Wasu baitocin marigayi Malam Lawan Maiturare

Ƙaunar Muhammadu na nutse ba waiwaye,
Na sanya kai na can ciki na dulmiya,
Ya hamidan Mahmudu ban da kamar ka.

Ya Annabin rahama gare ka na durƙusa,
Al-Musɗafa kai ne ka san matuƙar isa,
Mai son ka ma ya san isa domin ka.

Kaicon mutum ya san ka in bai so ka ba,
Kaicon mutum bai so ka don bai san ka ba,
Ba arziƙi gun wanda ba ya son ka.

Tsuguno da zaunawa da miƙewa tsaye,
Tafiya da hango nesa har mu yi waiwaye,
Mun sami wannan arziƙi domin ka.

Ya Ɗahirun mai kyan jiki da na zuciya,
Muɗahhiran ka tsakake mana ƙungiya,
Hadi ka na shiryar da mai ƙaunar ka.

Al-Musɗafa kai ne iya matuƙar rabo,
Mai son ka sai mai arziƙi kuma mai rabo,
Ba arziƙi faufau wajen maƙiyan ka.

Mutari du mai son ka ya gama arziƙi,
Mahmudu wanda ya ƙi ka ya rasa arziƙi,
Domin ko ba wani arziƙi sai naka.

Mutari jikan Nuhu in ba don ka ba,
Wallahi du taron mu da ba a yi mu ba,
Mun shaƙi ƙamshin arzikin nan naka.

Ya mai siraɗal mustaƙima mamallaki,
Don Murtala Hadi rasulun arziƙi,
Al- Musɗafa jirgin fiton bayin Ka.

Ya Rabbu mai Malakutu mai ma’ul haya,
Don sahibin Jibrila gwarzon Mariya,
Hasken ibada maganin mai shirka.

Mun roƙi alfarma saboda abin biya,
Mun tuba mun kora da ƙaunar zuciya,
Mun durƙusa Allah mu na roƙon Ka.

Ba za mu sami abin da bai zama naka ba,
Wa za mu ce wa ya ba mu in ba Ka ba mu ba?
Ka san buƙata ce da mu bayin Ka.

Ka ce a sa bakin da bai saɓe Ka ba,
Ban wo gaban kai na wajen roƙon Ka ba,
Shi ne na zo gun Musɗafa manzon Ka.

* Daga MALAM LAWAN MAITURARE (1976)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *