• About
  • Contact
Sunday, July 27, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Ba gyara Rabo ya zo yi ba

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
August 4, 2009
in Da Hausa
0

A gaskiya, ko kadan ba da nufin gyaran harkar fim Malam Abubakar Rabo ya zo ba. Ya dai zo yin gyaran gangar Abzinawa ne – wato kid’an ganga da lauje! Abin da ya sa na fadi haka shi ne, kusan dukkan muhimman matakan da Rabo ya dauka a kan wannan harkar, ya dauke su ne da nufin durkusar da harkar. Ga hujjoji na:

1. Tun daga ranar farko ta kama aikin sa, ya dukufa wajen b’ata sunan ‘yan fim. Ba wai a yau ya fara ba.

2. Duk wasu shawarwari nagari da ‘yan fim din da sauran jama’ar gari su ka ba shi na yin gyaran da ya dace, bai dauka ba.

3. Duk wani zaman shawara da ‘yan fim su ka yi da shi, aka zartar da shawarwari, bai taba aiwatar da ko daya ba; sai ma ya rika yi masu yankan baya bayan an tashi daga zaman.

4. Rabo ya zagaya jihohin Arewa da dama inda ya bukaci magabatan jihohin da su zartar da kudirorin hana yin sana’ar fim.

5. A kan d’an k’aramin laifi, Rabo ba ya tausaya wa d’an fim, sai kurum ya sa a kulle shi ko kuma kotu ta yi masa babbar tara.

6. Ya sa an kulle ‘yan fim din da ba su aikata laifin komai ba, musamman Hamisu Iyan-Tama, don kurum ya fashe wani haushi nasa na son rai.

7. Har yau bai karbo wani agajin kudi daga gwamnati ya raba wa ‘yan fim ba don inganta sana’ar su ko kuma ci gaba da yin sana’ar.

8. Ya dauki masu shawara tagari a matsayin abokan adawa ko ma abokan gaba, duk da yake su ba hakan su ka dauke shi ba.

9. Ba ya yarda ya tafi tare da masu ba shi shawara, sai ‘yan kore wadanda ke gaya masa abin da kunnen sa ya ke so ya ji.

10. A kullum kokarin sa shi ne ya gano hanyar da zai bi ya nakasa ‘yan fim da sana’ar su, ba hanyar da zai taimaka masu su ci gaba ba.

11. Duk wata bita da ya shirya da nufin wai gyaran fim, idan ka duba da kyau sai ka ga da biyu aka yi, ba wai an yi ba ne don gyara sana’ar. Domin ko su wadanda ake zaba su shiga bitar, sai an tsamo ‘yan kore, ‘yan a-bi-Yarima- a-sha-kida, sannan a yi da su.

12. Yau shekarar Rabo biyu a kan mulkin, me ya kulla na kawo gyara?

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Previous Post

Mohammed Yusuf – Nigerian Taliban Leader

Next Post

Police Arrest Kano Censors Board DG

Next Post

Police Arrest Kano Censors Board DG

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d