Haɗarin jirgin ƙasa na Langa-langa yana ɗaya daga cikin haɗurra mafi muni a tarihin safarar jiragen ƙasa a Afrika. Haɗarin Langa-langa ya faru ne a ranar 16 ga Fabrairu, 1970 kusa da ƙauyen Langa-langa da ke Ƙaramar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ta yanzu, jim kaɗan bayan kammala Yaƙin Basasar Nijeriya.
A wancan lokaci, Hukumar Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC) tana gudanar da jiragen fasinja da na jigilar kaya tsakanin Arewacin Nijeriya da yankin Gabas. Tafiya ta jirgin ƙasa ta bunƙasa sosai domin tana da arha kuma ana ganin ta fi ta mota aminci.
BALA’I A LANGA-LANGA
Jirgi ne ya tashi daga Jos a kan hanyar sa ta zuwa Lafiya, hedikwatar Jihar Nasarawa a yau. Daga Lafiya, zai zarce ne zuwa Makurɗi sannan ya gangara zuwa Gabashin Nijeriya. Da ya zo tashar garin Gudi, ya ɗan yada zango domin masu sauka a nan su sauka, wasu fasinjojin kuma su hau.
Jirgin, mai amfani da man dizal, ya cika maƙil da fasinjoji, saboda an ba da hutun Babbar Sallah, mutane suna hanyar zuwa bikin Sallah.
Jim kaɗan bayan jirgin ya bar Gudi, sai ya isa wata muguwar kwana kusa da ƙauyen Langa-langa. Kwatsam, sai kan jirgin, ya goce daga kan layin dogo a daidai kan kwanar. Kafin ka ce kwabo, gaba ɗaya kan jirgin tare da taragai huɗu na farko suka antaya cikin rami mai zurfin kusan mita 25.
Haɗarin ya haddasa mummunar ɓarna, inda wasu taragai suka murɗe gaba ɗaya, wasu kuma suka kama da wuta. Fasinjoji da dama suka mutu nan take, wasu suka ji mugun rauni. Da yawa suka maƙale cikin ƙarafan da suka murɗe, ga kuma kaya sun danne wasu.
Har yau babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu, saboda bayanan lokacin ba su cika ba. Yawancin rahotanni sun yi hasashen cewa aƙalla mutum 150 ne suka mutu, wasu bayanan kuma suka ce mutum 80, har ma 400 ko fiye ne suka mutu.
LABARIN BAN-TAUSAYI
Ɗaya daga cikin labarai masu ban-al’ajabi da taɓa zuciya game da haɗarin shi ne abin da wasu fasinjoji suka ji bayan jirgin ya faɗi. A cewar su, abin da ya fi firgita su shi ne a cikin duhun daren, sun riƙa jin hargowar waɗanda suka samu munanan raunuka suna roƙon don Allah a kawo masu taimakon gaggawa. Muryoyin mutanen suna raguwa a hankali yayin da lokaci ke tafiya, wasu kuma suna daina magana gaba ɗaya.
Wani da ya tsira daga haɗarin ya ba da labarin cewa: “A cikin duhu muna jin mutane suna kiran ‘ku taimake mu!’ daga cikin taragogin da suka murɗe. Wasu suna addu’a, wasu suna kuka.” Wani wanda ya tsira ya ce wannan shi ne abin da ya fi tsoratar da shi a rayuwar sa, domin ba zai taɓa mantawa da muryoyin waɗanda suka maƙale suna roƙon a agaje su ba.
MUHIMMANCI A TARIHI
A duk Afrika, ana kwatanta faɗuwar jirgi ta Langa-langa da wadda ta ya fi shi muni, wato wadda ta faru daga baya a ranar 10 ga Yuni, 2001, a yankin Uige na ƙasar Angola. A haɗarin, bam ne jirgin ya taka, irin wanda ake dasawa a ƙasa a lokacin yaƙin basasar Angola. Bam ɗin ya fashe, wanda ya sa jirgin ya faɗi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 250 tare da raunata wasu da dama.
Dangane da haɗarin Langa-langa, an riƙa yin zargi iri-iri. Wasu sun ce maƙarƙashiya ce wasu ‘yan Biyafra suka shirya, wai yana da alaƙa da Yaƙin Basasa da aka yi. Jim kaɗan da faruwar haɗarin, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike na musamman kan haɗarin da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a inganta tsaron jiragen ƙasa a Nijeriya.
RASHIN ISASSHEN AGAJI KO CETO
Ayyukan ceto sun kasance masu matuƙar wahala a wurin haɗarin saboda ƙarancin kayan aiki, ga shi kuma wurin yana da nisan gaske da gari, kuma jirgin ya ragargaje ƙwarai.
An ce likitoci sun riƙa yanke wasu sassan jikin fasinjoji – kamar ƙafafu ko hannaye – domin su samu damar fito da su daga cikin mushen jirgin. An kwashi wasu daga cikin waɗanda suka tsira zuwa asibiti a mota, amma ɗaya daga cikin motocin ta faɗa cikin wani kogi, wanda hakan ya haddasa ƙarin mutuwar wasu mutane. Hakan ya sa abin da ya faru ya zama bala’i sau biyu, wanda ya ƙara yawan waɗanda suka mutu.
Wasu ganau sun ce ma’aikatan ceto sun kasa fitar da mutane da dama da suka maƙale a cikin ramin da jirgin ya faɗa. A wasu rahotanni da aka fitar daga baya, an ce wasu jami’ai sun yanke shawarar a ƙona jirgin ma kawai, wai saboda kada waɗanda suka maƙale su ci gaba da azabtuwa tunda ba zai yiwu a ceto su ba. Wannan zargin ya jawo fushin jama’ar Nijeriya sosai a lokacin.
