• About
  • Contact
Sunday, July 27, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Rasuwar Tsigai da Danwanzan

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
April 11, 2007
in Da Hausa
0

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

Fitattun ‘yan fim guda biyu, Husaina Ibrahim Gombe (Tsigai) da Shu’aibu Mohammed (Danwanzan), sun rasu a ranar Lahadi, 8 ga Afrilu, a wani mummunan hatsarin mota. Su na dawowa ne daga Legas, inda aka gayyace su su ka yi wasan gala, sun shigo mota Toyota Hiace mai zuwa Kano. Sun kusa Kaduna (kilomita 22) sai direban ya yi zaton kila akwai ‘yan fashi da makami a can gaban su, su na tare mutane masu shiga Kaduna a daidai lokacin. Wajen karfe 4:30 na asuba ne. Sai direban ya yi u-turn ya koma daya hannun hanyar (mai zuwa Abuja daga Kaduna). Ai kuwa ba a dade ba su ka yi taho-mu-gama da wata tirela wadda ta dauko shanu daga Maiduguri za ta kai Anacha.

Mutane 16 ne a bas din. A cikin su, 11 su ka mutu – mata 4, maza 6, da karamin yaro 1. Mutum 5 sun tsira. Direban bas din, wani Bakano, ya rasu. Amma direban tirelar bai samu ko kwarzane ba. Hasali ma dai a jiya lokacin da mu ka tuntubi ‘yan sanda, ya na can cikin garin Kaduna ya na yawon sa abin sa.

An rufe Tsigai a Kaduna (a makabartar da aka rufe jaruma Balaraba Mohammed a Maris 2003). Shi kuma Danwanzan, an kai shi gida Kano aka rufe shi a can.

Tsigai ta na da ‘ya’ya biyu (Anas da Nafisa), Danwanzan ya na da ‘ya’ya 4. Maaifiyar Tsigai ta rasu, amma baban ta ya na nan da ran sa a Gombe. Iyayen Danwanzan duk su na nan da ran su a Kano.

Tsigai da Danwanzan sun yi fice ne a bangaren wasannin kwaikwayo na ban-dariya, masu nuna rayuwar talakawa ko ‘yan kauye. Tsigai ita ce matar Ibro (Rabilu Musa Danlasan) a wadannan wasannin. Hasali ma dai ita ce ta saka shi cikin wasan dirama, har ya zo ya zama shugaban kungiyar su ta dirama (Hamdala Drama Group). A wasannin, Tsigai ta kan fito a matar Ibro mafad’aciya, wadda ba ta gode dukkan abin da mijin ta ya ba ta, amma kuma daga karshe sai ta zo ta yi da-na-sani.

Lokacin da labarin rasuwar tasu ya bulla shekaranjiya waccan, ina Kano. Al’amarin ya girgiza mutane matuka, musamman ‘yan fim da kuma masoyan wasannin Ibro. Na garzayo Kaduna don sake shirya mujallar Fim, wadda har za ta fito a ranar da aka yi rasuwar. Nan da nan aka sake buga wata sabuwa, aka saka mamatan biyu a bangon mujallar.

Allah ya jikan Tsigai da Danwanzan, amin.

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Previous Post

Damina ta iso Kano

Next Post

To make or break

Next Post

To make or break

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d