• About
  • Contact
Sunday, July 27, 2025
  • Login
Ibrahim Sheme
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings
No Result
View All Result
Ibrahim Sheme
No Result
View All Result
Home Da Hausa

Sai Bango Ya Tsage…

IBRAHIM SHEME by IBRAHIM SHEME
February 10, 2011
in Da Hausa
0
Hatiman jam'iyyun PDP, ACN, da CPC
Hatiman jam'iyyun PDP, ACN, da CPC

Hatiman jam'iyyun PDP, ACN, da CPC

Idan har wannan makon ya ƙare jam’iyyun adawa na siyasa a Nijeriya ba su haɗu su ka fito da ɗan takara guda ɗaya da za su shigar a zaɓen watan Afrilu ba, to kawai mu ɗauka cewa duk a cikin su babu wanda zai iya doke Dakta Goodluck Jonathan – ko an yi zaɓe ba maguɗi ko kuma an yi zaɓe da almundahana. Abin da ya sa na yi wannan kintacen shi ne amannar da na yi cewa a yanzu kam, kawunan waɗannan jam’iyyu da ke kiran kan su jam’iyyun siyasa duk a rarrabe su ke a kan batun yin wani gagarumin shiri don zaɓen, kuma babu wata ƙwaƙƙwarar alama da ke nuna cewa za su iya zama su baje komai a faifai a cikin mako ɗaya.

Yanzu hankalin jam’iyyun a tashe ya ke a daidai lokacin da wa’adin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na su kawo sunayen ’yan takarar su ya kusa cika. Dalili shi ne fargabar da ta cika zukatan jam’iyyun ganin cewa yanzu Jonathan ya samu tikitin tsayawa takarar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, wanda ya ƙara masa ƙarfi fiye da yadda ya ke kafin a yi zaɓen fidda gwani na jam’iyyar mako uku da su ka gabata, kuma akwai alamun lallai zai iya lashe zaɓen da za a yi a Afrilu. Yanzu akwai bayyanannun alamu masu nuna cewa idan har jam’iyyun adawa ba su haɗu su ka mara wa ɗan takara ɗaya baya ba, to hamɓarar da Jonathan da kaifin ƙuri’a zai kasance tamkar ɗaukar Dala ba gwammo.

Akwai tarurrukan da ake ta yi don tabbatar da an cimma hakan, to amma har yanzu babu wanda ya haifar da ɗa mai ido. A ranar Juma’a ta makon jiya, jaridu sun ruwaito labarin wani taro da aka yi “a asirce” tsakanin Malam Nuhu Ribadu na jam’iyyar ACN da Janar Muhammadu Buhari na CPC a gidan shi Buharin da ke Kaduna. An ce an yi taron ne da nufin fito da hanyoyin da za a bi a ƙwace mulki daga hannun Shugaba Jonathan. Wannan tunanin ya yi daidai da ƙoƙarin da ake ta yi na ganin cewa mulki ya dawo arewa a zaɓe mai zuwa.

To amma ko wannan yunƙurin zai yi nasara kuwa? Kai mai karatu, ka ma fi ni sanin amsar. A haƙiƙanin gaskiya, jam’iyyun adawa na ƙasar nan dai duk jam’iyyun son rai ne. Kowane ɗan adawa so ya ke a ce shi ne a saman sauran, shi ya sa bai yarda da duk wata yarjejeniyar a haɗu a fidda jaki daga duma ba in ban da wadda za ta ba shi karsashi. Duk wani taro nasu ya na ƙarewa ne a fayau domin duk wanda ya je taron ya na zuwa ne da ƙoƙon barar don-Allah-wane-ka-bar-mani.

Ba sai mun wahala ba wajen gano abin da ke janyo hakan. Ita siyasar adawa da ake yi a Nijeriya a yau, ba irin ta da ba ce. Yanzu babu ɓurɓushin aƙida a jam’iyyun, wanda hakan ya sa su ka kasance tamkar ’yan biyu masu kama ɗaya in ban da ta wajen sunayen su. Amma su kuwa jam’iyyun zamanin da, lokacin da duniya na kwance lafiya, wato jam’iyyun Jamhuriya ta Farko irin su NCNC, NEPU, UMBC, da AG, da na Jamhuriya ta Biyu irin su UPN, NPP, GNPP, da PRP, an kafa su ne bisa wata aƙida. Duk mutanen da je jagorantar su ko su ke cikin su mutane ne da su ka kafe kan abin da su ka yi amanna da shi, ba wai don su na tunanin cewa amannar su ɗin za ta kawo masu dukiya ko suna ba, a’a sai domin sun yarda babu kokwanto da cewa hakan ita ce hanya mafi sahihanci da za a bi a gyara al’umma kuma a gina ƙasa.

Gidan yanar Wikipedia da ke intanet ya bayyana cewa aƙidun siyasa sun kasu ne gida biyu: 1. Buri: Wato yadda ya kamata al’umma ta rayu ko a tsara ta, sai na 2. Gwadabe: Wato hanya mafi dacewa da za a bi a cimma shi wannan burin. Shi ya sa a ƙasar Amurka za ka taras da cewa mutum ko dai ya na jam’iyyar Democrat ne ko kuma ya na jam’iyyar Republican; a Birtaniya kuma ko dai ka na jam’iyyar Labour ne ko ka na ta Conservative. Ban da waɗannan, babu wasu manyan jam’iyyu, illa wasu ƙananan jam’iyyu da ke gefe guda don kula da mutanen da su ke ganin ra’ayin su ya bambanta da na waɗannan ɗin.

