Bismillah a farkon majlisi,
Ya Jallah biya ni buƙatu.
A gare ka na wo ƙoƙon barar
Fiƙira da yawa ta rubutu.
Yi salatin Khairul Anbiya,
Al-Khatam tsibiri na zukatu.
A cikin duka jerin manzuna,
Shi ne aka bai wa sarautu.
Mai yin koyi da Muhammadu,
Abadan tsira ya rabautu.
Ban ƙosawa a yabo nasa,
Jiddadun domin sa na bautu.
Baitika na riƙo kaya guda,
Na yabo a gurin Al-Bintu.
Ai yau kam ‘Birthday’ ɗin ta ce,
Murna ta saka na ƙagautu.
Al-Hijazi jikanyar Arab,
Da Fulani ingantattu.
Tsatso ta jinin Ɗanfodiyo,
Duk mai shakku, yi karatu.
Mowar Mama Ta-Gusau, ku ji,
Wato marubuciya Hafsatu.
Da Ahmadu gwarzo, malami,
Da ya koyar kar mu shagaltu.
Ya Rabbi jiƙai nasa da’iman,
Sanya shi cikin cetattu.
Shi da Mama haƙiƙan mun yaba,
Sun ba mu ɗiya da nagartu.
Mai kyan haiba mai kyan diri,
Fasalin ta ƙwarai ya saitu.
Zuciyar ta fara, launi fari,
Aikin ta a kai ta magantu.
Al-Hijazi da himma ta taho,
Don kawar mana duk gotattu.
Burin ta Arewa mu wattsake,
Mu zamo duka duk ‘yantattu.
A wajen tanyon jama’ar mu kaf,
Rayuwar ta a nan ta kwaɗaitu.
In ta na yaƙin ceton ƙasa,
Sai ka ɗauka ko ta zautu.
Ba ta shayin mai zare ido,
Janaral ne ko kuma kurtu.
Mai yin rawani ko zanzaro,
In dai ƙullin su mu cutu.
Ba ta tsoro, shakka ta cire,
Ai fahimtu ko a ɗimautu.
Ko a gan ta da rai, Hijazatu,
Ko ta kwanta can a matattu.
Ni fa shaida ne na gani da ji,
Ban dogara gun ɗan sautu.
Sam irin ta a mata ba yawa,
Kallabi a maza ta kaɗaitu.
Shi ya sa taragon su guda ɗaya,
Ita da Bintu Majid, Rahmatu.
In ka ce ba ka san Hijazi ba,
Tafi Facebook za ka wadatu.
Al-Muhaiminu kare Zainaba,
Haska ta cikin mu halittu.
Mai so ya ga bayan wagga ‘ya,
Latse shi ka bar shi a kuttu.
Domin darajar wannan wata,
Ramadana wata na karatu.
Mai waƙen nan aminin ta ne,
Ibrahimu mun daidaitu.
Nan ne kuma aya zan ɗiga,
Ba don gajiya ta rubutu.
Sai don kada zancen yai tsawo,
Har ku ce kun kasa karatu.
Baitin mu talatin da biyar,
Na tukwici gun Al-Bintu.
Ibrahim Sheme
Abuja
06/04/2022