Shugaban Hukumar Hukunta ‘Yan Fim ta Jihar Kano, Malam Abubakar Rabo, ya cika alƙawarin sa na cewa sai ya ɗaure ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Kano, wato Malam Bashir Ɗandago. Domin kuwa a yau dai jami’an hukumar sun kama shi, sun gurfanar da shi a gaban kotun hukunta ‘yan fim.
Haka kuma an kama wani matashi mai suna Kabir Maulana.
Laifin da ake tuhumar su da shi, shi ne: wai sun saki faifan waƙar ‘Tsangayar Kura’ (mai ɗauke da waƙar nan ta “Hasbunallahu” ) bayan hukuma ta hana sakin faifan a Kano.
A kotu, su Ɗandago sun ce, “Not guilty.” To amma Alƙali Mukhtar Ahmed, kamar yadda ya saba yi, ya hana belin su, ya tura su gidan yari. Ya ce a dawo ran Litinin a ci gaba da magana. Manufa ita ce, su ma dai sun yi zaman jarun.
Ga waɗanda su ka saurari waƙar “Hasbunallahu, ” za su tuna da cewa akwai muryar Malam Bashir Ɗandago a ciki. To, da ma kaska ta na da haushin kifi.
Shi dai Ɗandago, ya yi fice ne a fagen waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAW), wato waƙoƙin bege. A cikin 2009 ne aka ji muryar sa a waƙar “Hasbunallahu, ” wanda hakan ya ƙara wa waƙar ƙarfi da karsashi. A wata hira da ya yi da ‘yan jarida kwanan baya, Ɗandago ya ce ya yi waƙar ne domin ya taimaka wajen murƙushe zaluncin da ake yi a Kano.
Kwanan nan kotun ta su “Asabe Murtala” ta ɗaure jagaban waƙar “Hasbunallahu, ” wato Malam Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA), a gidan yari. Za a ci gaba da shari’ar sa a makon gobe.
Majiya ta ce gurfanar da Rabo da ‘yan fim su ka yi a ofishin ‘yan sanda na Metro kwanan nan ya ƙara hayaƙa malamin, har ya sha alwashin yin ramuwa.
Majiyar ta ce don haka dai kwanan nan hukumar za ta kama wasu mata daga cikin ‘yan fim, musamman mawaƙan da ke cikin su. Sannan majiyar ta ce ana nan ana haƙon wani ɗan fim, tare da shan alwashin cewa a gidan yari zai yi azumin Ramadan.
“Zalunci ba zai ɗore ba” – Maryam A. Baba, a waƙar “Rabo, Rabo”