A yau, na wayi gari na ga ana nuna damuwa a soshiyal midiya a kan ji-ta-ji-tar wai ‘ya’yan Alhaji Mamman Shata sun sayar da gidan mahaifin su da ke Funtuwa, ana cewa bai kamata ba. Na farko, ina bada tabbacin cewa ba a sayar da wannan gidan ba. To amma wani hanzari ba gudu ba, shin idan ma an sayar ɗin, wani laifi ne aka ɗibga? Ko kaɗan!
Gidan dai mallakar wasu daga cikin ‘ya’yan Baba Shata ne a yanzu haka. To amma a cikin 2021 mutum biyu (maza) da su ka mallaki sashen gaba na gidan, wanda ya haɗa da garejin motar Dakta Shata da falo inda ya ke zama tare da karɓar baƙi sun sayar da nasu sashen. Wannan ɓangare nasu ne, haƙƙin su ne. An ma ji wani daga cikin su ya na faɗin, “Shin ko a Makka akwai gidan su Manzon Allah (s.a.w.) ne a yau?” Ya faɗi haka ne lokacin da aka nuna masa muhimmancin barin wannan gida na mahaifin sa a matsayin kayan tarihi.
Dalilin waɗannan ‘ya’ya biyu na Shata na sayar da gadon su shi ne su na da buƙatar su yi gidan kan su, su huta da zama a gidan haya. Kuma ba su da wata hanya sai wannan. A lokacin, sun buƙaci wani yayan su da ke kula da su (Alhaji Mustapha S. Shata) ya sanya hannu a takardar cinikin a matsayin shaida, shi kuma ya ƙi saboda bai lamunta da sayar da wannan gida mai ɗimbin tarihi ba. Shi ma Sarkin Maska (Hakimin Funtuwa) bai sa hannu a takardar ba saboda ya samu labarin cewa Alh. Mustapha bai sa hannu ba. Amma wannan bai hana cinikin ba. Kuma hakan ba ya nufin an sayar da gidan baki ɗayan shi.
Akwai wani haɗari da na hango. Nan gaba ake ji. Yanzu haka akwai ‘ya’yan Shata da su ma za su so su sayar da ɓangaren da su ka gada, domin su taimaki rayuwar su, musamman ganin cewa su Bala da su ka saida nasu sun yi amfani da kuɗin sun yi gidan kan su, sun huta da haya, sun rufa wa kan su asiri. Na san aƙalla mutum uku da su ka so su yi hakan su ma, amma aka kwaɓe su, aka nuna masu muhimmancin riƙe wannan gida a matsayin abin tarihi (historical legacy). Sun amince (amma ta ciki na ciki). To, idan yanzu akwai masu tsawatawa a kan kada ‘ya’yan Shata su sayar da gidan, nan gaba fa?
Sai dai duk da yake sayarwar ba laifi ba ne a addinance ko a hukumance, na yarda da cewa aje gidan a matsayin kayan tarihi ya na da matuƙar tarihi. Amma ni a nawa ganin yin hakan kuma ba haƙƙin ‘ya’yan Shata ba ne su kaɗai. Haƙƙi ne na hukuma da duk masoyan Shata da masu rajin adana kayayyakin tarihin mu na gargajiya.
Me zai hana gwamnatin Jihar Katsina ta sayi wannan gida, ta mallaka shi ga Hukumar Tarihi Da Al’adu ko Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua a matsayin cibiyar nazarin kaɗe-kaɗen Hausa? Ana ma iya sayen gidajen maƙwabtan Shata aƙalla guda huɗu domin a faɗaɗa wajen, a samar da ofisoshi da laburare da wurin fakin motoci da masallaci da inda za a shuka fulawoyi da itatuwa. Wannan aiki ya fi ƙarfin ɗan Shata ko wani mai ɗan ƙarfi! Kada ma a bari wani mutum guda ɗaya ya saya, ko wata ƙungiya mai zaman kan ta, domin matsalolin da ka iya tasowa. Mallakin gwamnati ya fi zama dindindin. Idan ma wani attajiri ya ce zai saya, to sai dai ya saya wa hukumar tarihi ko ita jami’ar.