An ce wannan yanayin ya ɗauki sa’o’i da dama saboda rashin isassun kayan aikin ceto kuma wurin da aka yi haɗarin yana da nisa.
Wasu shaidu sun ce akwai mutane da ƙafafun su suka maƙale a ƙarƙashin ƙarfe, wasu kuma kaya sun danne su.
LABARIN MAI RABON GANIN BAƊI
Ɗaya daga cikin labarai da aka riƙa yawan ambato game da haɗarin shi ne labarin wani fasinja da ya tsira. Mutumin yana cikin jirgin daga Jos zuwa Gudi. Da aka tsaya, sai ya sauka domin ya sayi ruwa ko abin sha, ko kuma ya ɗan miƙe ƙafafun sa saboda gajiyar zama cikin jirgin mai cunkoso.
Lokacin da yake waje, sai aka buga ƙararrawar tashin jirgin. Kafin mutumin nan ya ankara, jirgi ya motsa. Da ma Shata ya faɗa a waƙar Ummaru ɗan Ɗanduna cewa, “Jirgi ba ya jiran uban wani.” Mutumin nan ya yi ƙoƙarin sake komawa jirgin, amma ya kasa. Haka aka tafi aka bar shi a tasha, ya tsaya yana jiran jirgi na gaba. Bayan wani lokaci, labarin faɗuwar jirgin kusa da Langa-langa ya zo.
Da mutumin nan ya ji labarin, ya kaɗu matuƙa. Ya gode wa Allah da ya hana shi sake hawa jirgin, domin kuwa da ya hau ɗin, to wataƙila shi ma da sai buzun sa. Ya riƙa faɗin: “Allah ne ya sa na sauka a tashar a lokacin.”
Da ma Hausawa suna cewa mai rabon ganin baɗi, ko ana mazuru ana shaho sai ya kai.
WANI ABU MAI BAN-MAMAKI DA AKA SAMU BAYAN HAƊARIN
Shekaru da dama bayan haɗarin, mutanen da suka ziyarci wurin sun riƙa hango wasu sassa na mushen jirgin a cikin ramin da ya faɗa. Rahotanni daga wasu ‘yan jarida da suka je wurin shekaru bayan haɗarin sun ce sun ga wasu manyan sassan ƙarafunan jirgin da suka kasance a wurin a tsawon lokaci. Sai dai kuma yanzu duk ‘yan gwangwan sun yashe su sun sayar. Yanzu wurin ya cika da ciyawa da bishiyoyi saboda an bar shi babu wani gyara.
A tsawon lokaci, mutanen ƙauyukan da ke yankin sukan je kallon wurin haɗarin. Wurin ya zama wani ɓangare na tarihin su.
MURYOYIN FATALWA KO SHACI-FAƊI?
Wasu mazauna yankin sun ce har yau ana jin muryoyi kamar na mutane suna magana ko kuka daga cikin dajin da aka yi haɗarin. Wasu kuma sun ce wai ana jin sautin ƙarfe kamar ana bugun jirgi a wurin.
Hakan ya sa mutane dama suna guje wa wucewa ta kusa da wurin da dare, musamman a shekarun farko bayan haɗarin.
An kuma ce wasu makiyaya ko matafiya da ke bi ta yankin sukan guji yin zango kusa da wurin haɗarin, ko wucewa ta wurin da dare. Wasu sun ce suna jin tsoro ko wani yanayi na damuwa idan har sun bi ta wurin.
Sai dai kuma wasu na ganin cewa duk waɗannan labarai shaci-faɗi ne ko ji-ta-ji-ta kawai, kuma suna faruwa ne saboda girman bala’in da ya faru.
Sau da yawa, idan wani babban bala’i ya faru a wuri, mutane sukan ƙirƙiri labaran al’ajabi su liƙa wa wurin, su camfa shi.
Haɗarin Langa-Langa yana da muhimmanci a tarihin Nijeriya saboda yana ɗaya daga cikin mafi muni a harkar sufuri a ƙasar. Bugu da ƙari, ya hasko tulin matsalolin tsaro a tsarin sufurin jiragen ƙasa na ƙasar nan, sannan ya kasance wata alama ta yadda bunƙasar layukan jirgin ƙasa ta Nijeriya ta fara raguwa, waɗanda a da suka kasance masu matuƙar aiki. Fasinjoji sun riƙa fargabar shiga jirgin ƙasa.
HAƊARIN LANGA-LANGA A ADABIN HAUSA
Sakamakon haɗarin jirgi na Langa-langa, Alhaji Ahmadu Doka mai kukuma ya yi waƙa mai taken ‘Ta Cinye Maza Sai Toka Langa-langa’.
Ya yi waƙoƙi biyu a kan haɗarin. Ta farkon, ya yi ta shi kaɗai, ta biyun kuwa tare da ‘yan amshi.
Wannan ya sa haɗarin ya shiga kundin adabin baka na Hausa.
KAMMALAWA
An tabbatar da cewa wannan haɗari ya kasance babban ibtila’i a tarihin Nijeriya. Girman sa ya sa mutane suka dinga ba da labarai barkatai game da shi, kuma har yau ana tunawa da shi a tarihin jiragen ƙasa na ƙasar nan.
Sai dai kuma babu tabbacin idan gwamnati ta bayyana rahoton kwamitin bincike da ta kafa kan haɗarin. Sannan babu tabbacin idan ta biya diyya ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka ji rauni tare da asarar dukiya a haɗarin. Idan kuwa haka ne, to fatalwar haɗarin Langa-langa tana nan tana yawo a cikin tarihin safarar jiragen ƙasa ta Nijeriya kenan.
To, Allah ya kiyaye gaba, amin.
![]()
