Wannan waƙa, mai amshin “Ranar Kilishi Jikar Dikko”, Mamman Shata ya rera ta ne ga Hajiya Kilishi, matar Sarkin Daura Muhammadu Bashar (Allah ya jiƙan shi). Jigon waƙar shi ne kambamawa da yabo. A waƙar, Shata ya tuno da yadda aka yi bikin auren Kilishi (ɗiyar Sarkin Katsina Usman Nagogo) da Bashar lokacin ya na Wamban Daura.
Wannan waƙa gajera ce, to amma ta ƙunshi abubuwa da yawa.
- Ta nuna cewa sarakuna a ƙasar Hausa na auratayya tsakanin su;
- ta nuna ƙasaitar wannan bikin aure, wato irin babban taron da aka yi na jama’a da motoci da babura da kekuna, da kuma yadda sarakai ke yin babbar kyauta ga maroƙa ko mawaƙan su;
- ta taskace mana tarihin al’adar “durbar” da Turawa su ka kawo mana, wato hawan dawakai domin nuna al’adun mu;
- waƙar ta ba da tarihin ita Kilishi a taƙaice, wato Shata ya nuna mana cewa ita ‘yar Sarki ce jikar Sarki;
- a waƙar akwai nason addinin Musulunci, musamman ɓangaren karatu da kuma tarihi. Misali, mun fahimci cewa Shata ya san wani abu game da wasu waƙoƙin Larabci, wato irin “Alburda”, da mawaƙan Larabci irin su Alfazazi.
Na rubuta waƙar ne daga wani faifan Shata da na saurara. Na alamta inda aka yi amshi da alamar tauraro, wato *. Bismillah.
SHATA: Ranar Kilishi jikar Dikko.
AMSHI (*)
Ranar Kilishi jikar Dikko.
*
Bukin Kilishi jikar Dikko,
Taron ta sai ka ce an Durbar:
Mota dubu ta je tarbar ta,
Doki dubu ya je tarbar ta,
Dike dubu ya je tarbar ta,
Ba sa’ikul ba, ba ‘yan ƙas ba,
Tarbar Kilishi jikar Dikko.
*
Rad da Wamban Daura jikan Abdu,
Mamman jikan Sarki Musa,
Jikan Muska da Sarkin Fada,
Jikan Muska da Sarkin Fada,
Ran nan Wambai yab ban mota,
Yac ce don darajar ɗan Hamza,
Sardo Ahmadu jikan Shehu,
Sai ko Kilishi ta ce ita ta ba ni domin Ahmadu jikan Shehu.
*
Daidai, Kilishi jikar Dikko!
*
Kilishi Allah ya ba ki ladan aure,
Da ma ki san gidan Aljanna.
*
Da sauya waƙar Kilishi jikar Dikko,
Yara su na ta dukan fata,
Kiɗan sai ka ce fitah harsashi!
*
Zuba waƙa ni kai,
Ni sai zuba waƙa ni kai kama da ta Alfazazi,
Kamar ana tamsiri.
*
Zuba waƙa ni kai kama da ta Alfazazi,
Kamar ana Alburda.
*
Ta Tatsumburum garin Ɗanyaro,
Waccan Kilishi jikar Mamman,
Waccan Kilishi jikar Mamman,
Wannan Kilishi birnin Dikko,
Wannan Kilishi birnin Dikko,
Kakan ta Shehu ne Usumanu,
Baban ta Shehu ne Usumanu,
Kakan ta kau Muhamman Dikko.
*
Kilishi kakan ta kau Muhamman Dikko.
*
Kilishi kakan ta kau Muhamman Dikko.
*
Allah ya ba ki ladar aure,
Da ma ki san gidan Aljanna.
*
Daidai, Kilishi jikar Dikko.
*
Taron Daura ya kai taro,
Taron Daura ya kai taro,
Bukin Kilishi jikar Dikko.