• About
  • Contact
Monday, July 28, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

ALA: Korafin Marubuta Mata

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
July 9, 2009
in Da Hausa
0
ALA: Korafin Marubuta Mata
Rahma Majid

A yau din nan marubuta biyu mata sun yi magana kan tsare Amiunu Ala da aka yi. Ta farkon su ita ce fitacciyar marubuciyar nan Rahma A. Majid (wadda hoton ta yake kan shafin nan) sai kuma Malama Maryam Ali Ali, wadda ita ce sakatariyar kudi ta Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA). Sun yi magana ne a Majalisar Marubuta ta Yahoogroups. Ga abin da su ke cewa:

RAHMA A. MAJID:
DON ALLAH KADA MU YARDA!!!

“Lokaci ya yi da zamu hada karfi da karfe ta kowane sashi na adabi mu yaki gwamnatin
zalunci da manufofin ta. Kullun sai sharhi muke kan abinda muka rigaya muka sani kan manufofin hukumar zaluncin amma mun kasa jajircewa mu yi aiki kai tsaye. An kafa hukumar tace-tace domin ta tato duk wanda zai yi amfani da ganga, majigi, ko alkalami ya tona asirin manufofin ta na murdiya. Na jima da aka sinsina min haka tun a lokacin da ba a kafa hukumar karara ba inda wasu masu daure da irin zanin ta suka yi ikirari a jaridar New Nigeira cewa sun ba ni tallafin karatu sanda nake jami’a da sunan littafi na bai dace da fiqihu ba(don tsananin jahilcin kasa bambance shara’a, adabi da fiqihu). Amma a wancan lokacin Rahma wadda take bakuwa bata sami wanda ya tayata hangen abinda zai faru a yau ba har sai da yayi nisa.

“To! Ko a yanzu in an mike ba a yi laifi ba. Kira daya da zan yi na neman hadin kan uudabaù shine a yi wa Allah a yi wa adabi, kada a bar wannan fafitika ta zamo ta neman a saki Ala kawai. Don Allah ko da an wanke shi mu katange junan mu baki daya daga sabon cin fuska da dauki-dai-dai da wannan hukuma ke mana a sanadiyyar son girma, ko neman gindin zama ko rashin hadin kai, ko hassadar mu ta tsaga wa kadangare bango.

“Hakika a watan Nov. insha Allahu na shirya dawowa majalisa with full force, amma saukar da wannan sako ya yi a gadon bayan zuciya ta ya sa dole na karya doka ta.”

MARYAM ALI ALI:
“Salam,
“A gaskiya yadda Ala ya bauta ma wannan gwamnatin da baiwar sa, abin ya zama abin
tsoro in har za a yi mai haka, to lallai kam, abin da razanarwa, kowa ma ya shafa
ma kansa da gemun sa ruwa.”

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Previous Post

Kano Censorship: Aminu Ala Arrested, Jailed

Next Post

Aminu Ala released, but…

Next Post

Aminu Ala released, but...

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d