, wacce ta haƙiƙice da cewa yana nan da ransa cikin dajin nan na Kwatarkwashi. Shin me ya gama Adamu da wani zaki wanda ya banke shi lokacin da ya je dajin domin ya taimaka masa?
MARUBUCIYAR: Nabeela Ibraheem Khaleel ‘yar asalin Katsina ce. Ta yi makarantar sakandare a GGSS Kankiya (1992-1998), sa’annan ta wuce Jami’ar Bayero, Kano, a cikin shekara ta 2000, inda ta fara karatun share fage a fannin Kimiyya. Daga bisani tayi karatun digiri a fannin Kimiyyar Laburare da ta Halittu (Library Science and Biology), a Jami’ar Bayero, ta kammala a cikin 2005. Nabeela ta yi fice a matsayin marubuciyar musamman a mujallar Fim, inda take gabatar da filin “Daga Zuciya”. Masoyi Zaki shine littafinta na farko da aka buga.

![]()