Ka lura, ita aƙidar siyasa kamar addini ce: mutum ba ya ficewa don kurum kwaɗayin wata ganima da ya hango. Mutane su kan haɗe ne saboda sun yi amanna da wasu muradai da aka tsara, wanda shi ne ke sa su su yi wani abu a siyasance tare da yin aiki da kundin aƙidar su. Ba su haɗuwa don kawai a taru a ci abin ƙwalamar da ke kan tebur ko don a yi ginsamin abin jefawa cikin aljihu.

A yau, labari ya bambanta. Sai ka ga gungun mutane su na ta ninƙaya a tekun siyasa, su na sanye da bajen wai su ’yan siyasa ne. Duk ƙibar su, mayunwata ne kawai, kuma yunwar da su ke ji (ta giyar mulki ko ta naira) ita ce ke tunzura su, ba wai aƙida ba. Shi ya sa ba mamaki ka ga yadda ’yan siyasar da su ka yi suna a matsayin ’ya’yan wata jam’iyya, an wayi gari sun yi tsalle sun auka wata jam’iyyar, ko da kuwa sun yi shekaru su na ɓata ta. Ana kiran wannan halayyar wai sauyin sheƙa, kuma ’yan siyasa da dama a wannan ƙasa tamu su kan yi hakan cike da alfahari, kuma iya ƙarfin su, a yayin da kuma su ke borin kunyar cewa wai an ƙi jinin su ne a ɗaya jam’iyyar. Misalin irin waɗannan ’yan siyasa bai da adadi. An zaɓi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin gwamna a ƙarƙashin PDP a shekarar 1999, to amma lokacin da wasa ya yi tsami tsakanin sa da Obasanjo sai ya kafa jam’iyyar AC, wadda ta lashe zaɓe a Jihar Ikko. A yau, ya dawo PDP, jam’iyyar da ya so ganin bayan ta, har ga shi ya nemi zama ɗan takarar ta na shugabancin ƙasa. Alhaji Aminu Bello Masari babban ɗan PDP ne, wanda shi ne kakakin Majalisar Wakilai na tsawon shekaru. A yau, ya na takarar gwamna a jam’iyyar CPC a Jihar Katsina. Dora Akunyili ma ’yar PDP ce wadda ta riƙe muƙamin ministar yaɗa labarai da sadarwa a ƙarƙashin shugabannin ƙasa har biyu; a yau, ’yar takarar zama sanata ce a ƙarƙashin jam’iyyar APGA a Jihar Anambara. Dakta Abba Sayyadi Ruma, wanda a da babban ɗan PDP ne, inda har ya taɓa zama sakataren gwamnati a Jihar Katsina kuma daga bisani ya zama ministan aikin gona, yanzu ya na takarar gwamna a ƙarƙashin CPC. Shi ma Sanata Adamu Aliero jagora ne a PDP a da, amma yanzu ya na takarar zama sanata a ƙarƙashin CPC a Jihar Kebbi. Malam Nuhu Ribadu wani jigo ne a gwamnatin PDP a zamanin Cif Olusegun Obasanjo, amma yanzu ɗan takarar zama shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin ACN. Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa ya zama gwamnan Sakkwato ne a ƙarƙashin ANPP, amma ya tafi ya kafa jam’iyyar DPP har ya yi mata takarar zama shugaban ƙasa a zaɓen 2007, amma a yau ƙusa ne a ACN, inda kwanan nan ya nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa. Kai, lissafin bai kammaluwa!

A yanzu waɗannan mutanen da ire-iren su su na nuna mana cewa su wasu mahajirai ne da aka cuta a baya. To amma kowa ya san cewa sun canza sheƙa ne don kawai an tokare su a jam’iyyun su na baya, kuma za su iya komawa inda su ka fito da zarar sun samu mulki ko kuma sun ga babu sa’ida a inda su ka zo. Dalili kuwa, su a wurin su ai siyasa ba addini ba ce. Sai ka ce ba su ma san ma’anar kalmar ‘aƙida’ ba. Shi ya sa su ke watangaririya daga wannan jam’iyya zuwa waccan ba tare da jin kunya ko tsoro ba, sai ka ce ƙudan zuma mai neman furen kallo don ya yi ƙoto. Haƙiƙa, wannan shi ne babban dalilin da ya sa haɗuwar jam’iyyun adawa don su kada shugaban ƙasa da ke kan gado ya ke da matuƙar wuya a ƙasar nan, wai gurguwa da auren nesa. Bari mu gani a cikin ’yan kwanakin nan idan a siyasar wannan zamanin za su sauya hali duk da yake Hausawa sun ce hali zanen dutse, ba ya kankaruwa.

—-

An buga a LEADERSHIP HAUSA

Loading

Share this:

  • Facebook
  • X

Like this:

Like Loading...
Previous Post

As Another Pharaoh Falls…

Next Post

The Meaning Of People’s Power

Next Post
The Meaning Of People’s Power

The Meaning Of People’s Power

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bature Tanimu Gagare: Fighting, Not Just With His Pen
  • Goron Sallah
  • Wale Okediran @ 70: Tribute to a Workaholic Writer
  • ‘Found in Translation: Writing in Indigenous Languages’
  • Motherland at 64

Recent Comments

  1. UMAR IBRAHIM ABDULLAHI on Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a Ranar Arba’in
Ibrahim Sheme No. 19, Chelsea Chibuzor Street, Katampe District Abuja, FCT Nigeria 📞 +234 0809 400 0071 (text) ✉️ ibrahimsheme@gmail.com
  • Home
  • About
  • Contact

© 2023 Ibrahim Sheme

No Result
View All Result
  • Home
  • Bookworm
  • Book Publishing
  • Media
    • News & Events
    • Gallery
  • Blog
    • Columns
      • Blueprint
      • Leadership Weekend
    • Da Hausa
    • Online Musings

© 2023 Ibrahim Sheme

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d