Abu mai muhimmanci shi ne kada a banzatar da halin da iyalan Shata su ke ciki. A gaskiya, su na da buƙatu nasu na kan su kamar kowa, kuma duk mun san cewa rayuwa ta yi wuya a yanzu. Wa ya damu da halin da su ke ci? Wa ke taimaka masu? Ko aikin yi ko tallafin ƙaro karatu ba a ba su, don darajar mahaifin su. Sannan gwamnati ba ta damu da gidan Shatan ba a matsayin wani abu na tarihi. Kai, Shatan ma kan shi gwamnati ba ta damu da shi ba a yanzu! Me ta yi don karrama shi? Me ta yi wa iyalin sa?
Na taɓa kiran taro wanda na ke jin shi ne na farko na tunawa da Shata shekaru tara da su ka gabata inda na lissafa waɗannan muradai da na ambata a sama. Mun yi taron a ranar 15 ga Yuni, 2013 a Gidan Arewa da ke Kaduna inda mu ka kafa Ƙungiyar Tunawa Da Mamman Shata (wato Mamman Shata Memorial Association a turance) domin tunkarar al’amarin tattara kayan tarihin Shata har da sauran makaɗan Hausa baki ɗaya, wanda zai kasance a ƙarƙashin wata cibiyar bincike ta musamman mai suna ‘Mamman Shata Centre’ ko ‘Mamman Shata Hausa Music Centre’. Wasu ‘ya’yan Shata sun halarci taron, irin su Jamila, marigayi Mamuda, Sagir (Bala), Mukhtar, Halima (Dubulle) da Maimuna ɗiyar matar da Shata ya fara aura a rayuwar sa, da sauran su. Akwai kuma mu masoyan Shata; ban da ni akwai Hamisu Adamu Gamarali Funtua (wanda aka zaɓa a matsayin shugaban ƙungiyar), Yusuf Tijjani Albasu, Kabir Umar (PRO), Aliyu Ibrahim Ƙanƙara, Al-Amin Ciroma, Muhammad Sani Umar Faskari, Abdullahi Ɗantasi Funtua, Abba Muhammad, Abubakar Yusuf Ladan, Aliyu Abdullahi Gora, Salisu Fa’ida Funtua, da sauran su. Rahoton taron da jawabin da na yi duk su na cikin littafin ‘Shata Ikon Allah!’ da na rubuta (shafi na 884 zuwa na 885 da kuma shafi na 893 zuwa na 896). A ƙarshe, rarrabuwar kai ta farraƙa ƙungiyar. Yanzu mun bar wa “gwanayen abin” (waɗanda su ka rusa wancan ƙudirin na farko), su yi mu gani.
Saboda haka dai, batun maida gidan Shata wata cibiya, ba a yau aka fara shi ba. Amma maganar da ake yi a yanzu duk ta fatar baki ce kurum domin an kasa ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki a kai. Masu kurin cewa su masoyan Shata ne, su tashi tsaye mu gani. Za mu so su ida wannan nufi da mu ka sa wa ɗan ‘ba’ shekara 9 da ta gabata.
Amma fa ko me za a yi, to a yi shi tare da batun taimaka wa ‘ya’yan Shata waɗanda ke buƙatar taimako. Akwai maza da mata (wasu matan ma mazajen su sun mutu sun bar su da yara, jikokin Shatan) waɗanda ke buƙatar taimako. Duk wani surutu a kan a samar da cibiyar tarihin Shata zai kasance zancen kwabo idan har ba a kula da halin da iyalin Baba Shata ke ciki ba. Don haka ma, idan sun sayar da kayan sa da su ka gada, ciki har da gidan, ba su yi wa kowa laifi ba. Ko shi Shatan da bakin shi ya ce idan sun sayar da wannan gida na Funtuwa, ba laifi ba ne domin ƙasa ce kawai da ya tara.
Ina so a sani cewa a yanzu ko da wani ya saye gidan baki ɗayan sa, za a iya saya a wajen sa ko magadan sa (tare da babbar riba) a lokacin da masu kishin abin na gaskiya su ka zo – kila a wani ƙarnin bayan namu. Yanzu kam ni ban ga laifin masu sayarwa ba domin su tsira da mutuncin kan su ko su samu abin sakawa a bakin salati. To Malam, ina amfanin baɗi ba rai?